Kotu Ta Ruguza Lissafin APC da ADC, Ta Soke Zaben Fitar da Gwani a Jihohin Arewa 2

Kotu Ta Ruguza Lissafin APC da ADC, Ta Soke Zaben Fitar da Gwani a Jihohin Arewa 2

  • Kotunan tarayya da ke Gombe da Jos sun soke zaɓen fitar da ’yan takarar ADC da APC a wasu mazabun tarayya, tare da umartar gudanar da sabon zaɓe
  • A Gombe, kotu ta soke zaɓen Bashir Gaddafi a matsayin ɗan takarar ADC na mazabar Akko, tare da umartar INEC ta gudanar da sabon zaɓe cikin kwanaki 21
  • A Jos, kotu ta umarci APC ta sake zaɓen fitar da ɗan takara a rumfunan zaɓe 10, tare da hukunta waɗanda ake ƙara su biya Naira miliyan 1.5

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Kotunan tarayya da ke Gombe da Jos sun bayar da umarnin gudanar da sabon zaɓen fitar da ’yan takara na jam’iyyun ADC da APC a wasu mazabun yan Majalisar tarayya.

Kotunan sun yanke wannan hukunci ne bayan ƙalubalantar yadda aka gudanar da zaɓen fitar da ’yan takarar jam’iyyun gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Kotu ta nemi cafke tsohon gwamna da sanata, an gano rashin gaskiyarsu kan zabe

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman kotuna a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kotun Gombe ta soke zaɓen Gaddafi

Punch ta rahoto cewa a Gombe, Mai Shari’a Vera Ibrahim ta soke zaɓen Bashir Gaddafi a matsayin ɗan takarar ADC na mazabar tarayya ta Akko, tare da umartar a gudanar da sabon zaɓen fitar da ɗan takara cikin kwanaki 21.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Adamu Kashere ya shigar, inda ya ƙalubalanci sahihancin zaɓen fitar da ɗan takarar da ya samar da Gaddafi a matsayin ɗan takarar ADC

Kashere ya yi zargin cewa ba a gudanar da sahihin zaɓen fitar da ɗan takara a faɗin rumfunan zaɓe na mazabar ba.

Ya kuma nuna shakku kan cancantar Gaddafi, bisa zargin cewa ya shiga takarar ne yana riƙe da muƙamin ma’aikacin gwamnati ba tare da ya yi murabus a hukumance ba.

Sai dai kotun ta ce mai ƙarar ya kasa tabbatar da zargin cewa Gaddafi yana ci gaba da karɓar albashin gwamnati a lokacin da yake neman muƙamin siyasa.

Kara karanta wannan

Ta faru ta ƙare: INEC ta shirya fitar da sunayen ƴan takarar gwamna, ƴan majalisu

Alƙalin ta kuma tabbatar da cewa Gaddafi mamba ne mai rijista a jam’iyyar ADC kuma yana da cancantar shiga zaɓen fitar da ɗan takarar jam’iyyar.

Kotun Jos ta umarci APC ta sake zaɓe

A wani hukunci na daban da aka yanke a Jos, jihar Filato, Mai Shari’a Dorcas Agishi ta umarci APC ta gudanar da sabon zaɓen fitar da ɗan takara a rumfunan zaɓe 10 na mazabar dan Majalisar wakilai ta Jos ta Kudu/Jos ta Gabas, saboda wasu kura-kurai.

Alƙalin ta bai wa APC kwanaki 30 ta gudanar da sabon zaɓen. Ta kuma umarci kowanne daga cikin mutum uku da ake ƙara ya biya Naira 500,000 a matsayin kuɗin shari’a, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 1.5 da za a biya mai ƙara.

Jam'iyya mai mulki.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Esther Bitrus Danboyi ce ta shigar da ƙarar a kan Dachung Musa Bagos, jam’iyyar APC da kuma INEC, kan zaɓen fitar da ɗan takarar da ya samar da Bagos a matsayin ɗan takarar mazabar.

Rumfunan zaɓen da abin ya shafa su ne Du, Shen, Zawan ‘B’, Fobur ‘A’, Fobur ‘B’, Jarawan Kogi, Mai Juju/Doss, Federe, Shere East da Shere West.

Kara karanta wannan

Bayan an mata rubdugu, jami'ar ABU ta canza shawara kan batun ƙarin kuɗin makaranta

Kotu ta karbe tikitin dan takarar APC

Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zama Gombe ta soke zaben fitar da gwanin APC na takarar Majalisar wakilai a mazabar Balanga/Billiri.

Kotun ta hana Hon. Ali Isa J.C. sake tsayawa takara tare da umartar APC ta gudanar da sabon zaben fitar da gwani a mazabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262