'Yan Ta'adda Sun Tarwatsa Layin Wutar Lantarki a Najeriya
- Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun tarwatsa ginshikan wutar lantarki guda biyu da ke hada tashar samar da wuta ta Dam din Kainji da Jebba a jihar Neja
- Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na rana a ranar 17 ga Nuwamba, tsakanin al’ummomin Kanti da ke karamar hukumar Mashegu da Kanya a Mokwa
- Rahoton ya ce babu wanda ya rasa ransa, amma fashewar ta jefa mazauna yankunan da ke kusa cikin firgici tare da kara fargabar kai hari kan muhimman abubuwan more rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan layukan wutar lantarki guda biyu da ke hada tashar samar da wuta ta Dam din Kainji da Jebba a jihar Neja.
Rahoto ya ce harin ya faru ne da misalin karfe 2 na rana a ranar 17 ga Nuwamba, 2026, tsakanin al’ummomin Kanti da ke karamar hukumar Mashegu da Kanya a karamar hukumar Mokwa.

Source: Getty Images
Rahoton the Cable ya bayyana cewa an yi amfani da bama-bamai wajen tarwatsa ginshikan wutar lantarkin, lamarin da ya haddasa firgici a yankunan da ke kusa.
An lalata muhimman kayan lantarki
A cewar rahoton, ana zargin wadanda suka kai harin sun yi hakan ne domin lalata kayayyakin sadar da wutar lantarki, tare da yiwuwar kai hari kan tashar samar da wuta ta Dam din Kainji.
Rahoton ya kara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da sanya ido a yankin da lamarin ya faru domin bibiyar halin da ake ciki da kuma hana sake kai wani hari.
An samu hare-hare a Arewa
Zagazola Makama ya ce lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun hare-hare da lalata kayayyakin wutar lantarki a wasu sassan Najeriya.
A watan Nuwamba, Majalisar Wakilai ta kuduri aniyar gudanar da bincike kan lalata ginshikan wutar lantarki guda 10 cikin watanni biyar a jihohin Arewa uku.
Daga cikin kayayyakin da lamarin ya shafa akwai layukan wutar lantarki da ke hada Kano da Bauchi, Katsina da Kaduna.
Majalisar ta umurci kwamitocin da abin ya shafa da su gudanar da bincike, tantance asarar kudin da aka yi tare da gabatar da shawarwarin da za su taimaka wajen dakile sake faruwar hare-haren.

Source: Facebook
A wani hari makamancin haka, wasu ’yan bindiga sun kutsa cikin tashar wutar lantarki mai karfin 132kV ta Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) da ke Offa a jihar Kwara, a ranar 7 ga Mayu.
An kashe jami'in BEDC a Delta
A wani labarin, mun rahoto cewa an kashe wani ma’aikacin kamfanin BEDC bayan ya cire wa wani gida wutar lantarki a yankin Umunede da ke jihar Delta.
Shugabannin kamfanin sun ce rikicin da ya shafi bashin wutar lantarki ne ya yi sanadiyyar mutuwar ma’aikacin mai shekaru 38 a duniya.
Kamfanin BEDC ya bayyana cewa ’yan sanda sun kama mutum biyar da ake zargin suna da hannu a kisan ma’aikacin kuma ana bincike.
Asali: Legit.ng

