Farmaki kan Jonathan da Tinubu: Shehu Sani Ya Gargaɗi Ƴan Arewacin Najeriya
- Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya gargadi ’yan Arewa kan nuna goyon baya ko murnar kai hare-hare kan yan siyasa daga kudancin Najeriya
- Ya ce irin wadannan hare-hare na iya haddasa rikicin ƙabilanci, musamman idan aka samu ramuwar gayya daga matasan Arewa
- Shehu Sani ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji goyon bayan abubuwan da ba za su amince a yi wa shugabanninsu ba idan lamarin ya sauya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya gargadi ’yan Arewa kan nuna goyon baya ko murnar hare-haren da ake kai wa shugabannin siyasa daga Kudu.
Shehu Sani ya bayyana cewa irin wadannan hare-hare na iya tayar da rikicin ƙabilanci, inda ya bukaci al’ummar Arewa da su guji goyon bayan abubuwan da ba za su amince a yi wa shugabanninsu ba idan lamarin ya sauya.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Source: UGC
Tsohon dan majalisar ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, 2026.
Yadda aka kai wa Jonathan hari a Bauchi
Ya yi amfani da hare-haren da aka ruwaito an kai wa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, a Bauchi da kuma Shugaba Bola Tinubu a Abuja wajen bayyana damuwarsa.
Shehu Sani ya tambayi ko Najeriya za ta ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali idan aka kai wa wani dan takarar shugaban kasa daga Arewa ko shugaban kasa hari a kudancin kasar.
Ya ce:
“An taba jifan tsohon Shugaban kasa Goodluck a Bauchi, kuma kasar ta kasance cikin kwanciyar hankali. An kuma ruwaito an jefe Shugaba Tinubu a Abuja, amma kasar na cikin kwanciyar hankali.
“Shin kasar za ta kasance cikin irin wannan kwanciyar hankalin idan aka jefe wani dan takarar shugaban kasa daga Arewa ko shugaban kasa a nan gaba a Enugu ko Ekiti?”

Source: Facebook
Shehu Sani ya gargadi matasan Arewa
Tsohon sanatan ya yi gargadin cewa irin wannan lamari na iya haddasa martanin ƙabilanci daga matasan Arewa, inda wasu za su rika amfani da kalaman kyama ga sauran kabilu.
A saboda haka, ya bukaci al'ummar Arewa da kada su goyi bayan ko taya murnar abubuwan da ba za su taba lamunta ba idan aka yi wa shugabanninsu.
Ya ce:
“Mu da muke daga Arewa, kada mu goyi baya, mu yaba ko karfafa abin da ba za mu taba lamunta ba idan aka juya akalar lamarin.”
Yadda aka kai wa Jonathan da Tinubu hare-hare
A ranar 22 ga watan Janairun 2015, wasu matasa sun kai hari kan ayarin motocin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma wurin gangamin yakin neman zabensa a dandalin Ibrahim Babangida da ke Bauchi.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun yi amfani da duwatsu da wasu abubuwa wajen kai harin, inda jami'an DSS shida suka samu raunuka, yayin da wasu motocin ayarin suka lalace.

Kara karanta wannan
2027: Magoya bayan APC sun yi takansu da rigima ta ɓarke a wurin yakin neman zaben gwamna
Harin ya faru ne a lokacin da ake tsaka da zafin siyasa gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2015.
An gargadi kai hari a masallaci
An ji cewa Ƙungiyar matasan Arewa (NEYGA) ta nemi Sultan Sa’ad Abubakar ya shiga tsakani kan zargin amfani da masallatai wajen siyasa.
Ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara a Masallacin Ƙasa da ke Abuja yayin sallar Juma’a.
NEYGA ta kuma buƙaci shugabannin JNI da MURIC su ɗauki mataki domin dakile siyasantar da masallatai da kare zaman lafiya a Arewa.
Asali: Legit.ng
