Kakakin yakin neman zaben Tinubu ya ji kunya a idon kowa ana hira a gidan talabijin

Kakakin yakin neman zaben Tinubu ya ji kunya a idon kowa ana hira a gidan talabijin

  • Alwan Hassan, ya yi ikirarin cewa lambar gaggawa ta 112 na aiki, ya sa wannan cikin nasarorin gwamnatin Bola Tinubu.
  • Da aka gwada kiran lambar kai tsaye lokacin da ake hira da shi kai-tsaye a gidan talabijin, a karshe sai ‘dan siyasar ya ji kunya
  • Malam Alwan Hassan ya nemi a ba gwamnati ƙarin lokaci, yana mai cewa za a kammala daidaita ‘yan matsalolin da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar, Alwan Hassan, ya shiga wani yanayi da ya ji kunya a gaban dumiya.

Hakan ya faru ne lokacin da yake ƙoƙarin tallata gwamnatin APC a matsayinsa na ɗaya daga cikin masu magana da yawun kwamitin kamfe.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, yayin da Alwan Hassan ke tattaunawa da ɗan jarida Seun Okinbaloye a gidan talabijin na Channels TV.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi ikirarin cewa Allah ya nuna masa yadda zai daƙile rashin tsaro?

A yayin tattaunawar, Alwan ya bayyana amfani da lambar 112 domin neman agajin gaggawa a cikin nasarorin gwamnatin Bola Tinubu.

Ya kuma ƙalubalanci mai gabatar da shirin da ya gwada kiran lambar domin tabbatar da cewa tana aiki domin akwai masu ganin ba ta da amfani.

Alwan Hassan ya ce:

“Ɗauki wayarka ka kira 112. Mutane da yawa ba su san da wannan lambar ba. A da muna jin labarin lambar 911 a Amurka.

Ka kira 112 yanzu, ka saka wayar a lasifika, za su tambaye ka irin matsalar da kake ciki. Godiya ga gwamnatin APC.”

Sai dai bayan Seun Okinbaloye ya kira 112, lambar ta gagara shiga. Nan take mai gabatar da shirin ya ce: “Wannan lambar ba ta aiki.”

Malam Alwan Hassan ya dage cewa lambar tana aiki, yana mai cewa wataƙila matsalar sadarwa ce ta haddasa rashin samun nasarar kiran.

Sai dai Okinbaloye ya bayyana cewa sauran kiraye-kirayen da ake yi daga wurin suna shiga, sannan masu kallon shirin suna aika saƙonni.

Daga cikin saƙonnin da ake aiko wa har da korafin cewa ba a iya samun damar kiran 112.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso

Duk da haka, Alwan Hassan ya dage kan batun sa, inda ya ce shi da kansa ya taɓa amfani da ita sau da dama kuma tana aiki a kwanakin nan.

Fitaccen ‘dan siyasar ya yi bayanin cewa idan mutum ya kira layin 112, za a haɗa shi da cibiyar kula da abubuwan gaggawa da ke yankinsa.

Ma’aikatan cibiyar za su tantance irin matsalar da ake ciki, sannan su tura jami’an da suka dace.

Ya ce idan matsalar lafiya ce, za a sanar da jami’an bayar da agajin gaggawa na lafiya, idan matsalar tsaro ce, za a sanar da ofishin ’yan sanda.

Matashin ya kuma bayyana cewa gwamnati na aiki kan wani tsarin fasaha da zai taimaka wa cibiyoyin agajin gaggawa wajen gano inda ake kira.

Ko da akwai wata matsala, kwamitin kamfen na APC ya ce gwamnati za ta gyara nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng