'Yar Siyasar Arewa da Tinubu Ya Gina amma Wasu Suka Butulce Masa a 2023'
- Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce mutanen da Tinubu ya taimaka wa a baya sun janye goyon bayansu lokacin takararsa a 2023
- Yilwatda ya ce Tinubu ya taimaka wa ’yan siyasar Arewa saboda haɗin kan Najeriya da zaman lafiya
- Shugaban APC ya kuma kare ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da sukar ’yan adawa kan alkawarin rangwamen fetur da zargin sayar da kadarorin ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana wasu suka butulcewa shugaba Bola Tinubu.
Yilwatda ya ce da dama daga cikin mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya taimaka wa tsawon shekaru sun janye goyon bayansu lokacin da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.

Source: Twitter
APC ta karbi yan adawa daga jihohi 5
Yilwatda ya bayyana hakan ne a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa, yayin da yake karɓar wasu ’yan siyasa da suka sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa a jihohin Sokoto, Kaduna, Jigawa, Kano da Plateau, cewar Punch.
Ya ce:
“Mutanen da ya riƙa taimakawa tsawon lokaci a Arewa da Kudu, lokacin da ya ce yana son tsayawa takara, yawancinsu sun janye goyon bayansu.”
Ya bayyana cewa ’yan Najeriya da suka san tarihin Tinubu sun fito domin zaɓensa a 2023, musamman saboda rawar da ya taka wajen haɗin kan ƙasa da kuma abin da ya kira kare dimokuraɗiyya da rayuwarsa da jininsa.
Yayin maraba da sababbin mambobin, Yilwatda ya ce: “Ina maraba da ku baki ɗaya zuwa babbar jam’iyyarmu, kuma ina godiya da kuka ɗauki wannan muhimmin mataki.
Ba sauya jam’iyya kawai kuka yi ba, kun zo ne domin ƙarfafa imaninmu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ajandar Renewed Hope.”

Source: Twitter
Tarihin goyon bayan Tinubu ga ’yan siyasar Arewa
Yilwatda ya lissafo abin da ya bayyana a matsayin tarihin goyon bayan Tinubu ga ’yan siyasar Arewa, tun daga shekarar 2007.
Ya ce:
“Idan akwai wanda ya yi aiki domin haɗin kan Najeriya, to shi ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
'Ka mun afuwa': Ɗan Arewa ya roƙi yafiya daga Tinubu bayan watsi da tafiyar Atiku
A shekarar 2007, Tinubu ya goyi bayan Atiku domin ya zama shugaban Najeriya, saboda ya yi imanin cewa ya kamata mulki ya koma daga Kudu zuwa Arewa, cewar Vanguard.
Yilwatda ya ce Tinubu ya sake yin irin wannan abu a shekarar 2011, lokacin da Nuhu Ribadu, wanda yanzu yake matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).
Ya ce:
“Ya goyi bayansa, tare da ɗaukar nauyin hanyoyin sadarwarsa, domin tabbatar da cewa ya zama shugaban Najeriya. Shi ɗan Arewa ne.”
Yilwatda ya bayyana cewa a shekarar 2015, Tinubu ya tsaya tare da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, bisa hujjar cewa ya kamata mulki ya koma Arewa domin haɗin kan ƙasa da zaman tare, bayan rasuwar Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.
Ya ƙara da cewa a shekarar 2019, lokacin da manyan ’yan siyasar Arewa da dama suka juya wa Buhari baya, Tinubu ya ci gaba da goyon bayansa, har ma ya jagoranci kwamitin sulhu da ya haɗa ’yan Najeriya domin su goyi bayan tsohon shugaban.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya bukaci Atiku da Peter Obi su janyewa Tinubu, ya kawo hujja
Ayyukan da Tinubu ya yi a Arewa
Yilwatda ya gaya wa waɗanda suka sauya sheƙa cewa Tinubu ya yi ayyuka masu yawa a Arewa, musamman a fannin tituna da layukan dogo.
Ya ce:
“Sau da yawa ana yaudararku. Ana cewa, ‘Me Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Arewa?’ Suna ta maimaita wannan magana.”
Ya lissafa hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, hanyar Kano zuwa Maiduguri da kuma layukan dogo daga Kano zuwa Maradi da kuma daga Kaduna zuwa Kano, tare da wasu ayyuka da ya ce ana ci gaba da gudanarwa.
An fadi illar dawo da tallafin mai
Mun ba ku labarin cewa Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya yi gargaɗin cewa dawo da tallafin fetur na iya jawo litar mai ta kai Naira 2,000.
Oyedele ya ce cire tallafin fetur ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga asusun tarayya tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025.
Gwamnatin tarayya na shirin rage haraji da kuɗaɗen hanya, tare da ƙara tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi da rancen kasuwanci.
Asali: Legit.ng
