Amaechi Ya Fayyace Saukin da za a Samu tun Shekarar Farko idan Atiku Ya Kafa Gwamnati

Amaechi Ya Fayyace Saukin da za a Samu tun Shekarar Farko idan Atiku Ya Kafa Gwamnati

  • Rotimi Amaechi ya yi alkawarin rage tsadar sufuri, man fetur da abinci idan suka lashe zaben shugaban kasa
  • Ya ce gwamnatin da za su kafa za ta mayar da hankali kan farfado da tattalin arziki da rage tsadar rayuwa
  • ‘Yan adawa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 musamman ADC sun yi alkawarin cewa za su dawo da tallafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Tsohon ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi ya yi alkawari gwamnatinsa za ta kawo wa jama’a sauki.

Rotimi Amaechi ya ce gwamnatin Atiku Abubakar za ta karya kudin zirga-zirga, farashin man fetur da tsadar abinci.

Rotimi Amaechi
Rotimi Amaechi da Atiku Abubakar lokacin yi masa ta'aziyya Hoto: Chibuikwe R. Amaechi
Source: Facebook

Rotimi Amaechi ya yi alkawarin kawo sauki

A hirar da gidan talabijin Channels ya yi da shi, Rotimi Amaechi ya ce duk za su yi wannan ne cikin shekarar farko a ofis.

Kara karanta wannan

Amaechi ya zargi Shugaban kasa Tinubu da hannu a mutuwar mahafiyarsa

Ya soki salon mulkin Bola Ahmed Tinubu, ya ce an jefa mutane cikin matsi saboda cire tallafin fetur da tsadar shan lantarki.

‘Dan takaran mataimakin shugaban kasar na ADC yake cewa tunda Tinubu ya karbi ragamar mulki, mutane suke wayyo Allah.

Ya ce:

"Kowa yana shan wahala, kowa yana neman abincin da zai ci.
"Mutane ba su iya sayen fetur su yi tafiya. Kamfanonin jiragen sama na barazanar kara kudin jigila; komai ya tashi."

Bola Tinubu ya gaza cika alkawarin gyara wuta

An ji tsohon gwamnan na Rivers yana zargin Tinubu da yin alkawarin gyara wutan lantarki amma ya ce ya gagara cikawa.

Yake cewa shugaba Tinubu bai da damar da zai bude baki ya yi wata magana.

"Ya yi alkawarin gyara wutar lantarki kuma ya ce idan bai samar da wuta ba, ka da a zabe shi.
"'Yan Najeriya suna jiran su yi waje da shi daga kan mulki ba."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An buɗe wa Tinubu ƙofar da zai iya raba Atiku da mataimakinsa kafin zaɓen 2027

- Rotimi Amaechi

Gwamnatin ADC za ta maido tallafin fetur

The Nation ta ce Amaechi ya kara nanata alwashin Atiku Abubakar na dawo da tallafin fetur saboda talaka ya samu sa’ida.

Ya yi kaca-kaca da yadda tun a ranar farko, shugaban kasa ya sanar da cewa gwamnati ta daina biyan tallafin man fetur.

A sakamakon haka ne ya ce kudin hatsi, kayan miya da sauran abinci suka tashi a Najeriya.

Amaechi ya ce lantarki zai rage tsada

A bangaren wuta, ya ce gwamnatin ADC za ta rusa kason da aka yi zuwa sahu na A, B, C, D da E ga masu sayen lantarki a kasar.

Ya bada misali da kan shi, ya ce:

"Kudin wutan da na ke sha N500, 000 ne; yanzu N4m na ke biya. Idan Atiku ya zo za a koma N500, 000.
"Babu maganar Ban A ko B domin gwamnati za ta sa tallafi ba."

Kara karanta wannan

Atiku ya yi Alƙawarin warware matsalar da ta fi damun yan Najeriya kan INEC da tsarin zabe

Rotimi Amaechi da Atiku Abubakar
Rotimi Amaechi da Atiku Abubakar tare da wasu manyan 'yan siyasa Hoto: Chibuikwe R. Amaechi
Source: Facebook

Amaechi: Manufofin Tinubu sun kashe tsohuwarsa

An ji labarin yadda shugaban kasa ya ‘kashe’ mahafiyar Rotimi Amaechi tana shekaru kusan 90 a duniya a cewar 'dan siyasar.

Abokin gamin Atiku Abubakar a ADC ya ce ba don zuwan Bola Tinubu ba, da gyatumarsa na raye kamar sauran masu tsawon rai.

Amaechi ya yi alkawari gwamnatin ADC za ta mayar da hankali kan muhimman sassa idan ta samu nasara a zaben da za a yi a badi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng