Ana Shirin Zaben 2027, Jam'iyyun ADC da NDC Sun Samu Koma Baya a Kano da Jihohi 4 na Arewa
- Wasu ’yan takara huɗu na ADC da NDC daga jihohin Sokoto, Jigawa, Kaduna, Kano da Plateau sun sauya sheƙa zuwa APC
- ’Yan takarar sun yi alkawarin samo kuri’u miliyan biyu domin tallafa wa takarar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
- Gidauniyar Baba Tinubu Fisabilillah 2027 ta ce wasu ’yan takarar adawa 23 za su koma APC cikin makonni biyu masu zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wasu ’yan takarar majalisar wakilai da majalisun dokokin jihohi na jam’iyyun ADC da NDC a zaɓen 2027 sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Masu sauya sheƙar sun haɗa da ɗan takarar majalisar wakilai guda ɗaya da ’yan takarar majalisun dokokin jihohi uku. Sun fito ne daga jihohin Sokoto, Jigawa, Kaduna, Kano da Plateau.

Source: Facebook
Princess Aslam-Aliyu, wadda ta kafa ƙungiyar Baba Tinubu Fisabilillah 2027, ce ta jagoranci tawagar zuwa hedikwatar APC ta ƙasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 9 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan
"Ku yafe mini," Tsohon gwamna ya fito ya nemi afuwar yan Najeriya kan kawo masu Tinubu a 2023
Sun yi alkawarin samo wa Tinubu kuri’u miliyan 2
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ne ya karɓi masu sauya sheƙar a hedikwatar jam’iyyar.
’Yan takarar sun yi alkawarin samo kuri’u miliyan biyu domin tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Sun bayyana cewa za su ƙara ƙarfafa goyon bayan APC a matakin ƙananan hukumomi da unguwanni, tare da taimakawa wajen tabbatar da nasarar Tinubu a yunƙurinsa na sake tsayawa takara.
Da take magana a madadin tawagar, Aslam-Aliyu ta ce wasu ’yan takarar adawa 23 za su koma APC cikin makonni biyu masu zuwa.
Ta kuma yi watsi da yiwuwar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ita ta bayyana a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, samun nasara a zaɓen 2027.
Ta yi iƙirarin cewa Atiku zai fuskanci ƙalubale wajen shawo kan shugabannin jam’iyya na matakin gundumomi su koma ADC.

Kara karanta wannan
Dan takarar shugaban kasa ya gayawa Atiku da Obi hanyar kayar da Tinubu a zaben 2027
Aslam-Aliyu ta ce sauya sheƙar ba wai kawai barin wata jam’iyya da shiga wata ba ne, illa alamar amincewa da Tinubu da manufofin Renewed Hope Agenda da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
Ta kuma jaddada cewa APC za ta ci gaba da tattara goyon baya domin sake zaɓen Tinubu a 2027.
Shugaban APC ya kare sauye-sauyen Tinubu
Yayin da yake karɓar masu sauya sheƙar, Yilwatda ya buƙaci ’yan Najeriya su zaɓi ko za su goyi bayan ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki na gwamnatin Tinubu ko kuma su koma abin da ya kira “tsoffin kwanakin duhu” na ƙasar.
"Ba za mu iya komawa tsohon yanayinmu ba. Mun samu ci gaba. ’Yan adawa suna ƙoƙarin kawo tsaiko ga wannan ƙasa.” In ji shi.
Yilwatda ya ce Tinubu bai yi watsi da Arewa ba
Shugaban APC na ƙasar ya kuma ƙaryata zarge-zargen cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin Arewacin Najeriya.
Ya kafa hujja da ayyukan samar da ababen more rayuwa, ayyukan layin dogo da kuma ayyukan iskar gas da yake cewa ana gudanarwa a yankin.
A cewarsa, waɗannan ayyuka na nuna cewa gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin tabbatar da ci gaba mai daidaito a sassa daban-daban na ƙasar.

Kara karanta wannan
Zance ya kare: INEC ta yi magana kan hukuncin kotu da zai iya shafar takarar su Pantami

Source: Twitter
APC ta rubuta wasika ga INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC mai mulki ta rubuta wa hukumar INEC, tana neman ta gaggauta aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.
APC na magana ne kan miƙa rajistar mambobin jam’iyyun siyasa da kuma amfani da ita a zaɓen fidda gwani, tarukan jam’iyyu da manyan tarukansu.
Asali: Legit.ng