Wike Ya Jefa Babban Rikici a tsakanin Gwamnonin APC, Sun Rabu 2
- Rikicin da ke tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu gwamnonin APC ya raba gwamnonin jam’iyyar zuwa sansanonin siyasa daban-daban
- Wasu daga cikin gwamnonin na goyon bayan Wike, yayin da wasu ke tare da Shugabansu, Hope Uzodimma, da Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq
- Wasu gwamnonin kuma ba su bayyana matsayinsu ba tukuna, inda ake cewa suna jiran dawowar Shugaba Bola Tinubu daga waje kafin su yanke hukunci kan rikicin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Rikicin siyasa tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu daga cikin gwamnonin APC ya raba gwamnonin jam’iyyar zuwa sansanonin siyasa daban-daban gabanin zaben 2027.
Yayin da wasu gwamnonin ke nuna goyon baya ga Wike, wasu kuma sun jingina da Hope Uzodimma da AbdulRahman AbdulRazaq a rikicin da ke kara tsananta.

Source: Twitter
Gwamnonin da ke tare da Wike
Wata babbar majiya a jam’iyyar ta shaidawa Vanguard cewa ba dukkan gwamnonin APC ne ke adawa da Wike ba, tana mai cewa wasu daga cikinsu abokansa ne tun kafin ya zama minista.
“Zan iya tabbatar muku cewa ba dukkan gwamnonin ne ke adawa da ministan ba. Da yawa daga cikinsu abokansa ne tun kafin yanzu.
"Ministan ma ya taba zama gwamna. Ko da kowa ya juya masa baya, kun san cewa gwamnan Adamawa da wasu na tare da shi,”
in ji majiyar.
Bincike ya nuna cewa Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri; Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno; Gwamnan Edo, Monday Okpebholo; Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu suna tare da Wike.
Haka zalika an ce Gwamnan Kogi, Ahmed Ododo na daga cikin gwamnonin da ake cewa suna tare da matsayar Wike.
Matsayar Uzodimma da AbdulRazaq
A daya bangaren, ana cewa Hope Uzodimma, AbdulRahman AbdulRazaq, Gwamnan Kaduna Uba Sani, Gwamnan Ogun Dapo Abiodun da wasu gwamnonin na adawa da matsayar Wike.
Uzodimma shi ne Shugaban Gwamnonin APC, yayin da AbdulRazaq yake Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.
Wasu gwamnonin kuma har yanzu ba su yanke shawarar bangaren da za su mara wa baya ba, inda majiyoyi suka ce suna jiran dawowar Tinubu domin su fahimci matakin da za a dauka.

Source: Twitter
Rikicin ya dade yana faruwa a cikin APC, amma a baya-bayan nan ya fito fili, lamarin da ya jefa Wike cikin takaddama da wasu gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar.
Maganar haduwa da Atiku
A wani labarin, kun ji cewa wasu gwamnonin APC da ba su gamsu da wasu al’amuran cikin gida na jam’iyyar ba sun fara duba yiwuwar kulla alaka da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, gabanin zaben 2027.
Majiyoyi sun ce damuwar wasu daga cikin gwamnonin ta shafi yiwuwar Rainbow Coalition ta Wike ta kalubalanci tasirinsu a zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisu na 2027.
Rahotannin sun ce Atiku da jam’iyyar ADC na daga cikin hanyoyin siyasar da wasu daga cikin gwamnonin ke nazari domin kare muradunsu da tsarin siyasar da suka gina yayin da rikicin cikin APC ke ci gaba.
Asali: Legit.ng

