Tinubu Ya Yi Alhini da Allah Ya Yi wa Sakataren Majalisar Shari'ar Musulunci Rasuwa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini kan rasuwar Babban Sakatare na MJalisar Shari'a ta Najeriya (SCSN) na kasa, Malam Nafiu Baba-Ahmed
- Rahotanni sun nuna cewa Malam Nafiu Baba-Ahmed ya rasu ne a safiyar Talata bayan rayuwarsa ta hidima ga Musulunci da Najeriya
- Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai tasiri da ya jagoranci majalisar cikin hikima da hangen nesa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matuƙar alhini kan rasuwar Babban Sakatare na Majalisar harkokin shari'ar Musulunci ta Najeriya (SCSN), Malam Nafiu Baba-Ahmed.
Malam Baba-Ahmed, wanda ya kasance ƙwararren mai gudanarwa kuma jagoran addini da ake girmamawa, ya rasu ne a safiyar yaubTalata bayan doguwar rayuwa ta hidima ga Musulunci da ƙasa.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana saƙon Shugaban Ƙasa a cikin wata sanarwa.
A cewar Onanuga, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai tasiri wanda ya jagoranci harkokin majalisar shari'ar musulunci ta Najeriya cikin hikima, hangen nesa da kuma jajircewa wajen tabbatar da haɗin kai, adalci da zaman lafiya.
Tinubu ya tuna da Baba-Ahmed
Shugaban Ƙasa ya tuna da doguwar alaƙarsa da marigayin, musamman lokacin shirye-shiryen zaɓen 2011 da kuma shekarun da suka biyo baya zaben.
Ya kuma tuna da shawarwari da goyon bayan da Malam Nafiu Baba-Ahmed ya ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a shekarar 2023.
Tinubu ya ce Baba-Ahmed ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa majalisar ta ci gaba da bayyana matsayinta kan batutuwan ƙasa, tare da inganta fahimtar juna da kuma yaɗa manufofin gyaran ɗabi’a da adalci a cikin al’umma.
Bola Tinubu ya miƙa sakon ra’aziyya
Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban SCSN na kasa, mambobin majalisar shari'a, iyalan Malam Nafiu Baba-Ahmed, gwamnatin Jihar Kaduna da al’ummar jihar.
Haka zalika mai girma shugaban kasa ya kuma mika sakon ta'aziyya ga daukacin al’ummar Musulmi ta Najeriya bisa wannan babban rashi da suka yi.

Source: Facebook
Shugaban ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya shigar da shi Aljannatul Firdaus, sannan Ya ba iyalansa da al’ummar Musulmi ƙarfin jure wannan babban rashi.
Malamin Musulunci a Kogi ya rasu
Kun ji cewa an tabbatar da rasuwar daya daga cikin sanannun malaman addinin musulunci a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya, Malam Jamiu Yaakub.
Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa Sheikh Yaakub, Naibin Limamin Babban Masallacin Abobo da ke Jihar Kogi , ya rasu ne a daren Laraba, 30 ga watan Satumba, 2026.
Sheikh Yaakub ya shafe wani kaso mai tsoka na rayuwarsa yana koyarwa a aji, inda ya taimaka wajen gina rayuwar dalibai kafin ya yi ritaya daga koyarwa.
Asali: Legit.ng

