Bayan An Mata Rubdugu, Jami'ar ABU Ta Canza Shawara kan Batun Karin Kudin Makaranta
- Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta dakatar da aiwatar da sabon ƙarin kuɗin makaranta har sai an tattauna da ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki
- Sabon tsarin kuɗin makarantar ya ƙara kuɗin da ɗalibai ke biya daga tsakanin N62,000 da N84,000 zuwa tsakanin N143,000 da N298,000
- Hukumar jami’ar ta ce ƙarin ya zama dole saboda ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa da kuma tsadar ayyukan da take samar wa ɗalibai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zaria, Kaduna - Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, jihar Kaduna, ta dakatar da aiwatar da sabon ƙarin kuɗin makaranta da ta sanar kwanan nan, har sai ta gudanar da shawarwari da ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki.
Hukumar jami’ar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ta musamman da Sashen Hulɗa da Jama’a ya fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Bayan fetur, Gwamnatin tarayya na shirin rage hauhawar farashin muhimman kayayyaki

Source: Twitter
An wallafa wannan sanarwa a shafin jami'ar ABU na Facebook ranar Alhamis, 8 ga wwtan Oktoba, 2026.
ABU ta dakatar da karin kudin makaranta
Dakatarwar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan jami’ar ta ƙara kuɗin makaranta, lamarin da ya jawo tashin kuɗaɗen da ɗaliban digiri na farko ke biya a kowane zangon karatu.
A cikin sanarwar, jami’ar ta ce:
“Domin tabbatar da shawarwari, mutunta juna da gudanar da al’amura cikin kulawa, hukumar gudanarwa ta ABUbta yanke shawarar dakatar da aiwatar da sabon tsarin kuɗaɗen.
"Hakan zai ba da damar gudanar da shawarwari masu faɗi tare da karɓar ƙarin shawarwari daga ƙungiyar ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki.”
Sabon tsarin kuɗin makaranta
Legit Hausa ta ruwaito cewa sabon tsarin kuɗin makarantar ya ƙara kuɗaɗen da ake biya daga kusan N62,000 da N84,000 zuwa tsakanin N143,000 da N298,000, gwargwadon kwas da matakin karatun ɗalibi.
Hukumar jami’ar ABU ta ce ƙarin kuɗin ya zama dole saboda babban gibi da ke tsakanin kuɗaɗen da jami’ar ke da su da kuma ƙarin kuɗin gudanar da muhimman ayyukan da take yi wa ɗalibai.

Source: Facebook
Jami’ar ta kuma bayyana cewa matsalar ta ƙara tsananta bayan ta yi asarar kusan Naira biliyan 2.5 sakamakon hukuncin kotu, lamarin da ta ce ya ƙara matsin lamba sosai kan kuɗaɗen gudanarwarta.
A baya, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da Jami’ar Ahmadu Bello su biya Naira biliyan 2.5 a matsayin kuɗin diyya ga tsofaffin ma’aikata 110 da jami’ar ta kora daga aiki kusan shekaru talatin da suka wuce.
NANS ta yi fatali da karin kudin ABU
Kun ji cewa Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS), Akinteye Afeez, ya bayyana ƙarin kuɗin da ABU Zaria ta yi a matsayin “wasa da ya wuce gona da iri”.
Afeez ya ce idan shugaban jami’ar ba zai iya gudanar da makarantar yadda ya kamata ba, ya kamata ya yi murabus.
Asali: Legit.ng
