‘Babban Dan Majalisar Kano Ya Nema wa Tinubu da Abba Afuwa domin a Zabi APC
- Alhassan Ado Doguwa ya gana da wasu manyan magoya bayansa yayin da aka soma yakin neman zabe
- ‘Dan majalisar ya bukaci mutanensa su yi hakura da shugabannin APC, su sake goyon bayan jam’iyyar
- Hon. Alhassan Ado Doguwa ya jero ayyukan gwamnatin Bola Tinubu duk a kokarin ganin ya tallata shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Alhassan Ado Doguwa ya zage wajen yi wa jam’iyyarsa ta APC kamfe a mazabarsa ta Tudun Wada/Doguwa.
Kwararren ‘dan majalisar ya yi kira ga magoya bayansa da su zabi APC da duka ‘yan takaran da ta tsaida a 2027.
Sulhun da aka yi wa su Alhassan Doguwa
A wani bidiyo da Legit Hausa ta gani a shafin Siyasarmu a Facebook, an ji Alhassan Ado Doguwa yana tallar APC.
A nan ya sake dawo da maganar sulhun da aka yi tsakanin shi da Salisu Yusha’u Soja da Hon. Sa’adatu Salisu Soja.

Kara karanta wannan
Maganar zargin Dickson na shirya wa Obi da Kwankwaso makarkashiya ta yi nisa a NDC
Alhassan Ado Doguwa ya ce bai shakkan Air Commodore Salisu Soja mai ritaya da matarsa za su saba alkawari.
Alhassan Doguwa yana so a zabi APC
Saboda haka ya bukaci mutanen yankin Yar Mariya da sauran wurare su zabi APC a 2027 ba tare da wani sharadi ba.
“Ina rokon alfarmaku ta arziki, yadda ku ka yarda ni, ina rokonku ku je ku rike amanar APC daga sama har kasa.
“A zo a yi jam’iyyar nan da kyakkyawar zuciya, idan Allah ya yarda, ba zai ba mu kunya ba.
- Alhassan Ado Doguwa
Nema wa Abba da Tinubu afuwa a Kano
‘Dan majalisar tarayyan ya roki magoya bayansa su yafe wa Bola Tinubu da Abba Kabir Yusuf ko da sun yi masu laifi.
Ya roki afuwa a madadin shugabannin na APC mai mulki tun da watakila ba za su taba cin karo da talakawan nasu ba.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
Ado Doguwa ya yi kira ga ‘ya ‘yan na APC su yi wa kasa da shugaba Bola Tinubu addu’a ya iya sauke nauyinsa.
Yake cewa ya kamata shi ma Abba Kabir Yusuf a yi masa addu’ar samun damar yi wa mutanen Kano ayyukan kirki.
Hujjojin goyon bayan shugaba Tinubu
‘Dan majalisar ya ce ya kamata a zabi Bola Tinubu domin ba mutanen Arewa ba ne kawai a kasar, kyau a ba Kudu dama.
Hon. Doguwa ya ce shugaba Tinubu bai yi watsi da ayyukan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta soma a yankin Arewa ba.
Sai ya kafa hujja da hanyar Abuja zuwa Kano da ya ce saura ‘yan daruruwan kilomita kadan a gama wannan aiki a yau.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta karbe kwangilar daga kamfanin da aka ba a farko saboda ganin an karasa gina babbar hanyar.
Jagoran na APC ya kuma ce ganin an yi wa hanyar yawa, gwamnati mai-ci ta fara aikin gina titin Badagry zuwa Sokoto.
‘Dan majalisar ya ce ya je ya ga yadda aka fara wannan aiki kuma ana fatan zai tike a garin Sokoto tun daga jihar Legas.
Bayan nan kuma ya ce gwamnati ta zuba kudi domin a hada Najeriya da Nijar ta hanyar jirgin kasa, ya ce aikin ya yi nisa.
Murabus din Amaechi daga gwamnatin Buhari
Sai daga baya aka ji labari cewa gabanin hakura da mukaminsa na minista, kusan Rotimi C. Amaechi ya daina zuwa ofishinsa a Abuja.
Sau daya a mako ministan yake zuwa Ma’aikatar sufuri daga baya a karshen zamanin Muhammadu Buhari domin ya koma aiki a wata jami'a.
Rotimi Amaechi wanda aka yi shekaru bakwai da shi ya ce bai gamsu da yadda gwamnatinsu ta ke tafiya ba a lokacin duk da yana cikin kusoshi.
Asali: Legit.ng
