Dalilin Kyale Gwamna a Zabi Jigon PDP Ya Jagoranci Yakin Zaben Tinubu a Rivers
- Nyesom Wike ya fadi hikimar jawo shi ya shugabanci yakin tazarcen Bola Tinubu a jihar Rivers
- Ministan Abujan ya karyata batun da ake yi cewa jam’iyyar APC ta ajiye Gwamna Simi Fubara a gefe
- Tsohon gwamnan Rivers ya ce ana bukatar wanda zai yi da gaske, shiyasa aka daura masa nauyin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Nyesom Wike aka zaba ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu a jihar Rivers a takarar 2027.
Nyesom Wike ya samu wannan matsayi wajen kamfe duk da kasancewarsa bai cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a hukumance.

Source: Twitter
An dauko Nyesom Wike an kyale Simi Fubara
Vanguard ta ce Ministan na Abuja ya yi bayanin hikimar ba shi wannan mukami alhali APC tana da gwamna a jihar Rivers.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan Tinubu ya ɓallo magana kan takarar Sheikh Pantami a zaben 2027
Wike ya ce an hada shi da aikin jagorantar tallar Bola Tinubu ne saboda yanayin jihar Rivers ya bambanta da na sauran jihohi.
Sauya-shekar Simi Fubara zuwa APC
A Rivers, APC ce ta ke da gwamna - Mai girma Siminalayi Fubara, amma ba shi ne kan gaba wajen taya APC cin zabe ba.
Asali ma gwamna Siminalayi Fubara bai neman tazarce domin kuwa APC ta hana shi samun takara duk da ya shigo cikin ta.
Kwanaki Fubara ya sauya-sheka daga PDP a sanadiyyar rigimarsa da tsohon gwamna kuma mai gidansa a baya wato Wike.
Da yake magana hirar da aka saba yi da shi duk wata, Mista Wike ya ce jgorantar yakin zaben Tinubu na bukatar jagoranci.
Sai dai ‘dan siyasar bai fadada maganarsa domin a iya gane inda ya dosa da kyau ba.
“A duk zabe, ana bukatar shugabanci da kyau; akwai abubuwa da yawa da ake yi.

Kara karanta wannan
Alaƙa ta ƙara tsami tsakanin Tinubu da gwamna a Najeriya, an tono yadda aka naɗa minista
- Nyesom Wike
Can kuma sai aka ji yana cewa wajibi ne a samu wanda da gaske yake yi idan so ake yi shugaba Tinubu ya yi nasara a Rivers.
Watakila yana nufin shi yana da wadannan abubuwa yayin da gwamna kuma ya rasa su.
Ya ce:
“Kuna bukatar wanda da gaske zai yi,”
APC ta ajiye Gwamna Fubara ne?
People Gazette ta rahoto shi yana cewa ba a yi watsi da Mai girma gwamna Fubara ba, ana tafiya da shi a aikin yakin neman zaben APC.
“A’a, ba a watsar da shi a gefe ba.”
“Fubara cikakken ‘dan jam’iyya ne, yana yin aikinsa da kyau. Idan da ba ‘dan jam’iyya ba ne, me zai sa mu rika taro a gidan shi?”
“Kun san mene ne mutum ya rika bada masauki a yi taro irin wannan a gidan shi?”
- Nyesom Wike
Ya kare da cewa abin da ke gaban Fubara shi ne hadin-kan APC ko da bai takara a jam’iyyar.

Source: Twitter
'Yan takaran PDP sun koma bayan APC
A nan kuma, ji aka yi cewa Nyesom Wike ya sa wasu ‘yan takaran PDP sun ajiye zancen shiga zaben Majalisar tarayya a badi.
‘Yan adawan za su yi tallar Bola Tinubu da ‘yan jam’iyyar APC ne a birnin Abuja tun da sun hakura da neman mulki a karon kansu.
Amma Wike ya ce a jihar Rivers, zai yagi wasu kujerun ‘yan majalisa a PDP duk da yana tare da shugaban kasa a babban zabe.
Asali: Legit.ng
