'Yan Bindiga na Barazanar Kashe Mata da Mijin da Suka Sace, Atiku Ya Yi Magana
- Wani mutumi da aka yi garkuwa da shi a Kaduna, Ahmed Abubakar Zakka, na neman ɗauki bayan 'yan bindiga sun sace shi tare da matarsa da jaririyarsu suna neman Naira miliyan 300
- Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da ɗan majalisar tarayya Bello El-Rufai sun nuna damuwarsu tare da buƙatar jami'an tsaro da su gaggauta ceto su
- Bidiyon da yake yaɗuwa a kafafen sada zumunta ya nuna ɗan bindigar yana ƙoƙarin harbin Zakka a kai yayin da matarsa ke kuka tana neman ɗauki daga al'ummar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, sun nuna matakar fargaba da takaici kan sace Ahmed Abubakar Zakka tare da matarsa da jaririyarsu a Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa an sace mutanen ne a gidansu da ke Millennium City a jihar Kaduna, wajen da ke fuskantar barazanar tsaro.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa lamarin ya fito fili ne bayan yaɗuwar wani bidiyo a ranar Litinin a dandalin X, inda aka hango ɗan bindiga ya daura makami a kan Zakka yayin da yake riƙe da jaririya a kusa da matarsa.
Maganar wanda aka sace
A cikin bidiyon, Zakka ya bayyana cewa 'yan bindigar sun sace su ne da tsakar dare wajen ƙarfe 11:00 na dare, inda yake cewa:
"Suna buƙatar Naira miliyan 300, kuma ni ban san ta ina zan samu waɗannan kuɗi ba. Ina roƙon 'yan Najeriya da su tallafa mana saboda Allah."
A martanin da ya yi a Facebook, Atiku Abubakar ya bayyana bidiyon a matsayin abin fargaba da keta haƙƙin ɗan adam, yana mai cewa babu wani ɗan Najeriya da ya kamata ya roƙi a masa rai a hannun masu laifi.

Source: Original
Ya buƙaci jami'an tsaro da su gaggauta matsa lamba don ceto su gami da dukkan waɗanda ke tsaye a hannun masu garkuwa.
Martanin Bello El-Rufai
A gefe guda, ɗan majalisa Bello El-Rufai ya ayyana sace iyalan a matsayin abin kunya da ba za a amince da shi ba a tsakiyar birnin Kaduna.
Ya buƙaci gwamnatin jihar Kaduna da 'yan sanda su ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri don tabbatar da an ceto iyalan Zakka tare da kare yankunan Dan Bushiya, Malali, da Unguwan Rimi daga hare-haren masu laifi.
El-Rufai ya jaddada cewa tsaron jama'a abu ne da ba za a yi wasa da shi ba, kuma ya kamata a ɗauki matakai na gaske maimakon surutai kawai.
An kama Rochas Okorocha
A wani labarin, mun ruwaito cewa bayan cafke shi, tsohon gwamnan jihar Imo kuma tsohon sanata, Rochas Okorocha, ya watsar da rahotannin da ke cewa kotu ta ba da umarnin kamasa.
A cikin wata sanarwa da ke fitowa daga mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Sam Onwuemeodo, ya ƙalubalanci masu yaɗa labarin da su fito da takardar umarnin kotun fili idan da gaske ne.
Okorocha ya tabbatar da cewa babu wata babbar kotu ko kotun majistare da ta fitar da wannan umarni dangane da ƙorafin da aka shigar game da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng

