Tinubu Ya Shirya Kamfen don 2027, Ya Zabi Jihar Arewa da Zai Fara da Ita
- Shugaba Bola Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa na 2027 a Kaduna ranar 24 ga Oktoba, a cewar Sanata Abdulaziz Yari
- Kwamitin yaƙin neman zaɓen APC zai gudanar da taron ƙaddamar da aikinsa a fadar shugaban ƙasa ranar 14 ga watan Oktoban 2026
- Sanata Yari ya ce bayan Kaduna, tawagar za ta kai ziyara Port Harcourt da ke Jihar Ribas, sannan Maiduguri a Jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen sake zaɓensa a shekarar 2027 a Kaduna ranar 24 ga Oktoban 2026.
Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana hakan.

Source: Twitter
Yari ya bayyana hakan ga manema labaran fadar shugaban ƙasa a yammacin ranar Juma’a, 9 ga watan Oktoban 2026 bayan ganawa da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock, Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya gayawa Atiku da Obi hanyar kayar da Tinubu a zaben 2027
Ya ce shugaban ƙasar ya gayyace shi domin samun bayani kan matakin da kwamitin ya kai wajen shirya yaƙin neman zaɓen, tare da tattauna jadawalin ziyarar da za a kai jihohi.
Za a ƙaddamar da kwamitin ranar 14 ga Oktoba
Yari ya bayyana cewa an cimma matsaya kan yadda za a gudanar da yaƙin neman zaɓen, tare da tsara muhimman ayyukan da za a fara yi.
Ya ce za a gudanar da taron farko na kwamitin yaƙin neman zaɓen a ranar 14 ga Oktoba, 2026, a zauren liyafa na fadar shugaban ƙasa.
Sanatan ya ƙara da cewa, idan Allah ya yarda, za a ƙaddamar da kamfen ɗin a hukumance a Kaduna ranar 24 ga Oktoba.
Yari ya ce an kuma tsara ziyarar da za a kai jihohi daban-daban, kuma Tinubu ya amince da jadawalin.
Port Harcourt da Maiduguri za su biyo baya
Da aka tambaye shi jihohin da za a ziyarta bayan Kaduna, Yari ya ce Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, shi ne zai biyo baya, sannan a je Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Sai dai ya bayyana cewa za a fitar da cikakken jadawalin ziyarar bayan ƙaddamar da kwamitin a ranar 14 ga Oktoba. Ya ce an riga an tattauna jadawalin kuma tawagar shugaban ƙasa ta amince da shi.
Yari ya yi magana kan ’yan takarar adawa
Da aka tambaye shi game da ƙalubalen da ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa, Peter Obi da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, za su iya haifarwa, Yari ya nuna kwarin gwiwa kan sake zaɓen Tinubu.
Ya yi amfani da misalin yadda Tinubu ya taimaka wa Atiku da Peter Obi a wasu lokutan baya, yana mai cewa Allah ne ke ƙaddara nasara da rashin nasara, jaridar TheNation ta kawo labarin.
“Muna magana ne kan shugaban ƙasar nan, wanda da ikon Allah, ya taɓa taimaka wa Atiku a wani lokaci, sannan ya taimaka wa Peter Obi."
“Idan Allah ya yi amfani da ni wajen taimaka maka, babu yadda Allah zai yi amfani da kai wajen kawar da ni,” in ji shi.

Source: Facebook
Yan takara sun sauya sheka zuwa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ’yan takarar majalisar wakilai da majalisun dokokin jihohi na jam’iyyun ADC da NDC a zaɓen 2027 sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Masu sauya sheƙar sun haɗa da ɗan takarar majalisar wakilai guda ɗaya da ’yan takarar majalisun dokokin jihohi uku.
Asali: Legit.ng
