INEC Ta Fadi Dalilin Cire Sunan Pantami da Sauran 'Yan Takara, Ta ba Su Zabi

INEC Ta Fadi Dalilin Cire Sunan Pantami da Sauran 'Yan Takara, Ta ba Su Zabi

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bai wa jam’iyyun siyasa wa’adin ranar 24 ga Oktoba domin sanar da ita korafe-korafen cire sunayen ‘yan takararsu
  • Ta ce wa’adin ya yi daidai da Sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya bai wa jam’iyyun kwana 14 domin sanar da ita idan suna ganin an cire sunayen ‘yan takararsu bisa kuskure
  • Daga cikin waɗanda ba a saka sunayensu a jerin ba akwai ‘yan takarar gwamnan Gombe da Ogun na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami da Oladipupo Adebutu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya ranar 24 ga Oktoba a matsayin wa’adin ƙarshe da jam’iyyun siyasa za su sanar da ita idan suna ganin an cire sunayen ‘yan takararsu bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Jam'iyyar adawa ta yi maraba da aka saka gwamnanta a kamfen Tinubu

Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata.

Shugaban INEC a Najeriya
SHugaban hukumar zabe, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC ta yi bayani a Facebook ne bayan cire sunayen wasu fitattun ‘yan takara daga jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi, lamarin da ya janyo da kiraye-kirayen neman ƙarin bayani daga waɗanda abin ya shafa.

Manyan ‘yan takarar da aka cire

Daga cikin ‘yan takarar da ba a saka sunayensu a jerin INEC ba akwai Farfesa Isa Ali Pantami na PDP a Gombe da Oladipupo Adebutu na jam’iyyar a jihar Ogun.

Haka kuma, ba a saka sunan Aminu Gwarzo, ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, a jerin ba.

A jihar Jigawa kuma, jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta nuna rashin jin daɗinta kan cire sunan Aminu Ringim, wanda ta amince da shi a matsayin ɗan takarar mataimakin gwamna, tare da wasu ‘yan takararta.

Hukuncin da kotu ta yi

INEC ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, a shari’ar INEC v. Zenith Labour Party, mai lambar SC/CV/495/2026.

Kara karanta wannan

An tunkari INEC kan rashin ganin sunan Pantami da wasu 'yan takara

Hukumar ta ce kotun ta tabbatar da cewa tanade-tanaden Sashe na 77(5), 77(6) da 77(7) na Dokar Zaɓe ta 2026 sun dace da kundin tsarin mulki kuma dole ne dukkan jam’iyyun siyasa su bi su.

Tanade-tanaden sun wajabta wa jam’iyyun siyasa miƙa rajistar mambobinsu ga INEC cikin wa’adin da aka kayyade, tare da amfani da rajistar wajen gudanar da zaɓen fitar da gwani, tarukan jam’iyya da manyan tarukanta.

Wajen zabe a Najeriya
Wajen da aka tattara kuri'u a zaben Osun na 2026. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

A cewar hukumar, Kotun Ƙoli ta kuma tabbatar da mataki na biyu a jadawalin ayyukan zaɓe, wanda ya buƙaci jam’iyyun su miƙa rajistar mambobinsu tsakanin 21 ga Afrilu da 10 ga Mayu, 2026.

Dalilin cire sunayen 'yan takara

Hukumar ta bayyana cewa Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin cewa duk jam’iyyar da ta gaza bin tanade-tanaden dokar ba za ta cancanci tsayar da ɗan takara a zaɓen ba.

INEC ta ce ta yi amfani da wannan hukunci ne wajen kammala jerin sunayen ‘yan takarar gwamna, inda ta cire jam’iyyun da ba su cika sharudan miƙa rajistar mambobinsu ba.

Kara karanta wannan

PDP ta shaida matakin da ake dauka game da cire sunayen Pantami da wasu ‘yan takara

Ta ƙara da cewa matakin ya yi daidai da Sashe na 287(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi wa gyara, wanda ya wajabta wa hukumomi aiwatar da hukuncin kotuna.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa ta wallafa jerin sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar 12 ga Satumba, 2026, wato kwanaki 13 kafin Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin.

Matakin da ya kamata a dauka

INEC ta ce Sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya bai wa jam’iyyun kwanaki 14 daga ranar wallafa jerin sunayen domin sanar da ita duk wani kuskure da suke ganin an yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Fitattun 'yan siyasa 6 da suka tsallake rijiya da baya a jerin 'yan takarar INEC

Hukumar ta kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za ta ci gaba da bin doka da tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaɓe gabanin zaɓen gwamnonin da aka tsara gudanarwa a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

INEC ya gargadi INEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan naɗa wasu mutane biyu ‘yan kabilar Yarabawa a matsayin shugabannin muhimman sassan hukumar INEC.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana matsayinsa ne a cikin wata sanarwa, inda ya yi gargadi kan magudi a 2027.

Ya nemi a yi bayani kan naɗin Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi a matsayin shugabar sashen ayyukan zaɓe da rajistar masu zaɓe, da kuma Dr Lawrence Bayode a matsayin shugaban sashen fasahar sadarwa ta zamani (ICT).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng