Bayan Malamai, Tawagar Tinubu Ta Koma kan 'Yan Agajin Darika da Izala

Bayan Malamai, Tawagar Tinubu Ta Koma kan 'Yan Agajin Darika da Izala

  • Kungiyar agaji ta 'Joint Islamic First Aid Organization' reshen birnin tarayya FCT ta nuna goyon bayanta ga sake zaben Shugaba Bola Tinubu
  • Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga ci gaba da tsarin tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi a jam'iyyar APC
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan al'amuran siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar a ofishinsa da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan al'amuran siyasa da sauran muhimman al'amura, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya karɓi bakuncin shugabannin ƙungiyar agaji ta Joint Islamic First Aid Organization reshen birnin tarayya Abuja.

Tawagar ƙungiyar wadda shugabanta Alhaji Ahmad Jingi Adamu ya jagoranta, ta ziyarci Masari ne a ofishinsa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alhini da Allah ya yi wa sakataren Majalisar shari'ar Musulunci rasuwa

Ibrahim Kabir Masari da 'yan agajin Izala da Darika
'Yan agaji bayan ganawa da hadimin shugaba Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Ibrahim Kabir Masari
Source: Facebook

Ibrahim Masari ya wallafa a Facebook cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ayyukan agaji, cigaban ƙasa, faɗaɗa goyon baya a matakin ƙasa, da kuma ci gaba da aiwatar da tsarin Renewed Hope na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

'Yan agaji sun yabi Tinubu

Yayin da yake jawabi a taron, Alhaji Ahmad Jingi Adamu ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ɗari bisa ɗari ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027.

Ya nuna kwarin gwiwa kan kyakkyawan tsarin da gwamnatin ke kaiwa wajen sauya fasalin tattalin arziki da zamantakewar Najeriya.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta bayyana cewa tana goyon bayan a ci gaba da amfani da tsarin takara na Musulmi da Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa na 2027.

A nasa martanin, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya yabawa tawagar wajen ci gaba da jajircewa kan wannan tafiya, inda ya yi kira gare su da su jajirce wajen goyon bayan tikitin na Musulmi da Musulmi "saboda Allah."

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, INEC ta ɗora sabon tambarin jam'iyyar su Kwankwaso a shafinta

Kiraye-kiraye ga 'yan agaji

Haka zalika, wani memba a tawagar, Sheikh Ibrahim Lawal Usama, ya kira mambobin ƙungiyar da su kasance masu riƙon amana da jajircewa kan goyon bayan tikitin Musulim Muslim tare da gudanar da lamarinsu da kyakkyawar niyya da kwarin gwiwa.

Ya kuma buƙaci mambobin da su kiyaye haɗin kai, zaman lafiya, da shiga aikin dimokuraɗiyya cikin tsari da bin doka gabanin zaɓen 2027.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na yi wa jama'a bayani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mai ba shugaban ƙasar shawara ya jinjina wa ƙungiyar kan ayyukan agaji da suka sa gaba a tsakanin al'umma, yana mai jaddada muhimmancin ƙungiyoyin al'umma wajen gina haɗin kan ƙasa da haɓaka jin daɗin jama'a.

Wakilan ƙungiyar sun nuna godiyarsu ga Masari bisa karɓar da ya yi musu tare da alƙawarin bayar da gudunmawa wajen wayar da kan jama'a gabanin zaɓen 2027.

Tinubu ya gana da Oba Akiolu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ban girma ga sarki Oba na Lagos, Oba Rilwan Akiolu, a fadarsa da ke Iga Idunganran a tsibirin Lagos.

Kara karanta wannan

An tara malamai a masallaci sun yi wa Tinubu addu'a a Sokoto

Ziyarar ta bawa shugaban ƙasar damar samun addu’o’i da kuma shawarwari daga sarakunan gargajiya domin gudanar da gwamnatinsa cikin nasara.

Mambobin gidan sarautar da kuma tarin al'ummar yankin ne suka tarbi Tinubu tare da gudanar da jerin gwano na murnar zuwansa a yankin Marina da Isale Eko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng