Amaechi: Abokin Takarar Atiku Ya Kwadaitawa 'Yan Najeriya Manyan Ayyukan da ADC Za Ta Yi
- Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi, ya yi alkawarin dawo da tallafin fetur da rage tsadar rayuwa idan jam’iyyar ta lashe zaɓen 2027
- Amaechi ya ce rage kuɗin sufuri zai taimaka wajen saukar da farashin kayayyaki da ayyuka, tare da rage matsin tattalin arziƙi ga iyalai
- Ya kuma yi alkawarin ƙara makarantu, yin gyare-gyaren zaɓe da inganta manyan hanyoyin da suka haɗa Edo da sauran sassan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Benin, jihar Edo - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Rotimi Amaechi, ya sake daukarwa 'yan Najeriy alkawari.
Amaechi ya yi alkawarin cewa gwamnatin da jam’iyyar za ta kafa za ta rage tsadar rayuwa tare da dawo da tallafin fetur idan ta lashe zaɓen 2027.

Source: Twitter
Amaechi, tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon Ministan Sufuri, ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da jama’a na ADC da aka gudanar a Benin ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton Vanguard.
ADC za ta dawo da tallafin fetur
Amaechi ya ce tsarin tattalin arziƙin da jam’iyyarsa ke shirin aiwatarwa zai tallafa wa samar da man fetur a cikin gida tare da rage farashin fetur.
A cewarsa, rage farashin fetur zai taimaka wajen saukar da kuɗin sufuri, wanda hakan zai rage nauyin tattalin arziƙi da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Ya ƙara da cewa rage kuɗin sufuri zai taimaka wajen saukar da farashin kayayyaki da ayyuka, tare da sauƙaƙa wa iyalai biyan bukatunsu na yau da kullum.
Sai dai Amaechi ya amince cewa ba za a kawar da talauci nan take ba. Ya ce za a rage shi a hankali ta hanyar manufofin tattalin arziƙi da za su inganta rayuwar jama’a da samar musu da damarmaki, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Amaechi ya yi alkawarin ƙara makarantu da gyara zaɓe
Tsohon gwamnan ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin ADC za ta faɗaɗa damar samun ilimi ta hanyar gina ƙarin makarantu.

Kara karanta wannan
To fa: Gwamnatin tarayya ta yi gargadi kan sababbin hanyoyin da 'yan ta'adda suka bullo da su
Dangane da zaɓe kuwa, ya ce jam’iyyar za ta aiwatar da gyare-gyaren da za su ƙarfafa tsarin zaɓe tare da dawo da amincewar jama’a ga sakamakon zaɓuka.
Amaechi ya tabbatar wa al’ummar Edo cewa idan ADC ta kafa gwamnati, za ta ba su damar zaɓar gwamnan da suke so cikin ’yanci, maimakon a ɗora musu wanda ba su zaɓa ba.
Ya buƙaci jama’a su shiga zaɓen 2027
Amaechi ya yi kira ga masu zaɓe da su fahimci muhimmancin rawar da suke takawa wajen tsara makomar Najeriya ta hanyar shiga harkokin zaɓe.
Ya gargaɗi masu zaɓe da kada su ƙaurace wa rumfunan zaɓe, yana mai cewa alhakin samar da sauyin da suke buƙata yana hannunsu.
Amaechi ya yi maganar lalacewar hanyoyi
A bangaren ababen more rayuwa, Amaechi ya nuna damuwa kan halin da manyan hanyoyin da suka haɗa Edo da sauran sassan ƙasar ke ciki.
Ya ambaci hanyoyin Legas zuwa Benin, Abuja zuwa Benin da kuma hanyar Gabashin Najeriya zuwa Benin a matsayin hanyoyin da ke buƙatar kulawa.
Ya ce gyaran waɗannan hanyoyi zai sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, tare da tallafa wa harkokin kasuwanci da bunƙasar tattalin arziƙin ƙasar.

Source: Facebook
Amaechi ya ce zai yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan mataimakin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan salon mulkin da za su yi.
Amaechi ya ce zai yi murabus idan Najeriya ba ta sauya ba cikin shekara guda na mulkin ADC bayan sun yi nasara.
Asali: Legit.ng

