Kungiyar Musulunci Ta Shiga Batun Cire Sunan Pantami, Ta Yi Kira ga Tinubu
- Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta bayyana cire sunan Sheikh Isa Ali Pantami daga jerin ‘yan takarar gwamna a matsayin rashin bin doka da raina kotu
- Ta buƙaci hukumar INEC ta gaggauta mayar da sunan Pantami cikin jerin, tana mai cewa cire sunan nasa ba bisa ƙa'ida ba ne kuma rashin adalci ne
- MURIC ta kuma zargi shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da nuna wariyar addini, inda ta bayyana rashin amincewarta da jagorancinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos – Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta MURIC ta yi Allah-wadai da cire sunan Farfesa Isa Ali Pantami daga jerin ‘yan takarar gwamnan Gombe na jam’iyyar PDP, tana mai cewa matakin ya nuna rashin bin doka da raina kotu.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ƙungiyar da ke Legas ranar Talata.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa MURIC ta ce cire sunan Pantami ya zo ne bayan gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani bisa umarnin kotu, inda ta buƙaci INEC ta gaggauta mayar da sunan nasa cikin jerin ‘yan takarar zaɓen gwamnonin 2027.
Pantami ya lashe zabe a PDP
MURIC ta bayyana cewa Pantami ne kaɗai ya tsaya takarar gwamna a PDP ta jihar Gombe a watan Mayun 2026, inda aka tabbatar da shi ta hanyar kaɗa ƙuri’ar murya a ranar 26 ga Mayu, 2026.
Ƙungiyar ta ce daga baya wata babbar kotun tarayya ta soke zaɓen tare da umartar jam’iyyar ta gudanar da sabon zaɓe.
A cewar MURIC, an gudanar da sabon zaɓen fitar da gwanin ne a ranar 29 ga Satumba, 2026, inda Pantami ya samu ƙuri’u 2,054, yayin da Khamisu Mailantarki ya samu 389, Aliyu Garry kuma ya samu ƙuri’u 112.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa jami’an INEC sun sanya ido kan sabon zaɓen, ƙarƙashin tawagar da Gambo Umar Arabi ya jagoranta, wanda ya sanya hannu tare da miƙa rahoton aikin ga hukumar.
MURIC ta zargi INEC da son kai
MURIC ta zargi shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da hannu a cire sunan Pantami, tana mai zargin cewa akwai bambancin yadda ake mu’amala da ‘yan takara bisa addininsu.
Akintola ya yi ikirarin cewa Amupitan yana da wata ajandar da ta shafi cire malaman Musulunci daga cikin ‘yan takarar zaɓen 2027, musamman waɗanda ke neman manyan mukaman siyasa.
Ya ce:
“Mun daɗe muna faɗin hakan. Mutumin da ya ɗauki nauyin rubuta shafuka 80 na takarda mai cike da abin da muke ganin ƙarya ne game da Musulman Najeriya, wanda aka miƙa wa Amurka, ba zai iya zama nagartaccen mai kula da zaɓe ba.”
MURIC ta yi zargin cewa idan Amupitan ka iya gabatar da irin waɗannan bayanai game da Musulman Najeriya, to babu abin da zai hana shi ƙirƙiro zarge-zarge kan Pantami, wanda ta ce shi ne malamin Musulunci tilo da ke neman kujerar gwamna a yanzu.
Ana son maido sunan Pantami
MURIC ta bayyana cewa ba ta amince da jagorancin Amupitan ba, tare da kira ga Shugaba Bola Tinubu ya naɗa sabon shugaban INEC wanda ba ya nuna bambancin addini ko ƙabila.
Ƙungiyar ta buƙaci a gaggauta mayar da sunan Pantami cikin jerin ‘yan takarar gwamnan Gombe na PDP, tana mai cewa tana kare haƙƙin Musulman Najeriya ne ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke ciki ba.

Source: Facebook
Ta jaddada cewa ƙungiya ce mai zaman kanta wadda ba ta goyon bayan wata jam’iyyar siyasa kai tsaye, kuma babban burinta shi ne kare haƙƙoƙin Musulmi a faɗin ƙasar.
Pantami ya mika korafi ga INEC
A wani labarin, mun ruwaito cewa lauyoyin PDP sun ba INEC wa’adin kwanaki uku domin saka sunansa cikin jerin sunayen ‘yan takarar zaɓen gwamnonin 2027.
Lauyoyin, ƙarƙashin jagorancin Ahmed Raji, SAN, sun bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 12 ga Oktoba, 2026, wadda aka aika wa shugaban INEC.
Sun bayyana cire sunan Pantami a matsayin mataki da bai dace da doka ba, suna mai cewa ya yi rajistar zama ɗan PDP, ya sayi fom ɗin takara, ya shiga zaɓen fitar da gwani.
Asali: Legit.ng


