Alaka Ta Kara Tsami tsakanin Tinubu da Gwamna a Najeriya, An Tono Yadda Aka Nada Minista
- Alamu na anuna cewa alaka na kara tsami tsakanin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde
- Gwamna Seyi Makinde yabyi ikirarin cewa Tinubu ya zaɓi Bayo Adelabu a matsayin ministan wutar lantarki duk da ya mika sunan wanda ya dace
- Makinde ya ce Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ne ya fi cin gajiyar ƙawancen gwamnonin G5 da Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce Shugaba Bola Tinubu ne ya zaɓi Bayo Adelabu a matsayin ministan wutar lantarki.
Gwamna Makinde ya ce Tinubu ya nada Adelabu duk da cewa shi ya gabatar da sunan Bimbo Adekanmbi, tsohon kwamishinan kuɗi a gwamnatin marigayi Abiola Ajimobi.

Source: Facebook
Makinde ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da kafar watsa labarai ta Fresh FM.
Yadda Tinubu ya dauki minista a Oyo
Gwamnan ya ce da farko, Tinubu ya fara neman a zabi wani ƙwararren masanin tattalin arziki da zai jagoranci ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki.
Makinde ya ce ya zaɓi Adekanmbi ne saboda yana ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita harkokin gwamnatin Oyo da ta gabata.
Sai dai ya ce daga baya Tinubu ya sanar da shi cewa ya yanke shawarar naɗa Adelabu, wanda suka fafata a zaɓen gwamnan Oyo na 2019.
A rahoton The Cable, Makinde ya ce:
"“Na ce, ‘To yallabai, na san Bayo. Na fafata da shi a zaɓen 2019. Mutum ne mai ƙwarewa sosai.’”
Makinde ya yi fatali da bukatar Tinubu
Ya ƙara da cewa daga ƙarshe shugaban ƙasar ya ce masa: “Tun da na yanke shawarar naɗa Bayo, ya kamata ka karɓe shi a matsayin wanda ka zaɓa, har ka fito ka bayyana cewa kai ne ka zaɓe shi.”

Kara karanta wannan
Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami
Sai dai Makinde ya ce ya ƙi amincewa da buƙatar, yana mai jaddada cewa shawarar ta Tinubu ce.
“Na ce, ‘A’a, ranka ya daɗe. Bayo zaɓinka ne, kuma ya kamata jama’a su san cewa kai ne ka zaɓe shi," in ji shi.
Gwamnan ya ce aikinsa shi ne taimaka wa shugaban ƙasa ta hanyar gabatar da mutanen da za su iya kawo ci gaba ga gwamnatinsa. Ya ƙara da cewa idan shugaban ya ga wani wanda zai iya yin hakan, babu laifi ya naɗa shi.
Gwamnonin G5 da naɗe-naɗen ministoci
Makinde ya ce daga baya ya gano cewa an kuma nemi wasu gwamnonin su karɓi mutanen da Tinubu ya zaɓa domin naɗa su ministoci, su gabatar da su kamar su ne suka zaɓe su.
“A tawagar G5, ban da Wike, ba bu wanda aka ba mukaman ministoci," in ji gwamnan Oyo
Ya ƙara da cewa ba gwamnonin G5 kaɗai aka yi wa hakan ba, domin an ba da sunayen wasu mutane ga takwarorinsa gwamnonin, tare da neman su amince da su kamar su ne suka zaɓe su.

Source: Twitter
Makinde ya kuma zargi Tinubu da rashin la’akari da rabon mukamai tsakanin yankuna yayin naɗe-naɗen da yake yi.
Ya ce wasu na zargin cewa Kudu maso Yamma ne ya mamaye gwamnatin Tinubu, amma a ganinsa, an zaɓi da yawa daga cikin waɗanda aka naɗa ne saboda alaƙarsu ta siyasa da shugaban ƙasar.
Makinde ya yi gargadi kan zaben Tinubu
Kun ji cewa gwamnan Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Seyi Makinde, ya bukaci ’yan Najeriya su sauke Bola Tinubu daga mulki a zaɓen 2027.
Makinde ya tuna cewa Tinubu ya yi alkawarin magance matsalolin wutar lantarki a Najeriya cikin shekaru huɗu amma har yanzu bai cika ba.
Asali: Legit.ng

