Muhammed Idris Ya Lissafo Hanyoyin da kowane Dan Najeriya ke Amfana da Mulkin Tinubu

Muhammed Idris Ya Lissafo Hanyoyin da kowane Dan Najeriya ke Amfana da Mulkin Tinubu

  • Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce dukkan ’yan Najeriya na amfana da sauye-sauyen tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu
  • Ya bayyana hakan ne yayin gabatar da manufofin APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 mai taken “Daga Sauye-Sauye Zuwa Wadata”
  • Minista Mohammed Idris ya ce mutane miliyan 1.6 na amfana da asusun lamunin karatu na NELFUND

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce dukkan ’yan Najeriya na amfana da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar.

Ministan ya ce kowame Najeriya na amfana ta hanyoyi daban-daban kamar ta hanyar inganta tsaro, samun damar ilimi da bunƙasa ababen more rayuwa.

Mohammed Idris.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris a wurin gangamin yakin neman zaben APC Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

The Cable ta ce Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, yayin taron gabatar da manufofin APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ga manema labarai, mai taken From Reforms to Prosperity (Daga Sauye-Sauye Zuwa Wadata).

Kara karanta wannan

'Sai masu biyayya': An ware ƴan APC da za a ba motoci a kamfen Tinubu

Ya ce sauye-sauyen na shimfiɗa harsashin wadata a ƙasa, yana mai cewa shekaru huɗu masu zuwa ƙarƙashin gwamnatin Tinubu za su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun ci moriyar waɗannan matakai.

Ministan ya ce amfanin manufofin gwamnati bai takaita ga ’yan jam’iyyar APC ko wani rukuni na musamman a cikin al’umma ba.

Ya ce:

“A lokuta da dama, mutane na ta tambaya, ‘Su waye ke amfana da sauye-sauyen?’ Idan aka gina hanya, ban san ana buƙatar mutum ya nuna katin shaidarsa domin tabbatar da cewa ɗan APC ne ko yana cikin wani rukuni kafin ya bi hanyar ba.”

Amfanin Inganta tsaro da ilimi

Idris ya ce inganta tsaro na amfanar ’yan Najeriya a duk faɗin ƙasar, inda ya kawo Asusun Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) a matsayin wani misali na ayyukan gwamnatin.

Mohammed Idris ya ce:

“Idan tsaro ya inganta, kowa na amfana. Idan kuna neman misalin yadda waɗannan sauye-sauye ke shafar rayuwar talakawa, ɗalibai miliyan 1.6 da ke amfana da NELFUND ba daga wata duniyar daban suka fito ba, ’yan Najeriya ne da ke zaune a cikin ƙasarsu.”

Kara karanta wannan

Wike ya tsage gaskiya kan rawar da ya taka wajen soke takarar gwamnan APC a 2027

Ministan ya kuma ambaci cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ke cikin shakku na Ƙungiyar Yaƙi da Safarar Kuɗaɗen Haram da Tallafin Ta’addanci (FATF) a zangon ƙarshe na shekarar 2025.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Ya ce wannan mataki ya inganta damar Najeriya ta gudanar da harkokin kasuwanci da sauran ƙasashen duniya, cewar rahoton Vangaurd.

Ya ƙara da cewa hukumomin tantance darajar tattalin arzikin ƙasashe na duniya, ciki har da Fitch, Moody’s da S&P, duk sun ɗaga matsayin Najeriya.

Minista ya hango wadata ga Najeeriya

Ministan ya dage cewa waɗannan nasarori na nuna cewa sauye-sauyen na samar da alfanu ga ’yan Najeriya, duk da sukar da ake yi wa manufofin gwamnatin.

"Waɗannan duka misalai ne da ke nuna cewa sauye-sauyen na aiki, amma mutane na cewa ba su san waɗanda ke amfana ba. Ni kuma ina cewa kowane ɗan Najeriya na amfana," in ji shi.

Tinubu ya ja hankalin yan Najeriya

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci yan Najeriya du tantance ayyukan da gwamnatinsa ta yi wajen yanke masa hukunci a babban zaben 2027.

Ya kuma ƙalubalanci abokan hamayyarsa na siyasa da su bayyana abin da suka yi lokacin da suke riƙe da muƙaman gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262