Ta Faru Ta Ƙare: INEC Ta Shirya Fitar da Sunayen Ƴan Takarar Gwamna, Ƴan Majalisu

Ta Faru Ta Ƙare: INEC Ta Shirya Fitar da Sunayen Ƴan Takarar Gwamna, Ƴan Majalisu

  • Hukumar INEC ta sanar da cewa za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi na zaɓen 2027
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa jam’iyyu 21 sun gabatar da ‘yan takara 936 na gwamna da mataimakansu
  • INEC za ta gudanar da zaɓen gwamna a jihohi 28 ranar 6 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaɓen majalisun dokokin jihohi zai gudana a sauran jihohin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi na ƙarshe.

Hukumar ta ce komai zai zo ƙarshe a gobe Asabar 10 ga watan Oktobar shekarar 2026 da muke ciki.

INEC za ta fitar da sunayen ƴan takara
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Za a gudanar da zaɓen gwamna da na majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027, kamar yadda sashe na 32(1) na dokar zaɓe ta 2026 ya tanada, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Hukumar fanshon ƴan sanda za ta zuba hannun jari a matatar Dangote

Abin da bangaren doka ke cewa kan takara

Sashen ya bayyana cewa hukumar za ta wallafa cikakkun sunaye da adireshin dukkan ‘yan takarar da aka amince da tsayawa takara, a ofisoshinta da kuma shafinta na intanet, aƙalla kwanaki 60 kafin zaɓe.

Sashe na 32(2) ya kuma tanadi cewa jam’iyyar siyasa mai rijista da ta lura an cire sunan ɗan takararta daga jerin da aka wallafa za ta sanar da hukumar a rubuce.

Sanarwar za ta kasance da sa hannun shugaban jam’iyyar na ƙasa da sakatarenta, tare da takardar rantsuwa, cikin kwanaki 14 bayan wallafa jerin sunayen.

A yayin taron manema labarai na duniya da ganawar masu ruwa da tsaki ranar Talata, shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana adadin ‘yan takarar da aka gabatar.

Ya ce jam’iyyun siyasa 21 daga cikin 22 da aka yi wa rajista ne suka gabatar da ‘yan takara 936 na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28.

Kara karanta wannan

Atiku ya magantu kan tsadar kayan noma, ya fadi mafita tare da sukar Tinubu

Haka kuma, jam’iyyun sun gabatar da ‘yan takara 9,692 domin neman kujerun majalisun dokokin jihohi.

Majiyoyi daga cikin hukumar sun shaida wa jaridar The Nation cewa jami’an INEC sun fara tattara bayanan ƙarshe na ‘yan takarar gwamna da majalisun dokokin jihohi kafin wallafa jerin sunayen.

Jihohin da za a gudanar da zaɓen gwamna

Za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Legas, Ogun, Oyo, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Delta, Enugu, Ebonyi, Abia, Niger, Nasarawa, Kwara da Benue.

Sauran jihohin sun haɗa da Plateau, Yobe, Borno, Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Kebbi, Zamfara da Sokoto.

Sai dai ba za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohin Edo, Bayelsa, Ondo, Ekiti, Osun, Imo, Anambra da Kogi ba.

A gefe guda, za a gudanar da zaɓen majalisun dokokin jihohi a dukkan jihohin Najeriya, ban da Babban Birnin Tarayya, Abuja, wanda Majalisar Ƙasa ke zama ɓangaren dokokinsa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da jam’iyyun da ba su gabatar da ‘yan takara a zaɓen gwamna da na majalisun dokokin jihohi ba.

Kara karanta wannan

Dan takarar ADC a Gombe ya yi alkawura, zai kara da Pantami da Jamilu

Wa’adin sauya sunayen ‘yan takara a zaɓen gwamna da na majalisun dokokin jihohi ya ƙare ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026.

2027: APC ta tura wasika ga INEC

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC ta rubuta wa INEC wasiƙa, tana neman aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan amfani da rajistar mambobin jam’iyyun siyasa.

APC ta ce jam’iyyun da suka gaza miƙa rajistar mambobinsu ta zamani cikin wa’adin doka, ya kamata a hana su tsayar da ‘yan takara.

Jam’iyyar ta buƙaci INEC ta tabbatar da cewa masu rajista ne kawai za su kaɗa ƙuri’a ko neman takara a zaɓen cikin gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.