Abin da Wike Ya Fada da ‘Yan PDP Suka Janye wa APC Takarar Zaben majalisa
- Angulu Bako, Gomna Stephen Gashe da Ahmed Dogara Jacob sun yafe takarar majalisa da suka samu a Abuja
- ‘Yan takaran na PDP sun shaida wa kowa cewa sun fasa shiga zabe kuma jam’iyyar APC za su yi wa aiki a 2027
- Nyesom Wike ya jagoranci wannan yunkuri domin a kara wa APC da Bola Tinubu karfi a babban birnin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - ‘Yan takara uku da suka tsaya zaben majalisar tarayya a PDP a birnin Abuja sun hakura da shiga zabe.
Wadannan ‘yan takara sun janye kuma sun mara wa abokin gabanasu na jam’iyyar APC baya a zaben 2027.

Source: Facebook
The Cable ta ce ‘yan takaran da suka janye sun hada da; Gomna Stephen Gashe (Abaji/Gwagwalada/ Kwali/Kuje).
Akwai Ahmed Dogara Jacob (Municipal/Bwari), da Angulu Bako wanda da farko ya samu tikitin Majalisar dattawa.
A ranar Litinin dukkansu suka sanar da cewa babu su babu maganar yin takara a shekara mai zuwa.
Tasirin Rainbow Coalition a jam'iyyar PDP
‘Yan siyasar sun shiada wa duniya wannan ne a wajen wani taron ruwa da tsaki da tafiyar Rainbow Coalition a Abuja.
Hakan yana nufin sun koma goyon bayan Danladi Chiya (Abaji/Gwagwalada/ Kwali/Kuje) da Shekwogaza Gabaya (Municipal/Bwari).
Shi ma Sanata Philip Aduda na APC wanda yake harin koma wa majalisa ya samu goyon bayansu.
Meyasa PDP ta fasa shiga takarar majalisar?
Da yake magana a taron, Nyesom Wike ya ce sun hakura da kujerun ‘yan majalisa na Abuja ne saboda Bola Tinubu.
Ganin a birnin tarayya shugaban kasa yake zaune, Wike yana ganin bai dace a ce ‘yan PDP sun doke jam’iyya mai mulki ba.
Wike wanda ya bayyana kan shi a matsayin sarkin yakin neman zaben Tinubu a Rivers da Abuja har ya fara yi wa Tinubu aiki.
Yake cewa bambancin jam’iyya ba zai hana su aiki tare da nufin ganin shugaba Tinubu ya koma kan karagar mulki a 2027 ba.

Kara karanta wannan
PDP ta shaida matakin da ake dauka game da cire sunayen Pantami da wasu ‘yan takara
Wike yana harin kujerun majalisa a Rivers
Tsohon gwamnan ya nuna cewa PDP za ta fanshe a jihar Rivers domin a nan suna harin samun ‘yan majalisar tarayya.
Wike ya ce:
"Ainihi, a matsayin jagoran PDP na kasa, ya kamata in fada masu su bari in samu wata (kujerar).
"Amma saboda shugaban kasa a nan (Abuja) yake zama, ban so in raba komai da shugaban kasa.
"Ka dauki kujerar sanata da ‘yan majalisar wakilan tarayya biyu. Amma a jiha ta (Rivers), zan dauki ‘yan kadan."
‘Yan takaran na PDP da suka janye sun yi wa Wike mubaya’a, suka yi alkawarin za su yi aiki tare da shi a 2027.

Source: Getty Images
Wike, Adeleke sun shiga kwamitin yakin zaben APC
A baya aka ji cewa an yi gyara a kwamitin kamfen APC a zaben shugaban kasa amma ba a taba darekta janar da sakatare ba.
Bola Tinubu ne shugaban kwamitin, yayin da Kashim Shettima da shugaban APC suke taimaka masa kamar yadda APC ta sanar.
Nyesom Wike, Charles Soludo da Ademola Adeleke za su tallata APC a zaben shugaban kasa duk da suna jam’iyyun adawa.
Asali: Legit.ng
