Kotu Ta Karbe Takarar ‘Dan Majalisar APC bayan Ya Fara Jin Kamshin Tazarce
- Kotun tarayya da ke Jos ta umarci APC ta sake gudanar da zaben fitar da gwani a mazabu 10 a jihar Filato
- Hukuncin ya shafi mazabar Jos ta Kudu/Jos ta Gabas a Filato saboda rashin bin dokoki da ka’idar zabe
- Alkali ta kuma umarci jam’iyyar APC, ‘dan takara da INEC su biya tara bayan an gama sauraron shari’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Jos - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Jos, jihar Filato, ta umarci jam’iyyar APC da ta sake gudanar da zaben tsaida gwani na 2027.
A ranar 9 ga watan Oktoba 2026, Alkali ya ce a shirya sabon zabe ne a mazabu 10 na mazabar tarayya ta Jos ta Kudu da Jos ta Gabas.

Source: Getty Images
Kotu ta soke zaben tsaida gwanin APC a Jos
Jaridar Daily Trust ta ce an bukaci a shirya wani zaben ne a sakamakon samun kura-kurai a zaben farko da jam’iyyar APC ta shirya.

Kara karanta wannan
Wata mata ta fito fili ta bayyana cewa tana taimaka wa yan ta'adda a Arewacin Najeriya
Mai shari’a Dorcas Agishi ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a, bayan sauraron karar da Hon. Esther Bitrus Danboyi ta shigar gabanta.
An ji Mai shari’a tana mai cewa ba su da wata hujjar da za ta sa a amince da kariyar wadanda ake tuhuma.
'Dan takaran majalisa ya rasa tikitin APC
Hon. Esther Bitrus Danboyi ta yi karar Hon. Dachung Musa Bagos, jam’iyyar APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Karar ta shafi zaben fitar da gwani na APC da ya samar da Bagos a matsayin dan takarar jam’iyyar a mazabar, gabanin babban zabe.
Lauyan Danboyi, Ritji Timothy Yilwatda ya shaida wa manema labarai cewa karar ta samo asali ne daga zargin rashin bin ka’idar zabe.
A cewar lauyan, an ki bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, dokar zabe da kuma ka’idojin APC wajen gudanar da tsaida gwanin.
Ya ce Danboyi ta kuma yi zargin cewa ba a ba ta damar samun adalci wajen sauraron korafinta ba, duk da cewa ta shigar da koke a APC.

Kara karanta wannan
Maganar zargin Dickson na shirya wa Obi da Kwankwaso makarkashiya ta yi nisa a NDC
Mazabun da APC za ta sake zabe
Jaridar Punch ta ce a karshe dai kotu ta gano cewa ba a gudanar da zaben da ya dace a mazabun da mai karar ta yi korafi a kansu ba.
Saboda haka, ta umarci jam’iyyar APC da ta gudanar da sabon zaben cikin kwanaki 30, hakan ya bar nasarar Musa Bagos tana kasa tana dabo.
Mazabu 10 da hukuncin ya shafa su ne:
- Du
- Shen
- Zawan ‘B’
- Fobur ‘A’
- Fobur ‘B’
- Jarawan Kogi
- Mai Juju/Doss
- Federe
- Shere East
- Shere West
Kotun ta ci tarar APC, Bagos da INEC
Kotun ta yi watsi da korafe-korafen farko da takardun rantsuwar kare kai da wadanda ake kara suka gabatar a babban kotun tarayyar.
Haka kuma, kotun ta umarci kowane daya daga cikin wadanda ake kara da ya biya Danboyi N500,000 a matsayin kudin shari’a.
Hakan ya sa jimillar kudin da kotun ta umarci a biya ya kai Naira miliyan 1.5, inda Hon. Bagos, APC da INEC za su biya N500, 000.

Source: Getty Images
An zargi APC da kawo wa NDC cikas
A labarin nan ne aka ji cewa kungiyar OK Movement ta gamsu cewa ta kafa kwamitin yakin neman zaben 2027 ba tare da bin doka ba.
OK ta bayyana cewa Peter Obi bai da wata masaniya game da wannan shiri da aka yi ba da izininsa ba don haka ne jam'iyya ta soke shi.
Bugu da kari, OK ta zargi jam'iyyar APC da yunkurin amfani da sabanin nan da bai kai ya kawo ba domin raba kan NDC kafin a shiga zabe.
Asali: Legit.ng
