2027: Atiku Ya Zafafa, Ya Kwatanta Tinubu da Dakikin Dalibi
- Atiku Abubakar ya soki matakin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na bayar da rangwamen fetur na kwanaki 30, yana mai cewa ba zai magance matsin tattalin arziki ba
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin Tinubu ta kwaikwayi shawararsa ta tallafa wa fetur da aka tace a Najeriya, amma ba dari bisa dari ba
- Atiku ya kuma bukaci a tabbatar da gaskiya a zaben 2027, tare da yin kira ga jam’iyyarsa ta ADC da ta kai sakon yakin neman zabenta ga al’ummar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan matakin rangwamen farashin fetur na kwanaki 30, yana mai cewa shirin ba zai kawo sauki mai dorewa ga ’yan Najeriya ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, yayin kaddamar da kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa a cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kara tsadar rayuwa, yana mai cewa rangwamen da ta sanar ya zo ne bayan tsawon lokaci da jama’a suka shafe suna fama da hauhawar farashin kayayyaki da kudin sufuri.
Atiku ya soki rege kudin mai
Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ta dauki sama da shekaru uku tana mulki, amma har yanzu ’yan Najeriya na fama da tsadar kayan abinci, sufuri da gudanar da kasuwanci.
Ya ce sanarwar rangwamen fetur na kwana 30 da NNPCL zai yi a gidajen mai, tare da bai wa masu sufurin jama’a fifiko, ba za ta wadatar wajen rage matsin da jama’a ke fuskanta ba.
A cewarsa, rangwamen na dan lokaci ne kawai, kuma ba zai ba iyalai da ’yan kasuwa damar tsara kashe kudi na dogon lokaci ba.
Atiku ya ce:
“’Yan Najeriya ba sa bukatar taron manema labarai domin a gaya masu cewa suna cikin wahala. Sun shafe kwana 1,229 suna fuskantar hakan tun bayan hawanka kan mulki.”

Kara karanta wannan
"Yan Najeriya ba su cancanci haka ba," Atiku ya sake aika sako mai ɗaga hankali ga Tinubu
Ya kuma tambayi Tinubu abin da zai faru bayan karewar rangwamen na kwanaki 30, yana mai cewa jama’a na bukatar mafita mai dorewa maimakon matakin da zai kare bayan wata guda.
'Kamar dakikin dalibi'
Atiku ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta dauki shawarar da ya gabatar a baya ta tallafa wa man fetur da aka tace a cikin Najeriya, amma ta kasa aiwatar da ita yadda ya kamata.
Ya ce a lokacin da ya gabatar da shawararsa, gwamnatin ta zarge shi da rashin fahimtar manufofin tattalin arziki, tare da cewa ba za a iya aiwatar da irin wannan mataki ba.
Sai dai Atiku ya ce sanarwar rangwamen da gwamnatin ta fitar yanzu ta nuna cewa ta amince da bukatar samar da wani tsari na rage farashin fetur, duk da cewa ya yi zargin an aiwatar da shi ba yadda ya kamata ba.
Ya bayyana cewa shawararsa ta kunshi tallafawa man fetur da aka tace a Najeriya kuma ake sayarwa ’yan kasar, tare da sanya iyakar kudin tallafin, shigar da shi cikin kasafin kudi da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa.

Kara karanta wannan
'Kiran 'Bola' da Atiku ke yi wa Tinubu na neman saka shakku kan ingancin zabensa'
Atiku ya ce irin wannan tsari zai taimaka wajen tallafa wa matatun mai na cikin gida da rage farashin man fetur, maimakon bayar da rangwame na dan lokaci.
Ya kuma yi amfani da misali mai zafi wajen sukar gwamnatin, inda ya kwatanta ta da dakikin dalibin da ya kwafi amsar abokin karatunsa ba tare da fahimtarta ba.

Source: Getty Images
An rage kudin mai na kwana 30
A wani labarin, kun ji cewa NNPCL ya sanar da bayar da rangwamen farashin fetur a gidajen mai na fadin Najeriya na tsawon kwana 30.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi haka ne a wani mataki na rage wa jama’a tasirin hauhawar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ya ce NNPCL za ta yafe ribar da take samu daga sayar da fetur a matakin gidajen mai a tsawon lokacin rangwamen.
Asali: Legit.ng
