Pantami Ya Magantu da INEC Ta Cire Sunansa, Ya Kara wa Masoya Ƙarfin Guiwa

Pantami Ya Magantu da INEC Ta Cire Sunansa, Ya Kara wa Masoya Ƙarfin Guiwa

  • Bangaren Isa Ali Pantami ta yi magana kan rashin fitar da sunan Farfesa Isa Ali Pantami a jerin sunayen ’yan takarar da INEC ta wallafa
  • Farfesa Suleiman Mohammed Gombe ya ce tawagar lauyoyinsu na tattaunawa da PDP da INEC domin warware matsalar cikin wa’adin da doka ta tanada
  • Ya buƙaci magoya bayan Pantami da ƙungiyar Pantamiyya su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da haɗin kai da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe – Bangaren Farfesa Isa Ali Pantami ta yi magana bayan rasa sunansa a cikin jerin sunayen masu takara a zaɓen 2027.

Hakan ya biyo bayan cire jerin sunayen yan takarar gwamna da na majalisun jihohi da INEC ta yi a yau Asabar.

Pantami ya kwantar wa masoyansa hankali
Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Isa Ali Pantami. Hoto: Professor Isa Ali Pantami.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed Gombe ya fitar wanda aka wallafa a shafin Facebook na Isa Ali Pantami.

Kara karanta wannan

Masoyan APC sun yi hatsarin mota a kan janyar zuwa gangamin Tinubu, Shettima

Abin da Pantami ya ce kan lamarin

Sanarwar ta ce Pantami ne ɗan takararta da ya lashe zaɓen fitar da gwani da aka sake gudanarwa a ranar 29 ga Satumba, 2026, bisa umarnin Babbar Kotun Tarayya.

Ta bayyana cewa rashin bayyana sunan Pantami a jerin INEC ya jawo damuwa tsakanin dimbin magoya bayan PDP da ƙungiyar Pantamiyya a faɗin jihar Gombe da sauran wurare.

Sai dai Farfesa Suleiman ya buƙaci magoya bayan ɗan takarar da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu haƙuri da kyakkyawan fata, yana mai cewa matsalar ta ɗan lokaci ce kuma ba hukunci na ƙarshe ba.

Ya ce akwai mutanen da ke aiki a ɓoye domin kawo cikas ga shugabanci nagari da alhaki a jihar Gombe.

Babu sunan Pantami a takarar gwamnan Gombe
Taswirar jihar Gombe da Pantami ya nemi takara a PDP. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da tawagar lauyoyin Pantami ke yi

Duk da haka, ya bayyana cewa tawagar lauyoyinsu da masu hulɗa da hukumomi sun fara tattaunawa da hukumomin jam’iyyar da hukumar INEC domin tabbatar da bin umarnin kotu da gyara matsalar cikin wa’adin da doka ta tanada.

Kara karanta wannan

INEC ta cire sunan Sheikh Pantami daga jerin sunayen 'yan takarar gwamna a Gombe

Farfesa Suleiman ya nuna kwarin gwiwar cewa za a warware matsalar da yardar Allah, tare da kira ga magoya bayan Pantami da su ci gaba da shirye-shiryen siyasa da wayar da kan jama’a.

Ya jaddada cewa PDP da ƙungiyar Pantamiyya suna nan da ƙarfi, cikin haɗin kai da jajircewa wajen ceto al’umma da ’yantar da su daga matsalolin da suke fuskanta.

A ƙarshe, ya ce babu wata matsala da za ta karkatar da su daga manufarsu ta yi wa bil’adama hidima, sannan ya yi addu’ar Allah Ya albarkaci jihar Gombe da Tarayyar Najeriya baki ɗaya.

APC ta tura wa INEC wasika

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC ta rubuta wa INEC wasiƙa, tana neman aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan amfani da rajistar mambobin jam’iyyun siyasa.

APC ta ce jam’iyyun da suka gaza miƙa rajistar mambobinsu ta zamani cikin wa’adin doka, ya kamata a hana su tsayar da ‘yan takara.

Jam’iyyar ta buƙaci INEC ta tabbatar da cewa masu rajista ne kawai za su kaɗa ƙuri’a ko neman takara a zaɓen cikin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.