Iran Ta Fitar da Bidiyon Rumbun Makamai da ke karkashin Kasa
- Rundunar Masu Tsaron Juyin Juya Hali ta Iran (IRGC) ta nuna hotunan wata sabuwar cibiyar ajiyewa da harba makamai ta ƙarƙashin ƙasa
- Babban hafsan sojin Iran, Ali Abdollahi, ya gargaɗi cewa martanin ƙasar zai wuce yankin Gabas Tsakiya idan aka sake kaddamar da hari a kanta
- Iran ta bayyana cewa daukar matakin boye kayayyakin yakin a ƙarƙashin ƙasa na da nufin kare su daga harren ta sama na ƙasashen Amurka da Isra'ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tehran – Rundunar Masu Tsaron Juyin Juya Hali ta ƙasar Iran (IRGC) ta fitar da bidiyon wata sabuwar cibiyar soji ta ƙarƙashin ƙasa da ake amfani da ita wajen kera da adana makamai masu linzami a ranar Talata.
Gidajen talabijin na kasar Iran sun nuna Babban Hafsan Sojojin Iran, Ali Abdollahi, da Kuma Kwamandan Rundunar Sarakunan Samaniya ta IRGC, Majid Mousavi, suna zagayawa a cikin wannan katafaren rami.

Source: Facebook
Iran International ta rahoto cewa hukumomin kasar ba su bayyana takamaiman inda wannan cibiyar take ba ko kuma ranar da manyan sojojin suka kai ziyarar a cibiyar.
Gargaɗin da sojojin Iran suka yi
A lokacin ziyarar, Ali Abdollahi ya gargaɗi abokan gabarsu cewa martanin Iran ba zai tsaya kawai a yankin Gabas Tsakiya ba idan aka sake kaddamar da wani harin soji a kanta.
Rahotanni sun nuna cewa ya bayyan cewa:
“Idan abokan gaba suka sake daukar wani mataki a kanmu, martaninmu zai wuce iyakokin wannan shiyyar.”
Bayanin kakakin IRGC
Kakakin IRGC, Hossein Mohebbi, ya riga ya sanar tun a ranar Asabar cewa rundunar za ta fito da sabuwar cibiyar makamai masu linzami ta ƙarƙashin ƙasa domin kare kayayyakin su daga harren ta sama lokacin yaƙi.
Mohebbi ya ƙara da cewa Iran za ta iya amfani da samfuran makaman da ba ta taɓa nuna su a fili ba idan har faɗa tsakaninta da ƙasashen Amurka da Isra'ila ya tsananta.
Iran dai ta kwashe shekaru tana gina cibiyoyin harba makamai a ƙarƙashin ƙasa waɗanda take kira "biranen makamai masu linzami" don kare su daga hare-haren jiragen yaƙi.
Bayan bdiyon da aka fitar, rahoto ya nuna cewa hotunan satalaite suna nuna tana ci gaba da gyara da inganta waɗannan cibiyoyi na soji.

Source: Facebook
Matakan da Iran ke dauka na zuwa ne bayan yakin da ta gwabza da kasar Amurka da Isra'ila, lamarin da ake fargabar zai iya sake barkewa.
Shafin Defence Index ya wallafa bidiyon a X:
Ana son tsige Pete Hegseth
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Amurka, Hakeem Jeffries, ya bayyana goyon bayansa ga ƙudirin tsige Ministan Tsaro, Pete Hegseth, kan yaƙin Iran.
Jeffries ya zargi Hegseth da amfani da muƙaminsa ba bisa ƙa’ida ba, raunana tsaron ƙasar da kuma jefa Amurka cikin yaƙin da ya yi tsada sosai.
Biyo bayan lamarin, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kare ministan gaba ɗaya, inda ya buƙaci ’yan majalisa su goyi bayansa maimakon tsige shi daga mukaminsa.
Asali: Legit.ng

