Gobara Ta Yi Gagarumar Barna a Kasuwar Kano, Gwamna Abba Ya ba da Tallafin Naira Miliyan 100
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da tallafin N100m ga ’yan kasuwar Yankifi da gobara ta shafa
- Abba Gida-Gida ya kuma bayar da umarnin sake gina sassan kasuwar da gobarar ta lalata domin ci gaba da harkokin kasuwanci
- Gwamnan ya ce za a fitar da kuɗin tallafin cikin mako guda domin taimaka wa ’yan kasuwar farfaɗowa daga asarar da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da tallafin N100m ga ’yan kasuwar da gobara ta shafa a kasuwar Yankifi Cooperative Market da ke jihar Kano.
An ce wannan kasuwa ita ce babbar kasuwar kifi a jihar Kano, haka kuma Gwamna Abba ya bayar da umarnin sake gina sassan da gobarar ta lalata.
A sanarwar da gwamnatin Kano ta wallafa a Facebook, gwamnan ya sanar da bayar da tallafin ne yayin ziyarar jajantawa da ya kai kasuwar ranar Juma’a, bayan wata gobara da ta tashi a daren Lahadi.
Gobarar dai ta ƙone kifaye, na’urorin sanyaya kaya da sauran muhimman kadarori na miliyoyin Naira.
Abba ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa asarar da ’yan kasuwar suka yi ba ta shafi kasuwancinsu da hanyoyin samun abin rayuwarsu kaɗai ba, har ma da tattalin arzikin jihar.
Ya jajantawa waɗanda abin ya shafa tare da kira gare su da su kasance masu haƙuri da juriya, yana mai bayyana faruwar lamarin a matsayin jarrabawa daga Allah SWT.
Gwamnan ya kuma buƙaci shugabannin kasuwar da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa matakan kariya domin hana sake faruwar gobara makamanciyar wannan.
Gwamna Abba ya bada tallafin N100m
A cewar wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Sanusi Bature, ya fitar ranar Juma’a, za a fitar da kuɗin tallafin N100m cikin mako guda ta ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha da kwamishinan zuba jari da kasuwanci.
Haka kuma, Abba ya umarci kwamishinan ayyuka da ya tsara yadda za a sake gina sassan kasuwar da gobarar ta lalata domin a fara aikin cikin gaggawa.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, El Rufai ya tsage gaskiya a gaban kotu kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu
Sanarwar ta ce gwamnan ya nuna damuwarsa kan halin da ’yan kasuwar da ke sayar da kifi da sauran kayan abinci masu saurin lalacewa suka shiga, sakamakon babbar asarar da gobarar ta jawo wa sana’o’insu.
Gwamnatin jihar Kano ta sake jajantawa ’yan kasuwar da abin ya shafa tare da ƙarfafa musu gwiwa da su kasance masu juriya yayin da suke ƙoƙarin farfaɗowa daga asarar da suka yi.
Gwamna Abba ya gargadi jami'an gwamnati
Kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi barazanar hukunta duk jami’an ƙananan hukumomin da suka karkatar ko suka yi amfani da motocin asibiti 484 ba bisa ƙa’ida ba.
Gwamna Abba Kabir ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana amfani da motocin wajen amfanin kansa ko kuma cin zarafin shirin zai fuskanci hukuncin da ya dace.
Asali: Legit.ng
