Babu Mai Tsira: Gwamna Ya Ce Zai Rataye ko da Mahaifinsa ne kan Ta'addanci
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya sha alwashin sanya hannu kan takardar hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane har ta kai ga mutuwa
- Okpebholo ya ce ba zai tausaya wa kowa ba, ko da mahaifinsa ne aka samu da laifin, kuma ya shirya sa ido kan aiwatar da hukuncin
- Gwamnan ya bayyana cewa dokar jihar ta tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane idan har aka kashe wadanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana cewa a shirye yake ya sanya hannu kan takardar aiwatar da hukuncin kisa kan ta'addanci.
Ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane zai fuskanci hukunci ba tare da la’akari da kusancin da ke tsakaninsu ba.

Kara karanta wannan
"Na ƙara gane rayuwa," Sanata ya ɗauko muhimman darussa a zaman da ya yi a gidan yari

Source: Facebook
Gwamna ya shirya sa dokar hukuncin kisa
Gwamnan ya ce ba zai kare duk wanda aka samu da wannan laifi ba, ko da kuwa mahaifinsa ne ko wani na kusa da shi, inda ya kuma bayyana aniyarsa ta sa ido kan aiwatar da hukuncin, cewar Punch.
Okpebholo ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da jaridar TheCable ta wallafa a ranar Talata, yayin da gwamnatinsa ke kokarin tabbatar da dokar jihar da ta tanadi hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane idan har aka kashe wadanda aka sace.
Gwamnan ya ce:
"Ina addu'ar 'yan'uwanmu kada su shiga cikin wannan aika-aika, domin zan sanya hannu kan takardar hukuncin. Ko mahaifina ne, zan sanya hannu. Gaskiyar magana ita ce, dole ne mu cire miyagun mutane daga cikin al'umma domin abubuwa su daidaita.
"Domin wani zai mutu. Amma wadannan mutane ne suke kashe mutane. Mutane nawa muka kashe?"
Okpebholo ya bayyana dalilin daukar matakin
Gwamnan ya kare matsayarsa ta hanyar bayyana irin azaba, tsoro da raunukan da mutanen da suka fada hannun masu garkuwa da mutane ke fuskanta.
Ya ba da misalin wata mata da ya ce masu garkuwa da mutane sun tura kasa yayin wani yunkuri na sace ta, inda ya bayyana cewa tsananin firgicin da ta shiga zai iya haddasa mutuwarta.
Haka kuma, ya yi magana kan harin da aka kai wa babban alkalin jihar, inda ya ce daya daga cikin hannayensa ya samu mummunan rauni sakamakon arangama da masu garkuwa da mutane.
Okpebholo ya ce:
"Ku duba yadda suka rika tura waccan matar kasa. Me zai faru idan ta mutu a lokacin saboda tsoro? Tsoron kadai ya isa ya jawo mutuwarta. Mutane da dama sun fuskanci irin wannan mummunan hali.
"Ko babban alkalin jiharmu, idan kuka gan shi, za ku ga cewa masu garkuwa da mutane sun jikkata daya daga cikin hannayensa."
Gwamnan ya ce tuni ya tuntubi babban lauyan gwamnatin jihar domin sanin matakin da aka dauka kan takardun da suka shafi hukuncin, inda ya ce yana jiran karin bayani.

Source: Original
Gwamna ya sha alwashin bin shari'a har karshe
Okpebholo ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta kyale wadanda aka yanke wa hukunci su tsira daga hukunci ba, inda ya ce za ta bi dukkan matakan daukaka kara kafin aiwatar da hukuncin.
Ya ce:
"Za mu ci gaba da bin diddigin shari'arsu a matakin daukaka kara. Ba za mu kyale su su tafi haka kawai ba. Duk inda aka tsaya, za mu ci gaba daga nan. Ba za mu bar kowa ba.
"Na tsaya a kan wannan matsaya, idan aka kawo min takardar a yanzu, zan sanya hannu, har ma zan sa ido kan yadda ake aiwatar da hukuncin kisa."
Yaro ya kashe mahaifinsa shugaban APC
An ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Edo ta tabbatar da kisan wani shugaban APC na mazaba, Julius Bello, wanda aka fi sani da De Lord Ogata.
Ana zargin ɗansa mai suna Irobudo ya yi amfani da guduma mai nauyi wajen bugun kansa har ya mutu.
Majiyoyin daga cikin iyalinsa sun ce ɗan ya kashe mahaifinsa ne saboda zargin da yake cewa shi ne sanadin talaucinsa.
Asali: Legit.ng

