Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Ballo Magana kan Takarar Sheikh Pantami a Zaben 2027
- Nyesom Wike ya yi ikirarin cewa bai taba haduwa da tsohon ministan sadarwa kuma dan takarar PDP a jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami ba
- Ministan Abuja ya bayyana cewa gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya na zarginsa da goyon bayan takarar gwamna da Pantami ke yi a PDP
- Wannan na zuwa ne yayin da Wike ke .usayar yawu da wasu daga cikin gwamnonin APC, wadanda ba su goyon bayan gamayyar da ya kirkiro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan zargin da ake masa cewa yana goyon bayan dan takarar gwamnan jihar Gombe na PDP, Farfesa Isa Ali Pantami.
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya yi ikirarin cewa bai taba haduwa da Pantami ido da ido ba tun da yake harkokin siyasarsa.

Source: Facebook
Ministan ya bayyana haka ne a yayin tattaunawa da yan jarida wanda ya saba yi na wata-wata a yau Talata, 13 ga watan Oktoba, 2026, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wike ya tabo batun takarar Pantami
Da yake tsokaci kan zargin goyon bayan Pantami, Wike ya bayyana cewa bai taba gani ko haduwa tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ba.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya na zarginsa da goyon bayan takarar Pantami a zaben 2027 da ke tafe.
"Game da Pantami, ni ban taba ganin Pantami ido da ido ko na hadu da shi ba,na dai san ya rike minista a lokacin mulkin Buhari, amma gwamnansu (na Gombe) ya zo yaka ta babatu wai ina goyon bayan Pantami."
- In ji Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Rikicin Wike da gwamnonin APC
Wannan kalamai na Wike na zuwa ne yayin da ake samun takun saka tsakanin ministan da wasu daga cikin gwamnonin APC, wadnda ke zargin yana masu katsalandan a siyasar jihohinsu.
An fara samun sabani tsakanin Wike da gwamnonin APC ne yayin da aya bayyana shirinsa na jada wata gamayya mai suna Rainbow Coalation domin goyon bayan tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
A tattaunawa da yan jarida da ya gudanar yau Talata a Abuja, Wike ya jaddada cewa ba gudu ba ja da baya kan wannna gamayya, yana mai cewa ɗan jariri a siyasa ne kawai zai soki shirinsa.

Source: Facebook
Wike ya hango nasarar Tinubu a 2027
Ministan ya kuma tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ssmu nasara a babban zaben 2027 matukar aka fita aka kada kuri'a a rumfunan zabe.
Ya ce yan Najeriya za su sake zaben Tinubu ne saboda ayyukan alherin da aya aiwatar sassan kasar nan cikin shekaru uku da suka gabata, kamar yadda tashar TVC News ta ruwaito.
Wike ya shirya tawagar tallata Tinubu
Kun ji cewa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce zai kaddamar da tawagar yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu a Abuja da Rivers.
Wike ya bayyana cewa shi da magoya bayan Tinubu daga bangarorin siyasa daban-daban sun shirya fara gangamin neman kuri'u a zaben 2027
Asali: Legit.ng

