Jaruma Fati Muhammad Ta Sake Sukar Atiku bayan Jama'a Sun Mata Rubdugu

Jaruma Fati Muhammad Ta Sake Sukar Atiku bayan Jama'a Sun Mata Rubdugu

  • Fati Muhammad ta ce ba ta musanta cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya taɓa taimaka mata a wani lokaci na rayuwarta ba
  • Sai dai jarumar ta ce taimakon da Atiku ya taɓa yi mata ba yana nufin ba ta da damar bayyana ra’ayinta na siyasa ko sauya matsayar ta a yanzu ba
  • Fati ta ce ita ma ta taɓa tsayawa tare da Atiku, ta ba shi goyon baya kuma ta fuskanci matsaloli saboda goyon bayanta gare shi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jarumar fina-finan Hausa, Fati Muhammad, ta bayyana dalilin da ya sa ba ta goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Jarumar ta ce ba ta taɓa musanta alherin da Atiku ya yi mata a wani lokaci a rayuwarta ba, amma ta ƙi amincewa da cewa hakan ya kamata ya hana ta bayyana ra’ayinta a yau.

Kara karanta wannan

An yi wa jaruma Fati Muhammad rubdugu kan tallata Tinubu

Fati Muhammad da Atiku Abubakar
Fati Muhammad tare da Atiku Abubakar a shekaru baya. Hoto: Faty Muhammad
Source: Facebook

Fati Muhammad ta rabu da Atiku Abubakar

A sakon da ta wallafa a Facebook, Fati ta ce yayin da wasu ke magana kan taimakon da Atiku ya yi mata, suna mantawa da cewa ita ma ta tsaya masa tare da ba shi goyon baya a lokacin da take ganin hakan ya dace.

Ta ce bai kamata a kawo ɓangare ɗaya na tarihin dangantakarsu da siyasa a bar ɗayan ɓangaren ba.

“Ni Fati Muhammad ce, kuma ba ni da wani dalilin musanta cewa Atiku Abubakar ya taɓa taimaka min a wani lokaci a rayuwata. Na san alherin da ya yi min kuma ina yaba masa, ba zan taɓa cewa bai faru ba,”

In ji ta.

Yayin da ta ce ta kasance tare da Atiku tun 2007, ta ce nuna godiya ga wanda ya taɓa taimaka wa mutum ba yana nufin dole ne mutum ya ci gaba da kasancewa da ra'ayi ɗaya da shi har abada ba.

Kara karanta wannan

'Babban bala'in da ka iya tunkarar Najeriya idan Atiku ya ci zabe a 2027'

Ta ce:

“Taimakon mutum ba bashi ba ne da za a yi amfani da shi wajen tilasta masa yin shiru har abada. Idan na gode maka saboda alherin da ka yi min, hakan ba yana nufin ba ni da damar samun ra'ayi daban da naka ba.”
Fati Muhammad
Fati Muhammad a wajen taron siyasa. Hoto: Faty Muhammad
Source: Facebook

Ta fadi wahalhalun da ta sha

Fati Muhammad ta kuma bayyana cewa ta fuskanci wasu matsaloli sakamakon goyon bayan da ta bai wa Atiku a baya.

Ta ce wasu daga cikin mutanen da suke sonta da goyon bayanta sun juya mata baya a lokacin da take tare da Atiku.

“Masoya na da yawa sun juya min baya lokacin da nake tare da Atiku, har aka nemi a kashe ni saboda Atiku. To wai kuna ina a wannan lokaci?”

In ji jarumar.

Ta ƙara da cewa:

“Saboda Atiku aka ƙona gidana. Saboda Atiku aka ƙona motata. Saboda Atiku na bar rayuwata a Kaduna na dawo Kano. Saboda Atiku mutane da dama da suke sona da goyon bayana sun juya min baya.”

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu da abokinsa suka kusa fada wa gadar Legas a hadarin mota

A farkon makon nan ne 'yan kwamen suka yi wa Fati Muhammad rubdugu kan kiran masoyanta su zabi shugaba Bola Tinubu a 2027.

Buba Galadima ya soki APC

A wani labarin, kun ji cewa jigo a jam'iyyar NDC, Buba Galadima, ya zargi gwamnatin APC da sanya wa ’yan adawa cikas wajen gudanar da kamfe a sassan ƙasar gabanin zaɓen 2027.

Buba ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya yi zargin cewa wasu ’yan siyasar adawa na fuskantar hare-hare ko cikas yayin da suke ƙoƙarin zuwa wasu sassan ƙasar neman goyon bayan jama'a.

Ya ce irin wannan yanayi na sanya wahala ga jam'iyyun adawa wajen gudanar da harkokinsu cikin ’yanci, yana mai cewa ya kamata ’yan siyasa su samu damar yin kamfe, magana da zirga-zirga cikin ’yanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng