Najeriya da Saudi Sun Yi Zama kan Yadda za a Gudanar da Hajjin 2027

Najeriya da Saudi Sun Yi Zama kan Yadda za a Gudanar da Hajjin 2027

  • Najeriya da ƙasar Saudiyya sun rataba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2027 cikin lumana
  • Shugaban (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, da Mataimakin Ministan Aikin Hajji na Saudiyya, Dr Abdulfattah Mashat, ne suka yi yarjejeniyar a birnin Jeddah
  • Yarjejeniyar ta ƙunshi kason alhazai da za a bai wa Najeriya, tsarin masauki, sufuri, kiwon lafiya, da kuma biyayya ga dokokin ƙasar Saudiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jeddah – Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da za ta tsara hanyoyin gudanar da aikin hajjin shekarar 2027.

Wata sanarwa da Shugaban Sashin Yaɗa Labarai na Hukumar NAHCON, Shafii Sani Mohammed ya fitar, ta tabbatar da cewa an kulla yarjejeniyar ne a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

'Sai masu biyayya': An ware ƴan APC da za a ba motoci a kamfen Tinubu

Saudiyya da Najeriya Hajjin 2027
Taron Saudiyya da Najeriya a Makkah. Hoto: NAHCON
Source: Facebook

NTA ta wallafa a X cewa Shugaban Hukumar NAHCON na Ƙasa, Ambasada Ismail Abba Yusuf, da Mataimakin Ministan Aikin Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Abdulfattah Bin Sulaiman Mashat, ne suka sanya wa takardar hannu.

Abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa

Yarjejeniyar ta shafi fannoni daban-daban da suka haɗa da kason adadin alhazai da aka ware wa Najeriya, bin dokokin kasar Saudiyya, cika lokutan gudanar da ayyuka, tare da tsara masauki, sufuri, da kiwon lafiya.

Ambasada Yusuf ya mika godiyarsa ga hukumomin ƙasar Saudiyya bisa irin zuba jarin da suke yi wajen inganta abubuwan more rayuwa na aikin hajji da kyautata sabis ga alhazai.

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin alhazai na jihohi da kamfanonin yawon buɗe ido masu zaman kansu domin aiwatar da yarjejeniyar cikin nasara kafin kakar hajjin ta 2027.

Bayanin gwamnatin Saudiyya

Dr. Mashat ya bayyana cewa ƙasar Saudiyya ta samu kashi 93 cikin 100 na gamsuwar alhazai a lokacin aikin hajjin shekarar 2026, inda ya yabi Najeriya game da cika lokutan gudanar da ayyuka da aka diba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je har gida sun harbe shugaban Miyetti Allah

Ya bayyana cewa yana fatan alhazan Najeriya za su cigaba da kokarin wajen bin dukkan dokokin da Saudiyya ta sanya domin samun damar yin aikin Hajji lami lafiya.

Dakin Ka'aba a Saudiyya
Mutane na dawafi a dakin Ka'aba. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A yanzu haka dai Najeriya ta fara shirye-shirye game da aikin Hajjin shekarar 2027, inda tuni jihohi suka ayyana kudin da kowane mutum zai biya domin zuwa sauke farali a Saudiyya.

Tinubu ya shiga dakin Ka'aba

A wani labarin, kun ji cewa rahoton shigar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu cikin dakin Ka'aba mai alfarma ya jawo martani mabambanta daga 'yan Najeriya a kafafen sada zumunta.

Yayin da wasu 'yan ƙasar suka nuna farin cikinsu da ganin shugaban ya samu wannan babbar dama, wasu kuwa sun bayyana damuwarsu kan shingayen da aka kafa a kewayen dakin a lokacin ziyarar tasa.

Wasu daga cikin masu sharhi sun kuma gabatar da tambayoyi kan yadda ake ba shugabannin siyasa damar shiga wannan wuri mai tsarki, yayin da sauran Musulmi na yau da kullum ba su samun irin wannan damar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng