Amaechi Ya Kira Ruwa, Shettima Ya Taso Shi a Gaba kan Taba Kimar Buhari

Amaechi Ya Kira Ruwa, Shettima Ya Taso Shi a Gaba kan Taba Kimar Buhari

  • Kashim Shettima ya bayyana kalaman Amaechi kan marigayi Muhammadu Buhari a matsayin waɗanda ba su dace ba kuma rashin girmamawa ga tsohon shugaban ƙasar
  • Mataimakin shugaban ƙasar ya tuna irin goyon bayan da Bola Tinubu ya bai wa ’yan takarar shugaban ƙasa daga Arewa a zaɓukan baya
  • Kashim Shettima ya bukaci ’yan Arewa su rama goyon bayan Tinubu ta hanyar zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya soki tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan zargin cewa marigayi Muhammadu Buhari ya yi masa alƙawarin tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a 2023, amma daga baya ya karya alƙawarin.

Shettima ya bayyana zargin a matsayin magana marar dacewa da rashin girmamawa ga ƙwaƙwalwar marigayi Buhari.

Shettima ya ragargaji Amaechi
Rotimi Amaechi tare da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima Hoto: Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi, Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Shettima ya soki kalaman Amaechi kan Buhari

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

Mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan magana ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, cewar rahoton jaridar Leadership.

Ya kuma yi tambaya kan dalilin da zai sa mutumin da ya yi shekara takwas yana aiki a majalisar ministocin Buhari ya fito bayan rasuwarsa yana irin waɗannan kalamai.

A wajen taron, Shettima ya bukaci al’ummar Jigawa da sauran ’yan Arewa su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Ya tuna goyon bayan Tinubu ga ’yan Arewa

Shettima ya kwatanta amincin siyasar Tinubu ga Buhari da abin da ya kira cin amanar da Amaechi ya yi wa tsohon shugaban ƙasar.

Ya tuna cewa Tinubu ya taimaka wa ’yan takarar shugaban ƙasa daga Arewa a lokuta daban-daban, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a 2007.

Haka kuma, ya ce Tinubu ya bai wa tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, Nuhu Ribadu, damar tsayawa takara a 2011.

Ya ƙara da cewa Tinubu ya mara wa Buhari baya a zaɓukan shugaban ƙasa na 2015 da 2019, yana mai cewa watakila Buhari bai samu nasarar lashe zaɓukan biyu ba tare da taimakon Tinubu ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Tinubu ya sake daukarwa 'yan Najeriya alkawarin da ya gaza cikawa

“Idan aka yi la’akari da tarihin ƙasar nan da jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bai kamata wani ya fito ya yi kalaman da ba su dace ba ko waɗanda ke nuna rashin girmamawa ga marigayi Muhammadu Buhari ba.”
“A lokacin da Obasanjo ya juya wa Atiku baya a 2007, Tinubu ya ba shi damar tsayawa takara. Haka kuma a 2011, Tinubu ya ba wani ɗan Arewa, Nuhu Ribadu, damar yin takara. Ya goyi bayan Buhari a 2015 da 2019. Buhari ba zai iya lashe zaɓukan biyu ba idan ba don Tinubu ba.”

Rawar da Tinubu ya taka bayan rasuwar Buhari

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma tuna lokacin da Buhari ya je Birtaniya domin karɓar magani, inda ya ce Tinubu ya tura shi ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar a asibiti.

Ya bayyana cewa bayan rasuwar Buhari, Tinubu ya kuma umarce shi da ya tabbatar an dawo da gawar marigayin daga Birtaniya zuwa Daura, Jihar Katsina, domin binne shi.

Ya bukaci Arewa ta mara wa Tinubu baya

Shettima ya bukaci ’yan Arewa su rama goyon bayan siyasar da Tinubu ya ba shugabanninsu ta hanyar zaɓensa a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Ana kewar Buhari": Amaechi ya tuna rayuwa a lokacin tsohon shugaban kasa

"Mu ’yan Arewa an san​ mu da cika alƙawari da kiyaye magana. Mu rama wa Tinubu da ƙuri’unmu a watan Janairu.” In ji shi.

Haka kuma, Shettima ya bayyana cewa tsofaffin gwamnonin Jigawa, ciki har da Sule Lamido, Saminu Turaki da Abubakar Badaru, suna goyon bayan sake zaɓen Tinubu.

Ya ƙara da cewa wasu shugabannin siyasa da ministocin da suka yi aiki a gwamnatin da ta gabata ma suna mara wa shugaban ƙasar baya.

Shettima ya yi magana kan Amaechi
Kashim Shettima a wajen kamfen din APC a Jigawa Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Shettima ya magantu kan Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kashim Shettima, ya yi zargin cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya yi wa kansa illa a takarar zaɓen 2027.

Mataimakin shugaban ya bayyana cewa Peter Obi da ke neman shugabancin Najeriya, ya yi wa kansa illa ne saboda yaɗa ƙarya da alkaluma marasa tushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng