2027: Kwankwaso Ya Ji Dadin Irin Tarbar da Mutane Suka Yi Wa Tinubu a Jihohin Arewa 3

2027: Kwankwaso Ya Ji Dadin Irin Tarbar da Mutane Suka Yi Wa Tinubu a Jihohin Arewa 3

  • Jigon jam'iyyar APC, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya yaba wa 'yan Arewa kan goyon baya da haɗin kai da suke nunawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Ya ce tarbar da aka yi wa shugaban a ziyararsa ta baya-bayan nan a jihar Kebbi na nuna yadda mutanen Arewa suka amince da shugabancinsa
  • Kwankwaso ya bayyana cewa taron jama'a, ihun murna da addu'o'in da aka yi wa Tinubu a Birnin Kebbi sun nuna ci gaba da goyon bayan yankin ga gwamnatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jigon APC a Kano, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya yaba wa 'yan Arewa kan goyon baya da haɗin kan da suke nunawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027.

Kwankwaso ya ce tarbar da aka yi wa shugaban cikin farin ciki yayin ziyararsa a jihar Kebbi ta nuna yadda Arewa ke da kwarin gwiwa kan shugabancinsa da kuma aniyarsa ta sake tsayawa takara.

Kara karanta wannan

'Na samu tabbaci': Tinubu ya ce zai je ya yi barci bayan abin da ya gani a Kebbi

Musa Iliyasu.
Jigon jam'iyyar APC daga jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso Hoto: Musa Iliyasu Kwankwaso
Source: Facebook

Leadership ta ce a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, jigon na APC ya ce taron jama'a, ihun murna da addu'o'in da aka yi wa Tinubu a Birnin Kebbi sun nuna cewa Arewa na tare da gwamnatinsa.

Kwankwaso ya yaba wa yan Arewa

Ya lura cewa ziyarar siyasa da shugaban ya kai sassan Arewa, daga Kaduna zuwa Dutse, babban birnin jihar Jigawa, da kuma Birnin Kebbi, sun nuna ci gaba da samun goyon baya ga burinsa na yin wa'adi na biyu.

Ya ce:

“Daga Kaduna, inda Mai Girma Shugaban Ƙasa ya ƙaddamar da kamfen 2027, zuwa Dutse, babban birnin jihar Jigawa, da kuma jiya a Birnin Kebbi, 'yan Arewa sun nuna goyon bayansu ga sake zaɓen Tinubu tare da nuna kyakkyawan hali da ladabi.
“Arewa ta fahimci rawar da take takawa a tsarin siyasar ƙasa mai bambancin al'umma, kuma za ta ci gaba da goyon bayan haɗin kan ƙasa domin samar da ƙasa mai wadata.

Kara karanta wannan

"Alamu da lissafin siyasa sun nuna wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027"

“Tinubu ɗanmu ne, kuma shi ne zaɓi mafi dacewa ga Najeriya mai haɗin kai da ƙarfi.”

Ya bukaci a marawa Tinubu baya

Kwankwaso ya kuma yaba da gudummawar manoma, 'yan kasuwa, mata, matasa da iyalai masu aiki a faɗin Arewa, yana mai cewa ya kamata burinsu na samun ingantacciyar rayuwa ya shiga cikin muhimman manufofin gwamnati.

Ya dage cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar sun fara tasiri a rayuwar talakawan Najeriya, inda ya buƙaci 'yan ƙasa su ci gaba da goyon bayan shirin.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da manyan kusoshin APC a wurin gangamin yakin neman zabe a jihar Kebbi Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewarsa, babban zaɓen 2027 zai ba 'yan Najeriya damar yanke shawarar ko za su ci gaba da goyon bayan manufofin gwamnatin da kuma zuba jarin da take yi a fannonin ababen more rayuwa, samar da wadataccen abinci, farfaɗo da tattalin arziki.

Kebbi ya jaddada goyon bayan Tinubu

Kun ji cewa Gwamna Nasir Idris ya tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu cewa jihar Kebbi za ta ci gaba da kasancewa tare da APC a zaɓen 2027.

Gwamnan ya bayyana yawan mutanen da suka halarci gangamin APC a matsayin wata shaida ta goyon bayan da jihar ke bai wa Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262