Dalilin Atiku na Jawo Amaechi Su Yi Takarar Shugaban Kasa tare a ADC Ya Fito Fili

Dalilin Atiku na Jawo Amaechi Su Yi Takarar Shugaban Kasa tare a ADC Ya Fito Fili

  • Kenneth Okonkwo ya nuna abin da ya sa Rotimi Amaechi ya samu tikitin takara a jam’iyyarsu ta ADC
  • Atiku Abubakar ya tafi da tsohon gwamnan Rivers ne ganin kusan ya fi kowa kusanci da ‘yan kabilar Ibo
  • Sauya-shekar Peter Obi zuwa NDC ta kawo wa Atiku cikas, Mista Okonkwo ya ce shiyasa aka tafi da Amaaechi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Babban kusa a jam’iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya kare matakin da Atiku Abubakar ya dauka na jawo Rotimi Amaechi.

Atiku Abubakar ya zabi Rotimi Amaechi ya zama abokin gaminsa, ya zama masa ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC.

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Atiku Abubakar wajen kamfe a 2023 da Rotimi Amaechi a Majalisar dattawa a 2015 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Keneth Okokwo ya yi maganar tikitin ADC

An ji Keneth Okonkwo a tashar Channels ya ce an jawo shi ne domin ka da mutanen Kudu maso gabas su ji ana yi babu su a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

‘Kun ce ba ku son tsoho’, Sule Lamido ya yi watsi da masu kiran ya fito takara

Da aka yi masa magana game da zabin tsohon ministan sufurin, sai ‘dan siyasar ya yi bayanin yadda ADC ta iya cin ma wannan matsaya.

Wasu sun so abokin gamin Atiku Abubakar ya zama Ibo daga Kudu maso gabas kamar yadda ‘dan siyasar ya saba yi a zabukan baya.

Mista Okonkwo ya ce sai da ta yi zama na cikin gida, aka tuntubi manyan ‘ya ‘ya kuma aka shawo kan duk wasu korafi da za a samu.

A hirar ya ce daukacin ‘yan jam’iyyar hamayyar suna goyon bayan tikin Atiku-Amaechi. The Sun ta dauko rahoton a ranar Alhamis.

Kenneth Okonkwo ya ce:

“ADC ta sanar da Rotimi Amaechi a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar
Kuma yadda mu ke aikinmu, idan irin hakan ta tashi…mukan zauna a bayan labule mu sasanta, a tattauna a siyasance domin a samuy matsaya, kuma mu hada kai mu yi aiki.

Kakakin yakin neman zaben na Atiku ya ce ana faman tattauna wa a yanzu domin shawo kan korafe-korafe kuma a shiryawa zaben 2027.

Kara karanta wannan

Yadda ‘yan sanda suka shiga suka fita aka damko shugaban ma’aikatar bogi a wani kauye

Tsohon ‘dan wasan kwaikwayon ya gyara maganganun da ya yi a baya, ya ce tun farko shi bai adawa da Rotimi Amaechi a jam’iyyarsu ta ADC.

Abin da Okonkwo yake nema shi ne a samu Ibo a tikitin shugaban kasa ganin ba su taba shiga Aso Rock ba tun daga shekarar 1999 har zuwa yau.

Atiku
Atiku Abubakar a lokacin kamfe a PDP Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewarsa, ficewar Peter Obi daga ADC ta lahanta Atiku Abubakar, sai ya bar shi bai da zabi sosai daga jihohin da ke Kudu maso gabas.

Saboda babu yadda zai yi, Okonkwo ya ce sai Atiku ya zakulo Amaechi domin yana da kusanci na siyasa da yanki da mutanen kabilar Ibo.

Tsohon ‘dan wasan kwaikwayon ya kuma ce Atiku bai da wata kiyayya a kan Ibo kuma yanzu duk kansu a hade yake kuma babu baraka.

Shiyasa duk da haka Atiku Abubakar ya tafi ya dauko mutumin da ya fi kusanci da Kudu maso gabas.

- Kenneth Okonkwo

Peter Obi zai ci zabe a 2027?

Rahoto ya zo cewa Sanatan Kano, Rufai Hanga ya sace guiwar Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi hasashen Atiku Abubakar zai sha gaban Peter Obi

Kara karanta wannan

Tsakani da Allah Peter Obi ba zai iya cin zabe ba in ji Sanatan NDC, Rufai Hanga

Sanatan wanda na hannun daman Kwankwaso ne ya ce Peter Obi ba zai ci zabe a 2027 ba, amma yana ganin ADC za ta iya ganin bayan APC.

Rufai Hanga, ya ce 'dan takaran ADC a Anambra kurum zai ci zabe kuma Kwankwaso Kano kurum yake da karfi, a nan ma rabi-da-rabi a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng