Cikakken Tarihin Bola Tinubu: Shekarunsa, Dukiyarsa, Ƴaƴansa, Matarsa, Mahaifyarsa, Gidajensa Da Motocci

Cikakken Tarihin Bola Tinubu: Shekarunsa, Dukiyarsa, Ƴaƴansa, Matarsa, Mahaifyarsa, Gidajensa Da Motocci

Bola Tinubu fitaccen dan siyasan Najeriya ne, jagoran kasa kuma akanta. Ya yi wa kasarsa aiki ta hanyar rike mukaman siyasa daban-daban. Tinubu shine tsohon gwamnan jihar Legas. Ya yi mulki wa'adi biyu tsakanin Mayun 1999 zuwa Mayun 2007.

Bola Tinubu
Bola Tinubu sanya da farar babban riga ta maza. Hoto: Bola Tinubu
Asali: UGC

Bola muhimmin dan siyasa ne kuma jagoran kasa a Najeriya. Shi mamba ne na jam'iyyar All Progressives Congress, APC. Yana kuma da sarauta na Asiwaju na Legas da Jagaban na masarautar Borgu.

Takaitaccen Bayani

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Cikaken SunaBola Ahmed Adekunle Tinubu
Sunar da ya yi fice da shiBola Tinubu da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
JinsiNamiji
Ranar Haihuwa29 ga watan Maris na 1952
Alamar taurariAries
Garin haihuwaJihar Osun, Najeriya
MahaifiyaAbibatu Mogaji
Shekaru70 (a Janairun 2023)
KasaDan Najeriya
KabilaDan Afirka
AddiniMusulunci
Sana'aDan siyasa, Jagoran kasa, Akanta
Makarantar FiramareSt John Primary School Legas da Childrens Home School, Ibadan
SakandareRichard J Daley College, Chicago, Illinois, USA
Jami'aJami'ar Jihar Chicago, Illinois, USA
Shaidar KaratuDigiri a kimiyyar aikin Akanta
Shekarar gama karatu1979
Matsayin aureYana da aure
MataOluremi Tinubu
'Ya'ya4
Fitaccen dan uwaAttorney Adewale Tinubu
DukiyaDalla Biliyan 4
Facebook@officialasiwajubat
Twitter@officialabat
Shafin intanetwww.bolatinubu.com

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bidiyo Ya Fito Yayin Da Mutane Ke Yi Wa Sarkin Kano Ihu A Wurin Rantsar Da Abba Gida Gida

Tarihin Bola Tinubu

Bola bai bada wani bayani ba dangane da mahaifinsa ko yan uwansa. Mahaifiyarsa, Abibatu Mogaji, ta rasu a ranar 15 ga watan Yunin 2014 tana da shekara 68. Mahaifiyar Bola yar kasuwa ce kuma daga bisani ta zama 'Maman Kasuwa (Iyaloja) na Legas.'

Menene ainihun sunan Bola Tinubu?

An haifi Bola ne a ranar 29 ga watan Maris a 1952 a jihar Osun, Najeriya, cikaken sunansa Bola Ahmed Adekunle Tinubu.

Shekarun Bola Ahmed Tinubu nawa?

Shekarun Bola Tinubu 70 a Janairun 2023.

Karatunsa

Bola ya yi karatun frimari a St John Primary School a Aroloya, Jihar Legas, daga bisani ya koma makarantar Childrens Home a Ibadan. A 1975, Bola Tinubu ya tafi Amurka, inda ya shiga makarantar Richard J College a Chicago, Illinois.

Bayan kammala high school 'babban sakandare' ya shiga Jami'ar Jihar Chicago. Bola ya samu digiri a bangaren kararun Akanta a 1979.

Kara karanta wannan

Najeriya ta Karrama Mamman Daura, Matar Tinubu, Ganduje da Wasu 340 da Lambar Girma

Aikin da Tinubu ya yi a matsayin akanta

Ya yi wa kamfanoni da dama aiki a matsayin akanta, wasu daga cikinsu sune:

 • Arthur Anderson Limited Liability Partnership
 • Deloitte, Hasins & Sells
 • GTE Services Corporation

Bayan aiki a Amurka na shekaru, ya dawo Najeriya a 1983. Bola Tinubu ya fara aiki da Mobil Nigeria, bayan dan lokaci aka nada shi shugaba.

Yadda Tinubu ya fara siyasa

Bola ya fara siyasa a 1992. Ya shiga jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, daya cikin manyan jam'iyyun a wancan lokacin. An zabi shi a matsayin dan majalisar Legas ta Yamma a majalisar dattawa a jamhuriya ta uku wacce bata dade ba.

Bayan soke zaben June 12 a 1993, ya zama daya cikin wadanda suka kafa National Democratic Coalition. Kungiyar ta yi fafutikan dawo da demokradiyya kuma ta amince da Moshood Abiola a matsayin wanda ya lashe zaben June 12.

Bayan juyin mulki na 1993 a watan Nuwamba da Sani Abacha ya jagoranta, Tinubu ya yi gudun hijirar dole. Ya dawo Najeriya a 1998 bayan mutuwar Abacha. A Janairun 1999, ya yi takarar gwamna a Legas a jam'iyyar AD. An zabe shi gwamna.

Kara karanta wannan

Oluremi Tinubu: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Matar Zababben Shugaban Kasa

Wasu cikin nasarorin gwamnatin Bola Tinubu a matsayin gwamnan Legas

 • Ya fara aiki a matsayin gwamna a 1999. A wa'adinsa na farko ya yi wannan ayyukan.
 • Ya samarwa marasa karfi gidaje 10,000.
 • Ya saka hannun jari sosai a bangaren ilimi a Legas.
 • Ya rage adadin makarantu ta hanyar mayar da su zuwa ainihin masu shi.
 • Ya fara gina sabbin tituna.

A Afrilun 2003, ya sake cin zabe a matsayin gwamnan Legas. Ya kammala wa'adinsa a ranar 29 ga watan Mayun 2007.

Yana da sarautun gargajiya biyu. Shine Asiwaju na Legas don haka sunansa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Shine kuma Jagaban na masarautar Borgu a jihar Neja.

Matar Bola da yayansa

Tsohon gwamnan na Legas ya auri Oluremi Tinubu. Ita ce first lady na Legas daga 1999 zuwa 2007. Yanzu ita ce sanata mai wakiltar Legas central.

Yaran Bola Tinubu

Oluremi da Bola Tinubu suna da yara hudu. Folashade Tinubu-Ojo, Oluwaseyi Tinubu, Abibat Tinubu da marigayi Jide Tinubu. Yaran Tinubu suna harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Karar da PDP Ta Nemi a Soke Takarar Tinubu da Shettima

Gidajen Tinubu da motocinsa

Tsohon gwamnan na jihar Legas yana daya cikin mutane masu dukiya a kasar. Ana iya fahimtar hakan idan aka lura da irin gidajensa da da motocci.

A yanzu yana da katafaren gida a Bourdillon Road, Ikoyi Legas. Babu cikkaken bayani yadda cikin katafaren gidan ya ke. Yana kuma da gidaje a Ikoyi Estate Forestore da wasu gidajen. Yana da motocci a kalla 30. Wasu shi ya siya, wasu kuma abokai suka bashi kyauta.

A cikinsu akwai Land Range Rover, Prado Jeep, da sauransu. Tsohon gwamnan kuma yana da jirgin sama kirar Bombardier Global 6000 Express jet. Kudinsa ya dara dalar Amurka miliyan 75.

Dukiyar Tinubu

Dukiyar Tinubu ta kai kimanin $ 4 miliyan. Shine dan siyasa mafi arziki na biyu a Najeriya. Dukiyarsa sun hada da manyan motoccin alfarma, jirgin sama, gidaje da filaye a sassan kasar.

Me ya faru da Bola Ahmed Tinubu?

 • A Yunin 2022, jam'iyyar APC ta zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasarta.
 • Wasu abubuwa dangane da Bola Tinubu
 • Ya taka muhimmin rawa a kafa jam'iyyar APC a 2013

Kara karanta wannan

Ma’aikatar Gwamnati Ta Samu Sabon Shugaba Ana Saura Awa 96 Buhari Ya Sauka

A Janairun 2019, hukumar EFCC ta wanke shi kan zargin hadin baki, yin amfani da ofis ba bisa ka'ida ba, almundahar kudi da rashawa da ke da alaka da hannun jarin V Mobile a 2004, tare da gwamnan Akwa Ibom, Obong Victor Attah, da James Ibori na Delta.

Bola Tinubu ya goyi bayan tsare-tsaren gwamnati da jadadda siyasar cikin gida yayin gwamnatin Buhari lokacin yana shirin takara a 2023.

A 2019, ya goyi bayan tazarcen Buhari kuma ya taimaka masa ya kayar da Atiku Abubakar na PDP.

“Na Hango An Rantsar Da Shi a Matsayin Shugaban Kasa”: Fasto Ya Yi Sabon Hasashe Kan Tinubu

A bangare guda, Theophilus Olabayo, Shugaban cocin Evangelical Church of Yahweh Worldwide, ya yi hasashen cewa za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya na gaba a ranar 29 ga watan Mayu.

Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, da kuri'u fiye da miliyan takwas.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Buhari 14 Da Aka Fi Damawa Da Su A Gwamnatin Tarayya Daga 2015 Zuwa Yanzu

Amma, wasu daga cikin yan takara da suka fafata da shi a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu suna kotu don kallubalantar nasarar ta Tinubu bisa dalilai daban-daban da suka ce sun janyo cikas ga zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel