APC Ta Yi Gyara a Kwamitin Kamfen din Tinubu bayan an Yi Abun Kunya a Idon Duniya

APC Ta Yi Gyara a Kwamitin Kamfen din Tinubu bayan an Yi Abun Kunya a Idon Duniya

  • APC ta amince da Dele Alake, Abdulaziz Yari da Mohammed Idris a matsayin mutanen da za su riƙa magana a madadin kwamitin yaƙin neman zaɓenta
  • Femi Gbajabiamila ya ce an ɗauki matakin ne domin inganta tsarin sadarwa da tabbatar da daidaito a bayanan da kwamitin ke fitarwa
  • Matakin ya zo ƙasa da kwana guda bayan Alwan Hassan ya kasa nuna yadda lambar gaggawa ta 112 ke aiki a wata hira kai tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya taƙaita izinin yin magana a hukumance a madadinsa zuwa mutum uku.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026, mataimakin darakta-janar na kwamitin mai kula da harkokin gudanarwa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana sunayen mutanen da aka amince su riƙa magana a madadin kwamitin.

Kara karanta wannan

"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya

APC ta yi gyara a kwamitin yakin neman zabenta
Mai girma Bola Tinubu a wajen yakin neman zaben APC a Jigawa Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun, ya sanya sanarwar da Femi Gbajabiamila ya fitar a shafinsa na X.

Mutanen su ne Ministan Ma’adanai, Dele Alake; Darakta-Janar na kwamitin, Abdulaziz Yari; da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Mohammed Idris.

Gbajabiamila, wanda shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, ya ce an amince da wannan sauyi ne domin tabbatar da ingantaccen tsarin sadarwa, ladabi da haɗin kai wajen bayyana manufofin kamfen ɗin.

Sauran kakakin za su koma mambobi

Sanarwar ta ƙara da cewa duk sauran mutanen da aka sanar a baya a matsayin masu magana da yawun kwamitin za su koma mambobin daraktan yaɗa labarai da dabarun sadarwa.

An kuma shawarci gidajen rediyo da talabijin da su lura da sabon tsarin, tare da bin ƙa’idojin da aka gindaya wajen gayyatar jami’an kwamitin.

“An shawarci gidajen rediyo da talabijin da su lura da waɗannan sauye-sauye tare da yin aiki da su yadda ya kamata. Kwamitin kamfen ɗin zai tura mutanen da suka dace domin halartar shirye-shirye a duk lokacin da buƙata ta taso.”

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027: Gwamna Radda ya runtuma kora a gwamnatinsa

Matakin ya biyo bayan faruwar wani abu

Wannan mataki ya zo ne ƙasa da kwana guda bayan Alwan Hassan, wanda ke cikin masu magana da yawun kamfen ɗin APC, ya fuskanci tangarɗa yayin da yake ƙoƙarin nuna yadda lambar gaggawa ta Najeriya mai lamba 112 ke aiki.

Hassan ya bayyana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels ranar Talata, inda ya yi magana kan lambar a matsayin ɗaya daga cikin nasarorin gwamnatin Tinubu.

A yayin hirar, ya ƙalubalanci mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, da ya kira lambar 112 domin nuna yadda ’yan Najeriya za su iya samun taimakon gaggawa.

Sai dai ƙoƙarin kiran lambar sau da dama a yayin shirin kai tsaye bai yi nasara ba. Duk da haka, Alwan Hassan ya dage cewa lambar tana aiki, yana mai cewa wataƙila matsalar sadarwar waya ce ta kawo cikas.

Amma Okinbaloye ya nuna shakku kan wannan bayani, inda ya ce sauran kiran da aka yi daga cikin ɗakin shirin sun samu nasarar haɗuwa.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Matsayar kiristoci kan tikitin muslim muslim a Najeriya

Wata magana da ta jawo ce-ce-ku-ce

A watan da ya gabata, Alwan Hassan ya kuma yi ikirarin cewa wasu ministoci na biyan kuɗaɗen da suka kai biliyoyin naira domin samun naɗin mukamai a gwamnati.

Sai dai Felix Morka, kakakin APC, ya fito daga baya ya fayyace cewa irin wannan al'amari ya faru ne a gwamnatin da ta gabata, ba a gwamnatin Tinubu ba.

APC ta yi gyara a kwamitin kamfen
Kashim Shettima a wajen kamfen din APC a Jigawa Hoto: Stanley Nkwocha
Source: Facebook

APC ta fadi abubuwan da Tinubu zai yi

A wani labarin kuma, kun ji cewa APC ta bayyana cewa tsaron rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya zai kasance babban abin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ba fifiko idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.

APC ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta ɗauki ƙarin jami’an tsaro 78,000, waɗanda suka haɗa da sojoji 28,000 da ’yan sanda 50,000, domin ƙarfafa yaƙi da matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng