"Yadda Tinubu Zai Nuna Wa Atiku Karfin Siyasa, Ya Lashe Zabe a Jihohi 36 a 2027"

"Yadda Tinubu Zai Nuna Wa Atiku Karfin Siyasa, Ya Lashe Zabe a Jihohi 36 a 2027"

  • Shugaban Majalisar gudanarwa ts NPA, Dayo Adeyeye, ya ce ADC ba ta da ƙarfin hana Shugaba Bola Tinubu sake lashe zaɓe
  • Ya yi hasashen cewa jam'iyyar APC mai mulki za ta lashe zaɓe a dukkan jihohi 36 na Najeriya
  • Adeyeye ya kuma yi zargin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ba shi da isasshen goyon bayan siyasa a jiharsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeeia - Shugaban Majalissr Gudanarwa ts Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA), Sanata Dayo Adeyeye, ya yi watsi da ra’ayin cewa ADC na iya zama babbar barazana ga Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Adeyeye, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar South-West Agenda for Asiwaju (SWAGA), ya yi hasashen cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta lashe zaɓe a dukkan jihohi 36 na ƙasar.

Kara karanta wannan

'Sai masu biyayya': An ware ƴan APC da za a ba motoci a kamfen Tinubu

Dayo Adeyeye
Shugaban Majalisar gudanarwa na hukumar NPA, Sanata Dayo Adeyeye Hoto: Adedayo Clement Adeyeye
Source: Facebook

Ya ce ADC ba ta da ingantaccen tsarin siyasa, tasirin da ya kamata a matakin talakawa da kuma ƙarfin zaɓe da za su ba ta damar ƙalubalantar jam’iyyar APC, kamar yadda Vangaurd ta rahoto.

Ya kuma yi tambaya kan ƙarfin siyasar ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, yana mai zargin cewa bai da isasshen goyon baya ko a jiharsa ta Adamawa.

Adeyeye ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Ado-Ekiti ranar Laraba, inda yake nazarin yanayin siyasar ƙasar gabanin babban zaɓen 2027.

Ya yi watsi da ikirarin cewa APC na fargabar ’yan adawa, yana mai cewa irin wannan magana ba ta da tushe.

A cewarsa, ADC ba ta nuna isasshen ƙarfin siyasa a matakin jihohi da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da zai ba ta damar zama babbar abokiyar hamayya ga jam’iyyar APC.

Adeyeye ya yi magana kan ADC

“Ta yaya APC za ta ji tsoron wani abu a irin yanayin siyasar da muke ciki yanzu? Na faɗi sama da watanni uku da suka gabata cewa akwai yiwuwar Shugaba Tinubu ya lashe zaɓe a dukkan jihohi 36, kuma yanzu na ƙara gamsuwa cewa hakan zai faru.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da zai sa Obi ya gudu a Najeriya ko ya ci zaben 2027

“ADC jam’iyya ce da ba ta da gwamna a ko wace jiha cikin jihohi 36. Mambobi nawa take da su a Majalisar Dokoki ta Ƙasa? Majalisun dokokin jihohi nawa take iko da su? Ba za ka iya kwatanta jam’iyyar da ba ta da ingantaccen tsarin siyasa da APC ba.”

- In ji Sanata Dayo Adeyeye.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Zargin rashin goyon bayan Atiku

Tsohon sanatan ya yi gardamar cewa burin Atiku na zama shugaban ƙasa ya ƙara raunana saboda abin da ya bayyana a matsayin ƙarancin goyon bayan siyasa a Jihar Adamawa.

Ya yi zargin cewa gwamnan jihar da kuma fitattun ’yan siyasa a Adamawa ba su goyon baya tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba.

"Tinubu zai wahal da yan adawa"

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ayyukan raya kasa da Tinubu ya gudanar za su wahalar da jam’iyyun adawa wajen kayar da shi a zaben 2027.

Wike ya bayyana cewa ayyukan da ake gani a Abuja za su zama hujjar da APC za ta gabatar wa ’yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262