"Abin da Tinubu Ya Bukaci Yan Najeriya Su Duba wajen Yanke Masa Hukunci a Zaben 2027"
- Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su tantance gwamnatinsa bisa ayyukan da ta gudanar, ba alkawuran siyasa ba
- Ya ce gwamnatinsa ta kawo ƙarshen jinkirin shekaru 22 wajen aiwatar da tsarin tabbatar da mafi karancin fansho
- Ya kuma ƙaddamar da shirin PensionCare domin bai wa ’yan fansho masu ƙaramin ƙarfi damar samun muhimman ayyukan kula da lafiya kyauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙalubalanci ’yan Najeriya da su tantance gwamnatinsa bisa tarihin ayyukanta da abubuwan da ta cimma, maimakon alkawuran siyasa.
Shugaban ya yi wannan kira ne a ranar Talata yayin ƙaddamar da tsarin tabbatar da mafi karancin fansho (Minimum Pension Guarantee Scheme) a hukumance, a tsohon a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kawo ƙarshen jinkirin shekaru 22 wajen aiwatar da shirin, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya wakilci Tinubu a wajen taron. A jawabinsa, shugaban ya ce gwamnatinsa ta wuce matakin furucin siyasa, inda ta kafa tsarin kariya na doka ga ma’aikatan Najeriya.
Tinubu ya kaddamar da tsarin fansho
Ya ce hakan zai tabbatar da cewa ma’aikatan da ke bayar da gudummawa ƙarƙashin Tsarin Gudummawar Fansho (CPS) ba za su samu kuɗin shiga da ya yi ƙasa da mafi ƙarancin adadin da aka tanada ba bayan sun yi ritaya.
A yayin taron, Tinubu ya kuma ƙaddamar da shirin PensionCare, wani tsarin kula da lafiyar ’yan fansho da hukumar fansho za ta ɗauki nauyin gudanarwa.
An tsara shirin ne domin bai wa ’yan fansho masu ƙaramin ƙarfi damar samun muhimman ayyukan kiwon lafiya ba tare da biyan kuɗi ba.
Shugaban ya bayyana waɗannan shirye-shirye guda biyu a matsayin manyan nasarori a tsarin kare jin daɗin al’umma, yana mai cewa ma’aikatan da suka kwashe shekaru masu yawa suna yi wa ƙasa hidima sun cancanci samun tsaro na kuɗi da kuma kula da lafiyarsu bayan ritaya.
Tinubu ya yi magana kan ayyukansa
Tinubu ya ce:
“Ina roƙonku da ku yi mini hukunci bisa tarihin ayyukana a wannan zaɓe.”
Ya kuma ƙalubalanci abokan hamayyarsa na siyasa da su bayyana abin da suka yi lokacin da suke riƙe da muƙaman gwamnati wajen tabbatar da mafi ƙarancin fansho, samar da kariyar lafiya da inganta jin daɗin ’yan fansho.
Shugaban ya ce Tsarin Tabbatar da Ƙaramin Fansho zai fara aiki nan take, kuma Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom) ce za ta gudanar da shi bisa tanade-tanaden dokar gyaran tsarin fansho.
Tinubu ya sake kore batun dawo da tallafi
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba.
Ya ce bai kamata a riƙa kashe kuɗaɗen da ya kamata a tanada domin makomar yara wajen biyan tallafin man fetur ba, maimakon mayar da su kan ilimi da noma.
Asali: Legit.ng

