Kotu Ta Nemi Cafke Tsohon Gwamna da Sanata, an Gano Rashin Gaskiyarsu kan Zabe
- Wata kotun majistare a Abuja ta bayar da sammacin kama tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha
- INEC ta roƙi ’yan sanda da DSS su binciki Okorocha bisa zargin yaɗa sakamakon zaɓen bogi na fitar da gwani na APC
- Hukumar INEC ta ce Gwamna Hope Uzodimma ne ya lashe zaɓen fitar gwani na APC, kuma ta miƙa sunansa a matsayin ɗan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Abuja ta bayar da sammacin kama tsohon gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha.
An bukaci cafke Rochas Okorocha da tsohon Sanata Ifeanyi Araraume, bisa zargin haɗin baki wajen aikata laifi, ƙirƙirar takardu da kuma gabatar da takardun ƙarya.

Source: Facebook
Dalilin kotun na cafke Okorocha, Araraume
Kotun ta kuma bayar da umarnin kama Timothy Ama Chuks da Amen Okorocha, waɗanda ake zargin sun haɗa baki da Rochas Okorocha wajen ƙirƙira da gabatar da sakamakon zaɓen fitar da gwani na APC na bogi, cewar Punch.
Kotun ta bayyana cewa sammacin ya ba dukkan jami’an ’yan sanda a Najeriya izinin kama Okorocha, Araraume, Timothy Chuks da Amen Okorocha, sannan su gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Majistare mai lamba 3 da ke Jiwa, Abuja.
Umarnin kama mutanen ya zo ne a daidai lokacin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta roƙi ’yan sanda da Hukumar DSS su binciki Okorocha bisa zargin yaɗa sakamakon zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar APC da ake zargin na bogi ne.
A cikin sammacin kama mutanen mai ɗauke da ranar 9 ga Satumba, 2026, an tuhumi waɗanda ake nema da haɗin baki wajen aikata laifi, ƙirƙirar takardu da gabatar da takardun ƙarya.

Source: Original
Karar da aka shigar kan Rochas Okorocha
An shigar da ƙarar ne ƙarƙashin lambobin CR/M/JW/084/2026 da CR/M/JW/085/2026, inda Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya ya shigar da ƙara a kan mutanen huɗun.
A wani ɓangare kuma, INEC ta nesanta kanta da wata takarda da Okorocha ke yaɗawa, wadda yake iƙirarin cewa ta nuna shi ne ya lashe zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan
Ta faru ta ƙare: INEC ta shirya fitar da sunayen ƴan takarar gwamna, ƴan majalisu
Hukumar ta bayyana cewa takardar sahihiyar sakamakon da APC ta miƙa mata ta nuna cewa Gwamna Hope Uzodimma ne ya lashe zaɓen fidda gwani. Saboda haka, APC ta miƙa sunansa ga hukumar a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Imo ta Yamma, wato yankin Orlu.
A cikin wata wasiƙa mai tsauri da ta aika wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Imo da takwaransa na DSS, INEC ta bayyana cewa takardar da Okorocha ke yaɗawa ta bogi ce, tare da buƙatar hukumomin tsaro su binciki tsohon gwamnan.
Wasiƙar mai ɗauke da ranar 8 ga Oktoba, 2026, wadda Kwamishinan Zaɓe na Jihar Imo, Chukwuemeka Ibeziako, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa hukumar na kai rahoton wani lamari na “ƙirƙirar rahoton zaɓen fidda gwani na ƙarya da na bogi na APC na kujerar sanata a Jihar Imo, mai ɗauke da ranar 18 ga Mayu, 2026.”
INEC ta bayyana damuwarta cewa, sabanin takardar da APC ta sanya wa hannu tare da miƙa wa hedikwatarta, wadda ta nuna Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani, wata takarda da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ta nuna Okorocha ne ya yi nasara. Wannan ne ya sa hukumar ta shigar da ƙorafi.
Hukumar ta ce:
“Takardar ƙarya ta nuna Sanata Ethelbert Rochas Okorocha a matsayin ɗan takarar jam’iyyar da aka zaɓa bisa kuskure.”
INEC ta haɗa a cikin wasiƙarta da ainihin sakamakon da ya nuna Uzodimma a matsayin wanda ya cancanci lashe zaɓen fitar da gwani, tare da takardar ƙaryar da Okorocha ke yaɗawa.
Rigima ta yi tsanani tsakanin Okorocha, Uzodinma
A wani labarin, tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, ya maka INEC, Hope Uzodimma da APC ƙara a kotu.
Okorocha ya ce shi ne ya lashe zaɓen fitar da gwani na APC, inda ya samu ƙuri’u 150,780, yayin da Uzodimma ya samu 102,158.
Ya bukaci kotu ta soke sunan Uzodimma, sannan ta umarci INEC ta amince da shi a matsayin ɗan takarar APC na Imo ta Yamma.
Asali: Legit.ng

