Magana Ta Fito: Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Kara Yawan Jihohin da Zai Je Kamfen

Magana Ta Fito: Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Kara Yawan Jihohin da Zai Je Kamfen

  • Tinubu ya ƙara yawan jihohin da zai kai ziyara yayin kamfen daga 12 zuwa 19, baya ga Abuja, inda ake sa ran zai halarci tarurruka 20
  • Jihohin Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara na cikin sabbin wuraren da aka ƙara, yayin da Arewa maso Yamma ke kan gaba da jihohi bakwai
  • ADC ta ce Tinubu ya ƙara yawan jihohin ne saboda Atiku Abubakar ya matsa masa lamba da salon kamfen ɗinsa da saƙonnin da yake isarwa ga jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara yawan jihohin da zai ziyarta yayin kamfen ɗin neman sake zaɓensa a 2027, inda adadin ya tashi daga 12 zuwa 19, baya ga Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Sabon jadawalin ya nuna cewa shugaban ƙasar zai halarci tarurrukan kamfen guda 20 a sassa daban-daban na Najeriya, domin ƙarfafa gangamin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

2027: Arewa ta zama kan gaba da Tinubu ya kara jihohin da zai je kamfen

Tinubu ya kara yawan jihohin zuwa kamfen
Kashim Shettima, mai girma Bola Tinubu da matansu a wurin kamfen din APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jihohin da Tinubu zai ziyarta yayin kamfen

Daga cikin jihohin da aka ƙara a jadawalin akwai Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara. Haka kuma, an saka Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi bayan Tinubu ya halarci tarukan kamfen a jihohin, The Punch ta kawo labarin.

APC ta tsara gudanar da tarukan kamfen guda 37 a faɗin jihohin Najeriya 36 da Abuja. Sai dai shugaban ƙasar zai halarci taruka 20 da kansa, yayin da sauran shugabannin jam’iyyar za su jagoranci sauran tarukan.

Jadawalin ya nuna cewa Arewa maso Yamma ce ke da mafi yawan jihohin da Tinubu zai ziyarta, inda aka ware mata bakwai: Kaduna, Jigawa, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara da Sokoto.

Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu kowannensu na da jihohi uku, yayin da Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas kowannensu ke da jihohi biyu.

Wannan rabon ya nuna cewa Arewa maso Yamma ce za ta fi samun damar ganin shugaban ƙasar yayin kamfen, duk da cewa jadawalin ya tanadi ziyara a sauran yankunan ƙasar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ƙara yawan jihohin da zai je yaƙin neman zabe gabanin 2027

Dalilan sauya jadawalin kamfen ɗin Tinubu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa APC da shugaban ƙasar sun sauya jadawalin farko ne sakamakon kiraye-kirayen wasu gwamnoni, waɗanda suka nemi Tinubu ya je jihohinsu domin ƙaddamar da ayyukan da aka kammala.

Wani dalili kuma shi ne ƙoƙarin ƙalubalantar ra’ayin jam’iyyun adawa da suka fassara matakin Tinubu na mayar da hankali kan mulki a matsayin rashin ƙarfin halin gudanar da kamfen a dukkan jihohi 36 da Abuja.

Wata majiya da ke da masaniya kan yadda APC ke gudanar da kamfen ɗin shugaban ƙasa ta bayyana cewa Tinubu ya riga ya je wasu jihohi, ciki har da Akwa Ibom da Jigawa, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka.

“Idan kun lura sosai, shugaban ƙasa ya je jihohi kamar Akwa Ibom da Jigawa, inda ya ƙaddamar da wasu ayyuka.
“Lokacin da shugaban ƙasa ya bayyana cewa yana son mayar da hankali kan mulki, jam’iyyun adawa sun ɗauka cewa bai san abin da yake faɗa ba.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

“Idan yana son halartar kamfen a dukkan jihohin ƙasar, zai iya yin hakan. Amma ba ya son barin gudanar da mulki saboda kamfen. Yana ganin za a iya gudanar da abubuwan biyu tare,” in ji majiyar.

ADC ta ce ta matsa wa Tinubu lamba

A martaninta kan ƙarin jihohin da Tinubu zai ziyarta, kwamitin kamfen ɗin shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC PCC) ya ce shugaban ƙasar ya ɗauki matakin ne saboda ADC da ɗan takararta, Atiku Abubakar, sun matsa masa lamba.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin kamfen ɗin ADC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa Tinubu na ƙoƙarin ziyartar ƙarin jihohi ne saboda saƙonnin kamfen ɗinsa ba sa isa ga jama’a yadda ya kamata.

Ologbondiyan ya ce Atiku ya sauya salon kamfen ɗinsa daga ziyartar jihohi zuwa kai ziyara kai tsaye ga al’ummomi, kuma saƙonninsa na samun karɓuwa a wajen ’yan Najeriya.

“Yanzu Atiku ya sauya daga kamfen a matakin jihohi zuwa kamfen a tsakanin al’ummomi, kuma saƙonninsa na isa ga ’yan Najeriya. Wannan aiki ne da dole shugaban ƙasa Tinubu ya yi ƙoƙari domin ya kamo shi. Yana ƙoƙarin yin gogayya da Atiku.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Ya kuma zargi Tinubu da APC da ci gaba da yin alkawura duk da cewa sun shafe kusan shekaru huɗu suna mulki.

A cewarsa, wannan ne ya sa ake jin kalmar “Bamayi”, domin saƙonnin kamfen ɗin APC ba sa samun karɓuwa a wajen jama’a.

Tinubu zai je jihohi 19
Mai girma Bola Tinubu a wajen kamfen Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

An yaba wa Arewa kan tarbar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon APC a Kano, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya yaba wa 'yan Arewa kan goyon baya da haɗin kan da suke nunawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027.

Kwankwaso ya ce tarbar da aka yi wa shugaban cikin farin ciki yayin ziyararsa a jihar Kebbi ta nuna yadda Arewa ke da kwarin gwiwa kan shugabancinsa da kuma aniyarsa ta sake tsayawa takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng