'Yan Ta'adda Sun Tarwatsa Gangamin APC a Borno, Sojoji Sun Kai Dauki

'Yan Ta'adda Sun Tarwatsa Gangamin APC a Borno, Sojoji Sun Kai Dauki

  • Wasu ’yan ta’adda da ake zargin ’yan Boko Haram ne ko ISWAP sun kai hari kan gangamin yakin neman zaben APC a Kukawa da ke jihar Borno
  • Rahoto ya ce maharan sun harba bama-bamai uku kan garin, inda suka yi niyyar kai wa tawagar Sanata Mohammed Mungono hari
  • Sai dai dakarun Operation Hadin Kai sun dakile harin tare da taimaka wa sanatan da sauran manyan ‘yan siyasa da ke tare da shi tserewa ba tare da rauni ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Maiduguri – Wasu ’yan ta’adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne ko kuma kungiyar ISWAP sun tarwatsa gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a Kukawa da ke jihar Borno.

Rahoto ya ce maharan sun harba bama-bamai guda uku a kan garin a ranar Talata, inda suka nufi tawagar Sanata Mohammed Mungono, babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa kuma mai wakiltar mazabar Borno ta Arewa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan ta'adda sun kai hari kan tawagar Sanata Monguno da wasu jiga jigan APC

Gwamna Zulum a Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum a Borno. Hoto: Dauda Iliya
Source: Twitter

Premium Times ta wallafa cewa Mungono, wanda ke neman sake komawa majalisar a zaben da ke tafe, na tare da tsohon gwamnan jihar Borno, Maina Lawan, da wasu manyan ‘yan siyasa a lokacin da aka kai harin.

Sojoji sun dakile harin

Rahoton ya bayyana cewa wasu majiyoyi sun yi gargadin cewa ’yan ta’addan na shirin kawo cikas ga gangamin, lamarin da ya sa aka tura jami’an tsaro zuwa yankin.

Sai dai dakarun Operation Hadin Kai, rundunar hadin gwiwa da ke yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas, sun dakile harin tare da taimaka wa Mungono da tawagarsa tserewa ba tare da sun ji rauni ba.

Rahoton ya kara da cewa dakarun sun kuma dakile wasu yunkurin kai hari kan garin a tsawon daren Talata.

Haka kuma, an dakile wani harin da aka yi yunkurin kai wa kauyen Kekeno da ke Kukawa a safiyar ranar Talata.

Sai dai rundunar Operation Hadin Kai ba ta fitar da sanarwar hukuma kan lamarin ba, yayin da kakakinta, Mohammed Goni, bai mayar da martani kan tambayar da aka aika masa ba.

Kara karanta wannan

An bayyana mutanen da aka kama bayan kai wa Kwankwaso hari a Kano

Tarihin hari kan ‘yan siyasar Borno

Kai hari kan ‘yan siyasa da harkokin yakin neman zabe ba sabon abu ba ne ga ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya.

A ranar 3 ga Satumba, Mustapha Gubio, dan takarar gwamnan Borno na APC, ya tsallake rijiya da baya bayan mayakan sun kai masa hari a kan hanyar Gubio zuwa Kareto da Damasak, yayin da yake tafiya domin ziyartar magoya bayan jam’iyya.

Rahotanni sun ce maharan sun yi amfani da bama-bamai da rokoki, amma jami’an tsaron da ke rakiyar dan takarar sun fatattake su. An lalata motar yaki ta ‘yan sanda, amma ba a samu asarar rai ba.

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

A watan Fabrairun 2019, mayakan sun kai hari kan tawagar motocin tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, inda suka kashe akalla mutum uku, ciki har da soja da wani mamba a tawagar yakin neman zabensa.

Shugaban APC ya yi hadari

A wani labarin, mun rahoto cewa shugaban APC na Gombe, Mohammed Dantata Ndus, da daraktan kamfen, Sa’adu Hassan, sun samu raunuka a wani hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan adawa ke kara kokarin haduwa su kifar da Tinubu a 2027

Hatsarin ya faru ne a ranar Talata a mahadar Deba zuwa Talasse, yayin da shugabannin jam’iyyar ke kan hanyarsu ta zuwa karamar hukumar Balanga ta Arewa.

Kwamitin yakin neman zaben APC ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana sunayen wadanda suka rasu a matsayin Haruna da Kabiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng