Hadimin Kashim Shettima Ya Ja wa Fati Muhammad Kunne duk da Tsallakowa wajen Tinubu

Hadimin Kashim Shettima Ya Ja wa Fati Muhammad Kunne duk da Tsallakowa wajen Tinubu

  • Fati Muhammad ta fuskanci suka kan yadda ta juya wa Atiku Abubakar baya domin faranta ran ‘yan jam’iyyar APC
  • Gimba Kakande ya ce sabanin siyasa abu ne da kan faru, amma yadda mutum ya rike mu’amala yana da muhimmanci
  • Idan mutum ya kwayewa iyayen gidan shi baya saboda ya canza layi, matashin ya ce zai jawo wa kan shi bakin tabo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Gimba Kakanda wanda hadimi ne a Fadar shugaban kasa ya aika wa Fati Muhammad sako a bainar jama’a.

Tsohuwar ‘yar wasan kwaikwayo, Fati Muhammad ta fito tana sanar da duniya cewa ta rabu da Atiku Abaubakar.

Fati Muhammad
Atiku Abubakar tare da Fati Muhammad a gidansa a 2023 da hoton tsohuwar 'yar fim din Hoto: @FatyMuhd
Source: Twitter

Gimba Kakanda ya gargadi Fati Muhammad

Gimba Kakanda wanda da su ake dama wa a mulki ya maida mata martani a shafin X a ranar Alhamis 8 ga Oktoba 2026.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya zafafa, ya kwatanta Tinubu da dakikin dalibi

Mai taimaka wa Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya fada wa Fati ta bi a hankali da kallon da za a rika yi mata.

Gimba Kakanda ya ce ganin yanayin yadda ta juya wa Atiku Abubakar baya, za a iya yi mata shaidar bakar maci amana.

Fitaccen marubucin ya ce canza gida a siyasa ba laifi ba ne, amma abin duba shi ne yadda mutum ya mu’amalanci alakokin.

Ya rubuta:

"Ban san wanda ke ba Fati Muhammad shawara ba, amma idan ka juya wa wanda ya taɓa taimaka maka baya domin kawai ka faranta ran sababbin masu taimaka maka, ka sani cewa su ma za su fara kallonka a matsayin mutumin da zai iya cin amanarsu nan gaba.
"Abu ne na dan Adam mutum ya samu sabani da wasu saboda hadin kai na siyasa, bambancin ra'ayi ko fifita wasu zabi.
"Babu wani laifi a cikin hakan kai tsaye. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda mutum yake tafiyar da kansa idan irin wadannan alakoki suka sauya."

Kara karanta wannan

Amaechi zai iya samu kan shi a matsala saboda kalaman da ya yi game da APC

Kuskuren Fati Muhammad bayan barin Atiku

Kakanda ya ce idan shi zai rika cin mutuncin tsohon mai gidansa saboda ana yi da shi yau, hakan zai sa a jefa matsa alamar tambaya.

Wannan shawara ta zo ne ganin Fati Muhammad ta fito tana zargin Atiku da karya, ta ce saboda haka ta bi layin Shugaba Bola Tinubu.

A rubuce-rubucen da ta yi, tsohuwar ‘yar wasar ta yi ikirarin cewa alkawarin dawo da tallafin fetur da Atiku ya yi duk yaudara ce kurum.

Gimba Kakanda ya yi misali da kan shi, yana cewa:

"Na san tabbas cewa ranar da zan zauna ina zagin wani da ya taba taimaka mani, ina kuma kokarin wulakanta shi domin kawai in sami karbuwa a wajen wanda yake taimaka mini a yanzu, wannan sabon mai gida zai fara tambayar kansa ko ina da kyawawan dabi'u da ka'idoji, kuma ko za a iya amincewa da kuma yadda nake rike sirri.

Kara karanta wannan

Obi da Kwankwaso sun bayyana inda matsala ta fito masu wajen yakin neman zabe

Ya ce babu wanda zai damka amana ga mutum mai saurin kware wa wani baya saboda ya rabu da shi.

Mutumin da yake tafa maka a yau saboda ka ci amanar wani, shi ma yana lura da irin abin da za ka iya yi masa gobe.

- Gimba Kakanda

Malam Kakanda ya ce ya shata wa kansa layin da ba zai tsallaka ba saboda kawai ya faranta ran wani sabon mai gida da ya yi a rayuwa.

Gwamna ya manta da adawarsa ga Tinubu

Kwanaki aka ji labari Gwamnan jihar Bauchi ya yaba wa sauye-sauyen tattalin arzikin Bola Tinubu duk da ‘dan adawar da ta ke tsakaninsu.

Mai girma Bala Mohammed ya gode wa shugaban kasa saboda kafa sansanonin soja a Alkaleri da Tafawa Balewa domin yakar 'yan ta'adda.

Gwamnan ya fadi haka ne da aka kaddamar da wata cibiyar bincike a Asibitin Koyarwa na jami’ar ATBU da Gwamnatin tarayya za ta gina masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng