Kalaman Ministan Tinubu Sun Jefa Shi a Matsala, Mutanensa Za Su Kai Shi kotu

Kalaman Ministan Tinubu Sun Jefa Shi a Matsala, Mutanensa Za Su Kai Shi kotu

  • Kungiyar ’yan asalin Ebonyi mazauna ƙasashen waje ta yi barazanar maka Ministan Ayyuka, David Umahi, a kotu
  • Ta bai wa Umahi wa’adin sa’o’i 72 ya janye kalamansa tare da neman afuwar Obi da ’yan asalin Ebonyi da al’ummar Igbo
  • AEISCID ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya gargaɗi ministocinsa, tana mai cewa bai kamata a yi amfani da tsarin rabon mukamai wajen hana mutane takara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abakaliki, Ebonyi - Kungiyar yan Asalin Ebonyi Masu Zaman Kasashen Waje ta yi barazanar daukar matakin shari’a kan Ministan Ayyuka, David Umahi.

Majiyoyi suka ce mutanen tsohon gwamnan sun shirya daukar wannan matakin ne saboda kalamansa kan dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi.

Ana shirin maka minista Umahi a kotu
Ministan ayyuka a Najeriya, Dave Umahi. Hoto: Federal Ministry of Works.
Source: Facebook

Kungiya za ta shiga kotu da minista

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

Shugaban kungiyar, Ambasada Paschal Oluchukwu, ya bayyana a wata sanarwa ranar Litinin cewa sun bai wa Umahi wa’adin sa’o’i 72 ya janye kalamansa, cewar Vanguard.

Ya ce dole ne ministan ya nemi afuwar Obi, ’yan asalin Ebonyi da kuma daukacin al’ummar Igbo saboda kalaman da ake danganta masa.

Kungiyar AEISCID ta ce matsayinta ya biyo bayan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda ake zargin Umahi ya yi magana kan adawa da burin Obi na shugabancin Najeriya da tsarin rabon mukaman siyasa.

A cewar kungiyar, a cikin bidiyon, an ambato Umahi yana cewa an soki wasu shugabannin Ebonyi saboda bayyana matsayarsu na kin goyon bayan Obi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kungiyar ta kuma ce Dave Umahi ya yi tambaya kan ko Obi ya taba nada wani dan asalin Ebonyi a gwamnatinsa lokacin da yake gwamnan Anambra.

Yan Ebonyi za su kai karar ministan Tinubu
Taswirar jihar Ebonyi da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da yan Ebonyi ke zargin Umahi

Dangane da rabon mukaman siyasa, an ambato Umahi yana cewa ba lokacin Kudu maso Gabas ba ne ta samar da shugaban kasa, haka kuma ba lokacin Ebonyi ta Kudu ba ne ta samar da gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Tsohuwar gaba ta yi kamari: Wike ya yi wa Amaechi mummunan baki a siyasa

An kuma ambato ministan yana cewa zai tattauna da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Ebonyi, Cif Ifeanyi Chukwuma Odii, domin shawo kansa ya janye takararsa bisa tsarin rabon mukamai.

AEISCID ta soki kalaman da ake danganta wa ministan, tana mai cewa bai kamata a yi amfani da tsarin rabon mukaman siyasa wajen hana mutane neman mukaman zabe ba, cewar Punch.

Kungiyar ta tuna da takarar gwamnan Ebonyi a shekarar 2015, lokacin da Umahi ya nemi kujerar duk da rahotannin cewa gwamna mai barin gado, Cif Martin Elechi, ya fi son Farfesa Onyebuchi Chukwu.

Chukwu, wanda a lokacin yake ministan lafiya, dan asalin Ebonyi ta Kudu ne, amma Umahi ya ci gaba da neman kujerar gwamnan duk da wannan matsaya.

Umahi ya nuna kwarin gwiwar tazarcen Tinubu

Mun ba ku labarin cewa Dave Umahi ya ce yana da yakinin Allah zai ba Shugaba Bola Tinubu damar komawa kan mulki a wa’adi na biyu a 2027.

Ministan ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu, yana cewa duk da wahalhalun da suka haifar, an ɗauke su ne domin ceto tattalin arziki.

Umahi ya ce Tinubu ya gaji ayyukan tituna 2,068 da darajarsu ta kai kusan N13tn, kuma kusan kashi 80 cikin 100 na ayyukan ma’aikatarsa gadarsu ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.