INEC Ta Fadi Adadin Miliyoyin Jama'ar da ake sa Ran za Su Yi Zabe a 2027

INEC Ta Fadi Adadin Miliyoyin Jama'ar da ake sa Ran za Su Yi Zabe a 2027

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta cire bayanan masu rijistar zaɓe sama da miliyan 1.6 da ba su inganta ba
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce wannan mataki ya rage adadin masu rijistar zaɓe daga miliyan 103 zuwa sama da miliyan 100
  • Ya bayyana cewa mutane sama da miliyan 10.77 da suka yi sabon rijista sun samu nasarar shiga sahihin kundin masu zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa adadin masu rijistar zaɓe a Najeriya ya haura miliyan 100 bayan ta cire bayanan da ba su inganta ba, waɗanda aka samu a cikin kundin masu zaɓe.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, yayin wani taro da kwamishinonin zaɓe na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Farfesa Joash Amupitan
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa ya ce hukumar ta cire bayanan sama da miliyan 1.6 na waɗanda suka yi rijista sau da dama, waɗanda suka rasu da kuma sauran bayanan da ba su inganta ba.

An samu korafe-korafe 311,000

Amupitan ya ce hukumar ta yi amfani da na’urar tantance bayanan halittar jiki ta ABIS, tare da binciken korafe-korafe da ƙalubalen da aka gabatar kan kundin masu zaɓe.

Ya bayyana cewa bayan INEC ta buɗe damar gabatar da ƙorafe-ƙorafe kan bayanan masu zaɓe a cibiyoyin rijista da kuma intanet, ta samu ƙorafe-ƙorafe kusan 311,000.

A cewarsa, binciken da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewa kusan 232,000 daga cikin ƙorafe-korafen gaskiya ne, kuma an ɗauki matakan gyara matsalolin da aka gano.

Tribune ta wallafa cewa ya ƙara da cewa hukumar ta gano wasu bayanai 113 da kanta a cikin ƙarin kundin masu zaɓe.

An cire bayanan da suka maimaitu

Kara karanta wannan

Trump zai gana da Abdul El Sayed da ya ci zaben Sanata a Amurka

Shugaban INEC ya ce yawancin korafe-korafen da aka samu ta intanet sun shafi kurakurai da matsaloli a cikin tsohon kundin masu zaɓe da aka tattara tsakanin 2011 zuwa 2023.

Ya ce duk da cewa hukumar ta dakatar da babban aikin sake tantance masu zaɓe har zuwa bayan zaɓe, ta yanke shawarar gyara manyan kurakuran da aka gano a tsohon kundin nan take.

Masu zabe a Najeriya
Wasu masu zabe a jihar Gombe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Amupitan ya bayyana cewa sashen fasahar sadarwa na hukumar, tare da sashen kula da kundin masu zaɓe, sun kammala tantance bayanan da ke ɗauke da maimaituwar rijista.

Ya ce an kuma cire bayanan da ba su da cikakkun sunaye, da kuma waɗanda aka yi amfani da hoto guda wajen yin rijista sau da dama.

2027: Za a rufe jami'o'i

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) na shirin sauya jadawalin karatu a jami’o’in Najeriya na mako uku zuwa huɗu domin malamai su samu damar shiga aikin zaɓen 2027.

Shugaban NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da tawagarsa zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Ribadu ya ce NUC na shirin haɗa kai da shugabannin jami’o’i domin samar da ƙwararrun malamai da za su taimaka wa INEC wajen gudanar da zaɓen, musamman a matsayin jami’an tattara sakamako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng