APC Ta Tafi Kotu a Guje yayin da Atiku ke Kokarin Hana Tinubu Shiga Takarar 2027
- Jam’iyyar APC ta kalubalanci umarnin wata kotun tarayya da ya ba Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC damar kai wa Shugaba Bola Tinubu takardun sammaci
- APC ta ce ba a bukatar umarnin, domin lauyoyin Tinubu sun riga sun karɓi takardun shari’ar tare da gabatar bukatar ba shugaba Tinubu kariya
- Jam’iyyar ta kuma ce Atiku da ADC ba su kai mata kwafin umarnin kotun da aka yi wa rajista ba, duk da cewa kotun ta bayar da umarnin a ranar 16 ga Satumba 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa IbrahAim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyar APC ta rubuta wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tana kalubalantar umarnin da ya ba Atiku Abubakar da jam’iyyar ADC damar kai wa Shugaba Bola Tinubu takardun sammaci ta hedkwatar jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Magana ta yi nisa, 'Tinubu Must Go' ta raba wasikun hada kan Atiku, Obi da sauransu
Jam’iyyar ta ce umarnin bai zama dole ba, saboda lauyoyin Tinubu sun riga sun gabatar da kariyarsa tare da kai wa lauyoyin masu shigar da ƙara takardun kafin bayar da umarnin.

Source: Facebook
Maganar APC kan sammacin
Punch ta wallafa cewa a cikin wasiƙar da aka sanya wa hannu ranar 22 ga Satumba 2026, Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, Ajibola Basiru, ya ce jam’iyyar ta samu labarin umarnin ne ta kafafen yaɗa labarai.
Basiru ya rubuta wasiƙar ne zuwa ga Mataimakin Babban Magatakardar Kotun, domin a kai ta ga Magatakardar Kotun Mai Lamba 6 da ke ƙarƙashin Mai Shari’a Inyang Ekwo.
Jam’iyyar ta ce har zuwa lokacin rubuta wasiƙar, masu shigar da ƙarar ba su kai mata kwafin umarnin kotun da aka yi wa rajista ba.
Atiku ya kalubalanci Tinubu
Shari’ar da ke gaban kotun ta samo asali ne daga ƙarar da Atiku Abubakar da ADC suka shigar domin neman kotu ta hana Tinubu da APC shiga zaben shugaban ƙasa na 2027.
Babban dalilin ƙarar ya shafi bambancin da ake zargin akwai tsakanin sunan da ke kan takardar NYSC da aka miƙa wa INEC da kuma cikakken sunan Shugaba Tinubu.
Kotun ta bayar da umarnin ranar 16 ga Satumba 2026 da ya ba masu shigar da ƙarar damar kai wa Tinubu takardun shari’ar ta hedkwatar APC, bayan da suka ce sun fuskanci matsala wajen kai masa su kai tsaye.
Yadda shari’ar ta gudana
APC ta ce an shigar da ƙarar ne a watan Agusta 2026, inda aka sanya Tinubu, APC da INEC a matsayin waɗanda ake ƙara.
Jam’iyyar ta ce yayin da aka kai wa APC da INEC takardun ƙarar, ba a kai wa Tinubu takardun kai tsaye ba.
A cewar jam’iyyar, Tinubu ya ɗauki hayar tawagar lauyoyi ƙarƙashin jagorancin Babban Lauya Wole Olanipekun, SAN, bayan ya samu labarin shari’ar ta kafafen yaɗa labarai.
APC ta ce a ranar 1 ga Satumba, ɗaya daga cikin lauyoyin Tinubu, Omosanya Popoola, SAN, ya bayyana a kotu cewa yana da damar karɓar takardun a madadin shugaban ƙasar.
Jam’iyyar ta ce lauyoyin masu shigar da ƙarar sun ƙi amincewa da hakan, lamarin da ya sa kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 28 ga Satumba domin ci gaba da sauraron lamarin.

Source: Facebook
APC ta ce a ranar 10 ga Satumba, Olanipekun ya rubuta wa kotu yana sanar da cewa Tinubu ya umarci lauyoyinsa su karɓi takardun ƙarar tare da samun kwafin da kotu ta tabbatar.
Hasashen makomar Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Fasto Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu ba idan ya sake lashe zaben shugaban ƙasa na 2027.
Ayodele ya ce wani yanayi da zai hana Tinubu kammala wa’adin na iya kai ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar.
Sai dai ikirarin da Ayodele ya yi kan lafiyar Tinubu ba a tabbatar da su daga wata majiya mai zaman kanta ba, kuma maganganunsa hasashe ne da ya bayyana kawai.
Asali: Legit.ng

