Yawan Murabus Ya Rikita Katsina kan Rashin Jituwar Gwamna Radda da Masari
- Ana ci gaba da samun yawan murabus daga gwamnatin Gwamna Dikko Umar Radda yayin da ake samun sababbin sauye-sauyen siyasa a Katsina
- Wasu majiyoyi sun ce wasu daga cikin wadanda suka yi murabus makusantan Ibrahim Masari ne, mai bai wa Tinubu shawara kan harkokin siyasa
- Masana sun ce murabus din na iya nuna rashin jituwar cikin gida a APC Katsina, amma wadanda abin ya shafa ba su tabbatar da hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Ana yawan samun murabus a gwamnatin jihar Katsina, inda akalla masu mukamai biyar suka ajiye aikinsu.
Murabus din ya jawo hankalin ‘yan siyasa saboda lokacin da aka yi shi da kuma yawan jami’an da suka bar gwamnatin cikin kankanin lokaci.

Source: Facebook
Haka kuma, mutane da dama sun alakanta lamarin da lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa tsakanin mambobin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Katsina, cewar Daily Trust.
Jami'an da suka yi murabus a Katsina
Wanda ya yi murabus na baya-bayan nan shi ne Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina mai kula da ayyuka, Muhammad Shitu Maslaha.
Maslaha ya gabatar da wasikar murabus dinsa mai kwanan wata 6 ga Oktoba, 2026, inda ya bar mukaminsa a hukumar Hisbah ta jihar.
Murabus dinsa ya zo kwana daya bayan Kwamandan Janar na Hukumar Hisbah, Dr Aminu Usman, wanda aka fi sani da Abu Ammar, ya bar mukaminsa ranar Litinin, 5 ga Oktoba.
Hakan ya biyo bayan murabus din Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Kabir Bature Sarkin Alhazai.
Sarkin Alhazai ya yi murabus bayan ya shafe shekaru yana rike da mukamin tun bayan da Gwamna Radda ya nada shi a shekarar 2023.
A cikin wadanda suka yi murabus akwai Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Gwamna kan Aiwatarwa, Sa Ido da Tantance Ayyukan Jihar Katsina, Fadila Sani Dalhatu.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
Fadila ta gabatar da wasikar murabus dinta mai kwanan wata 5 ga Oktoba, yayin da Alhaji Abubakar Soja Tsanni shi ma ya bar mukaminsa.

Source: Facebook
Menene dalilin jami'an na yin murabus?
Sai dai har yanzu ba a bayyana dalilan da suka sa jami’an suka yi murabus ba, domin babu wanda ya danganta matakin da wata rashin jituwa da Gwamna Radda.
Gwamnatin jihar ma ba ta bayyana cewa murabus din yana da alaka da juna ba ko kuma cewa wata matsalar siyasa ce ta cikin gida ta haddasa su.
Sai dai masu lura da siyasa sun yi imanin cewa lamarin na iya kasancewa da alaka kai tsaye ko a kaikaice da zargin rashin jituwar cikin gida a APC Katsina.
Manyan ‘yan siyasar da ake alakanta su da wannan sabani sun sha musanta cewa akwai wani rikici tsakaninsu ko kuma wata matsala a jam’iyyar.
Wata majiya a APC jihar ta shaida cewa wasu daga cikin tsofaffin jami’an sun fara kusantar bangaren Ibrahim Kabir Masari, cewar Punch.
Muƙamin da Masari ke da shi a sama
Ibrahim Masari shi ne mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan harkokin siyasa, kuma yana da tasiri a siyasar Katsina da Abuja.
Majiyar ta ce wasu daga cikin wadanda suka bar gwamnatin Dikko kwanan nan sun koma layin Ibrahim Masari domin hada kai da bangaren APC na Abuja da Katsina.
Wasu majiyoyi kuma sun danganta murabus din da wata magana da ake zargin Gwamna Radda ya yi wa jami’an a gwamnatinsa.
A cewar wadannan majiyoyi, gwamnan ya bukaci jami’an da ba sa samun damar da suke bukata ko kuma ba sa iya bayar da gudunmawa su yi murabus.
Sai dai ba a iya tabbatar da wannan magana ta gwamna da kansa ba, ko kuma ko tana da alaka kai tsaye da murabus din jami’an.
Gwamna Radda na cikin wadanda za a karrama
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya za ta karrama wasu daga cikin gwamnonin Arewacin Najeriya saboda nasarorin fasahar zamani ciki har Dikko Umaru Radda.
Za a gudanar da bikin bayar da lambar yabo a Abuja ranar 13 da 14 ga Oktoba, yayin taron Nigeria GovTech na karo na huɗu.
Bikin zai mayar da hankali kan amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan gwamnati da bunƙasa tattalin arziki na zamani.
Asali: Legit.ng

