An Samu Baraka, Ministan Tinubu Ya Fara Takun Saka da Gwamnonin APC 2 a Najeriya

An Samu Baraka, Ministan Tinubu Ya Fara Takun Saka da Gwamnonin APC 2 a Najeriya

  • Alamu sun nuna alaka ta fara tsamni tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnonin APC biyu yayin da ake tunkarar zaben 2027
  • Wike ya fito a bainar jama'a ya zargi Gwamna Hope Uzodinma na Imo da AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara da jagorantar masu adawa da shi
  • Wike ya ce duk da kasancewarsa a PDP, zai ci gaba da goyon bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu karo na biyu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Rivers, Nigeri - Ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana gwamnonin jam'iyyar APC biyu da yake zargin sun sa kafar wando daya sa shi.

Wike ya yi ikirarin gwamnonin jihohin Imo da Kwara, Hope Uzodinma da AbdulRahman AbdulRazaq, na daga cikin gwamnonin da ke adawa da shi a siyasance.

Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike a wurin kaddamar da wasu ayyuka Hoto: Nyesom Wike
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Wike ya yi wannan zargi ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.

Ya kuma yi watsi da ikirarin cewa harkokin siyasarsa na da nufin yin aiki da gwamnoni na APC.

Kara karanta wannan

Aiki ja: An bayyana abin da gwamnonin APC 31 za su yi wa Tinubu a 2027

Kalaman ministan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye a fagen siyasa gabanin zaben 2027.

Wike na goyon bayan Tinubu

Wike, duk da cewa har yanzu yana cikin jam'iyyar PDP, yana bayyana goyon bayansa ga sake tsayawar Shugaba Bola Tinubu takara a zaben 2027.

Dangantakarsa da wasu gwamnoni na APC ta jawo hankalin jama'a, musamman yayin da 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban ke sake tsara matsayinsu gabanin zaben.

Wike ya fi karkata suka ga gwamnan Kwara, AbdulRazaq, wanda ya zarga da jagorantar wani yunkuri na siyasa da ake yi domin adawa da shi.

Rikicin Wike da gwamnan Kwara

Ministan Abuja ya ce:

“Ku dauki na Kwara a matsayin misali, shi ne yake jagorantar wannan yaki da ake yi da ni a ko'ina, kuma na fuskance shi kan lamarin. Ba na magana kan abin da ba zan iya karewa ba.”

A cewar Wike, AbdulRazaq ya zarge shi da daukar nauyin wasu 'yan siyasa da ke adawa da 'yan takarar gwamnan ya fi so a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya fadi matsayarsa kan batun juyawa Tinubu baya a 2027

Sai dai Wike ya ce maimakon haka, ya kamata gwamnan ya yaba masa saboda rawar da ya taka wajen samar da dandalin siyasa ga wasu jiga-jigan APC da suka bar jam'iyyar suka koma PDP.

Wike ya yi magana kan Uzodinma

Zargin da Wike ya yi wa Hope Uzodinma bai zo da cikakken bayani ba, amma ya bayyana shi kai tsaye, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wike ya ce:

“Gwamna Hope ya san irin goyon bayan da na ba shi," yana maintuna cewa a wani lokaci gwamnan Imo ya ki mara masa baya.
Uzodinma.
Shugaban gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma Hoto: Hope Uzodinma
Source: Facebook

Wike ya taba kare kujerar Uzodinma bayan Kotun Koli ta soke nasarar Emeka Ihedioha tare da tabbatar da Uzodinma a matsayin gwamnan Imo a shekarar 2020.

Sai dai Wike ya ce sabanin da yake tsakaninsa da wasu 'yan siyasa ba zai hana shi cimma burinsa na taimaka wa Tinubu wajen lashe wa'adi na biyu ba.

Wike ya sha alwashin kayar da Atiku

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce zai ci gaba da taka rawar gani a siyasar jihar Rivers gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Wike ya ce ba zai zauna ya rike hannu bibbiyu ya bar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasar mai zuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262