Jagoran PDP da Pantami ke Takara a Gombe Ya Shiga Kwamitin Kamfen Tinubu

Jagoran PDP da Pantami ke Takara a Gombe Ya Shiga Kwamitin Kamfen Tinubu

  • APC ta fitar da sabon jerin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda aka haɗa Nyesom Wike, da gwamnonin adawa
  • Bola Tinubu zai jagoranci kwamitin, yayin da Kashim Shettima da Nentawe Yilwatda za su kasance mataimakan shugabanni, tare da Godswill Akpabio
  • APC ta naɗa Abdulaziz Yari darakta janar, yayin da Hope Uzodimma zai zama sakatare, domin tsara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Sabon jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC na zaɓen 2027 shekarar 2027.

Kwamitin ya ƙunshi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu gwamnonin adawa da Sanatan PDP, Ibrahim Hassan Dankwambo.

Sanata Dankwambo ya shiga jerin sunayen kamfen Tinubu
Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo. Hoto: Governor Dankwambo.
Source: Twitter

An sabunta kwamitin kamfen Tinubu

Sauran waɗanda aka saka sun haɗa da Gwamnan Osun, Ademola Adeleke; Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori; Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo; tsohon Gwamnan Lagos, Babatunde Fashola; da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, cewar Vanguard.

Kwamitin ya kuma haɗa tsofaffin gwamnoni da manyan jiga-jigan jam’iyyar a matsayin masu ba da shawara.

Kara karanta wannan

Wike da Gwamnonin adawa sun fito da APC ta fitar da sabon kwamitin yakin zaben Tinubu

Waɗannan sun haɗa da tsofaffin shugabannin APC na ƙasa, Adebisi Akande da Abdullahi Adamu; tsohon Gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun; tsohon Gwamnan Osun, Iyiola Omisore; Sanata Ibrahim Dankwambo; Sanata George Akume; tsohon Gwamnan Ogun, Segun Osoba; da Wale Edun.

Yadda Pantami ya samu takara a PDP

Dankwambo shi ne jagoran PDP a Gombe wanda aka ce ya taka rawa wurin ganin Farfesa Isa Ali Pantami ya samu takarar gwamna a jihar.

Pantami ya samu tikitin takarar a sauki bayan shiga barin APC sakamakon rasa takarar gwamna da aka ba Jamilu Isiyaku Gwamna.

A yanzu kuma, Pantami na cikin matsala bayan fitar da sunayen ƴan takarar gwamna ba tare da na shi ba wanda ya jawo maganganu.

An sabunta kwamitin kamfen Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya da ke neman tazarce a APC. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Tinubu zai jagoranci kwamitin kamfen dinsa

Bisa sabon jerin da aka bai wa ’yan jarida ranar Talata, Shugaba Bola Tinubu zai jagoranci kwamitin, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, za su zama mataimakan shugabansa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, su ma za su kasance mataimakan shugaban kwamitin.

Kwamitin ya naɗa Sanata Abdulaziz Yari a matsayin darakta janar, yayin da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni; Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; da Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, za su zama mataimakan darakta janar.

Kara karanta wannan

APC ta yi matsaya kan girmama Atiku da ke kiran Tinubu da 'Bola'

An kuma naɗa Sanata Adams Oshiomhole a matsayin mataimakin darakta janar mai kula da wayar da kan jama’a da tattara goyon baya, cewar Punch.

Sauran jami’an sun haɗa da Femi Gbajabiamila, wanda zai kula da harkokin gudanarwa; Ibrahim Kabir Masari, mai kula da jigilar kayayyaki da ayyuka; da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Aminu Masari, wanda zai zama mataimakin darakta janar mai kula da tattara goyon bayan ’yan majalisa.

Oluremi Tinubu za ta ba dalibai tallafi

Mun ba ku labarin cewa uwargidan shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, ta sanar da shirin bai wa ɗalibai 100,000 tallafi domin rage matsalolin kuɗin karatu.

Ta ƙaddamar da rabon fakitin kayan tsaftar jinin al’ada miliyan biyu da kayan karatu ga ’yan mata a makarantun gwamnati.

Ministan Ilimi ya ce gwamnati za ta sanya shirin cikin kasafin kuɗin shekara, yayin da jami’ai suka buƙaci a tabbatar da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.