Manyan ADC a Arewa Sun Hada Kai Sun Tunkari NJC kan Hana Atiku Takara

Manyan ADC a Arewa Sun Hada Kai Sun Tunkari NJC kan Hana Atiku Takara

  • Kungiyar Shugabannin Jam'iyyar ADC na Jihohi 19 na Arewa ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta rusa shugabancin jam'iyyar na ƙasa karkashin David Mark
  • Shugabannin sun bayyana aniyarsu ta daukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da mika koke gaban Hukumar Shari'a ta Ƙasa (NJC) saboda abin da suka kira sabawa tsarin shari'a
  • Sanarwar ta kalubalanci hukuncin mai shari'a Peter Lifu, tana mai cewa ya ci karo da wani hukuncin da mai shari'a Musa Liman ya yanke a baya kan takaddama guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ƙungiyar shugabannin jam'iyyar ADC na jihohin Arewa 19 ta fito fili ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja wanda ya tsige kwamitin shugabancin jam'iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin David Mark.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce ya gano tarkon da Tinubu ya kafa masa kan bashin da zai ci a waje

Shugabannin sun tabbatar da cewa ba za su karɓi wannan hukunci ba kuma suna kan hanyar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara don ƙalubalantar matakin.

Shugaban ADC na kasa
David Mark da ke jagorantar ADC. Hoto: ADC Vanguard
Source: Twitter

Punch ta rahoto cewa wannan matsaya ta fito ne cikin wata sanarwa da shugabannin jihohin suka sanya wa hannu a ranar Talata, biyo bayan hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar 5 ga Nuwamba.

Korafin shugabannin ADC na Arewa

A cikin sanarwar da suka fitar, shugabannin sun bayyana cewa hukuncin ya yi karo da wanda Mai Shari'a Musa Liman ya yanke a ranar 2 ga Yuli, 2026 a kan takaddama guda tsakanin Leke Abejide da jam'iyyar ADC.

Suka sanar da cewa:

“Muna rashin amincewa da wannan hukunci baki ɗaya kuma za mu ƙalubalance shi a kotun ɗaukaka ƙara. Wannan mataki ne da ya ke a bayyane daga tsarin shari'ar da aka riga aka yi a kan wannan batu.”

Shugabannin sun ƙara da cewa kotun ba ta da ikon shiga cikin al'amuran cikin gida na jam'iyyun siyasa, sannan sun ƙalubalanci matsyar wanda ya shigar da ƙarar, Nafiu Bala Gombe, wanda a cewarsu ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar a baya.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fitar da sanarwa ga shugabannin ADC da aka rusa takarar Atiku

Kazalika, sun zargi kotun da yin watsi da korafe-korafe 27 da neman dakatar da aiwatar da hukuncin ba tare da sauraron lauyoyinsu ba.

Hukuncin dai ya soke takarar ƴan takara ciki har da tikitin shugaban ƙasa na Atiku Abubakar, wanda shugabannin suka ce an tauye musu haƙƙinsu na samun shari'a ta adalci tun da ba a gayyace su zuwa kotun ba.

Atiku Abubakar a gidan shi
Dan takarar ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

ADC ta soki APC

Ƙungiyar ta zargi jam'iyyar APC mai mulki da wasu jami'an gwamnati da ƙoƙarin amfani da kotu wajen murƙushe 'yan adawa da rage ƙarfin tsarin jam'iyyu daban-daban a ƙasar.

A ƙarshe, sun sanar da cewa tawagar lauyoyinsu ta riga ta shigar da takardun ɗaukaka ƙara tare da shirin mika koke ga Hukumar Shari'a ta Ƙasa (NJC) don ɗaukar mataki a kan abin da suka kira sabawa tsarin shari'a.

Atiku zai maido tallafin mai

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya sake maimaita alƙawarsa na dawo da tsarin tallafin man fetur.

Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC ya bayyana matsayarsa ne a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, ta hanyar wallafa wani bidiyo na yaƙin neman zaɓe.

Atiku ya jaddada cewa matsayinsa bai canza ba kuma dawo da tallafin shine hanyar da za ta sa rayuwa ta zama mai sauƙi da araha ga 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng