Gwamnatin Kano Ta Fadi Karyar da Ta Ce an Shirya kan kai wa Kwankwaso Hari
- Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi Kwankwasiyya da ƙirƙiro labarin cewa an kai wa tawagar Rabiu Kwankwaso hari a Bichi
- Sanusi Bature ya ce babu hotuna ko bidiyo da suka tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an ƙirƙiro zargin ne domin samun tausayin jama’a
- Sai dai kakakin ɗan takarar gwamnan NDC ya tabbatar da harin, inda ya ce an raunata wasu tare da lalata motoci kusan bakwai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi ƙungiyar Kwankwasiyya da ƙirƙiro labarin cewa an kai wa tawagar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a ƙaramar hukumar Bichi.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da samun rahotannin kai wa 'yan siyasa hari, musamman 'yan adawa a lokutan kamfen.

Source: UGC
Kwamishinan ya yi wannan zargi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar da sahihancinsa, inda ya nuna shakku kan faruwar harin.
Bature ya karyata harin
Sanusi Bature ya bayyana cewa rahoton harin na iya kasancewa wani yunƙuri ne na neman tausayin jama’a ga mambobin Kwankwasiyya.
Ya ce babu hotuna ko bidiyo da aka fitar domin tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa:
“A ƙoƙarin neman tausayin jama’a, tawagar Kwankwasiyya ta ƙirƙiro wani harin ƙarya a Bichi, babu hotuna, babu bidiyo.”
Yadda aka ce harin ya faru
Sai dai kakakin ɗan takarar gwamnan NDC, Ibrahim Garba Shu’aibu, ya tabbatar da cewa an kai wa tawagar hari.
Ya ce tawagar ta kammala ziyartar ƙananan hukumomin Tofa, Rimingado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai ba tare da samun wata matsala ba.
A cewarsa, sun samu rahoton cewa wasu mutanen da ba sa goyon bayan gangamin sun tare hanyar da za su bi zuwa Bichi.
Ya bayyana cewa bayan isarsu Bichi, sun ga alamun jifan motoci kafin su wuce gaban sakatariyar ƙaramar hukumar, inda wasu fusatattun matasa ɗauke da makamai suka fito suka far musu.
An ce an raunata mutane
Daily Trust ta rahoto cewa Shu’aibu ya yi zargin cewa maharan sun raunata wasu daga cikin tawagar kamfen tare da lalata motoci da dama.
A bayanin da ya yi, Shuaibu ya ce da kansa ya ga motoci kusan bakwai da aka farfasa a yayin harin.
Sai dai kwamishinan ya kuma yi tsokaci kan yadda NDC ta ziyarci ƙananan hukumomi bakwai a rana guda, yana mai cewa duk wanda ya san yadda gangamin siyasa ke gudana a Kano zai fahimci muhimmancin hakan.

Source: Twitter
Maganar da Obi ya yi
A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da rahoton harin da aka kai wa tawagar Kwankwaso a Bichi.
Obi, wanda ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan’uwansa kuma abokin takararsa, ya ce ya yi matuƙar baƙin ciki da labarin raunata wasu mambobin tawagar da lalata motoci kusan bakwai.
Ya ce bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama dalilin tashin hankali, tsoratarwa ko lalata dukiyoyi ba, yana mai jaddada cewa dimokuraɗiyya ba yaƙi ba ce.
Asali: Legit.ng

